Sashe 79
Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
*** Ƙamshin sa ne ya zagaye makeken falon kafin ta kon tafiyar shi mai cike da natsuwa da kwanciyar hankali ya fara shiga kunnen Abbu da Mubarak da ke zaune suna magana wanda baka jin abinda suke faɗa sai kukan Ac da ke tashi haɗe da sanyin turare mai daɗi da yake garwaye da falon, dan musamman Abbu yau ya tare falon bayan ya tado sa dan in bai fito ba ya koma ya sako shi gaba,dan tun safe yake son ya fito da shi zuwa ƙauyen su Shatou duba aikin da ake yi ya san halin shi tsaf zai kasa yin tafiyar kamar kwana biyu da suka wuce ya zille wa tafiyar wadda sai yau Allah ya nufa za,ayi ta dan Abbu da kan sa ya shiga bedroom ɗin sa ya tado shi dan haka kyakkyawar fuskar nan ta sa take a ɗaure dan gaba ɗaya ji yake an takura masa ba yanzu ya so yin tafiyar ba.Murmushi Abbu yayi yana kallon sa ganin yadda ya tura bakin sa gaba kamar wani ƙaramin yaro ɗan goye.Sanye yake cikin wasu haɗaɗdun riga da wando masu kyau yan Companyn le vanor tsadaddu yana sanye da riga ruwan shuɗi da Black blue jeans sai p cap da yaɗaura akan sa mai ɗauke da rubutu kamar haka ANGEL.cikin tsari mai kyau da burgewa kwantaccen gashin kan sa ya kwanta luff agefe da gefen cap ɗin sa Black blue,sai takalmin sa rufaffu suma masu tsada da kyau blue Black. Murmushi Mubarak yayi ganin yar hararar da ya sauke masa ta gefen ido wadda ba kowa zai iya lura da yayi masa ita ba.
Abbu cike da sakin fuska da murmushi ya furta " Masha ALLAH bayan ya gama ƙarewa ɗan na sa kallo ya so ace shigar manyan kaya yayi amma ko hakan babu laifi ɗan na sa kyakkyawa ne Masha ALLAH.
Cike da ƙasaita da natsuwar sa ya ƙara sa saukowa fuska ya shagwaɓe a hankali yana zama kusa da Abbu da yake ta murmushi.
Kan sa ya shafa a hankali sannan ya ce " Masha ALLAH,Allah ya tsare muku hanya yayi albarka ya baku iyalai masu albarka " .
Cike da farin ciki ya amsa da Amin sai dai Abbun ne kawai ya ji shi dan akan laɓɓan sa yayi ta.
Addu'ar Abbu ta ƙarshe kuwa bata samu amshi ba sai ma lumshe idanun sa da yayi hakan da yayi ya sa Abbu girgiza kan sa kawai yana cigaba da murmushi shiko Mubarak cike da jin daɗi yake Amsawa da Amin yana yin ƙasa da kan sa a addu'ar ƙarshe ta Abbu da ya ɗan jima kunya.
Miƙewa yayi a hankali bayan ware idanun sa sannan a hankali ya furta " Abbu sai mun dawo ".
" Allah ya tsare hanya banda rigima da Æ´aÆ´an mutane ".
Abbu ne yayi Furucin yana sakin ƙayataccen murmushi wanda MAHAJ da maganar ta bashi mamaki yake ɗan satar kallon Abbun na zancen sa mai haɗe da murmushin sa da ke nuna farin cikin sa a fili,kan shi ne ya ɗan ɗaure masa yana mamakin yadda aka yi Abbu ya sako wannan zancen sai dai kamar zai ce wani abu bayan ɗan ƙara waigowa da yayi ya ɗan ƙara satar kallon Abbun,sai kuma ya sa kai ya fice yana baza ƙamshin sa a ko wane saƙo da lungu.
Muby kuwa ƙaramar dariya yayi fahimtar inda furucin Abbu ya nufa kafin shima yayi wa Abbu sallama tare da bashi tabbacin zasu kula da hanya.Addu,a ya ƙara bin su da ita yana Amsawa da Amin har ya fice daga ƙaton falon gaba ɗaya.
Murmushi ne ya cigaba da wanzuwa akan fuskar Abbu kafin ya ɗan girgiza kan sa ya miƙe yana gyara zaman hular sa door ɗin da zata sadaka da part ɗin Aiyah ya shiga da Sallama ɗauke a bakin sa.
Zaune ya same ta kan darduma tana lazimi dan gama sallar walhan ta kenan dan Aiyah akwai ibada matuƙa.
" Aiyah Barka da safiya "
Abbu ya furta a natse yana mai tanƙwashe ƙafafun sa kusa da sallayan ta mai taushi da take kai.
Kasancewar ta saba bayan gaisuwar bayan Sallahn Asuba idan zai fita irin wannan lokaci dole zai shigo yayi mata ina kwana tare da mata ya fita ta yi masa addu'a.
Shafe addu'a tayi tana sakin fuskar ta a hankali ta amsa masa tana furta " Har za,a fita ".Da murmushi kwance akan fuskar ta.
" Eh Aiyah zamu yi meeting da shugaban ƙasa ne by 10"
Kai Aiyah ta jinjina cike da sakin fuska ta ce " Allah ya taimaka ya bada nasara ya sa awanye lafiya ".
" Amin ya hayyu ya qayyum "
Abbu ya amsa cike da jin daɗi kafin a hankali kuma murya cike da raunin da yake ɓoyewa ya furta " MAHAJ ma sun fita ƙauyen chen duba aikin nan da ya fara ".
Ya kai ƙarshen zancen kamar mai jin tsoron ƙarasa zancen ko tsoron abinda Aiyah zata tai masa.
Aiyah kuwa take fuskar ta ta chanza ta haɗe rai kamar an mata saƙon mutuwa shiru ƙaton Falon na Aiyah da ya ke tsit ya ƙara ɗauka sai sautin AC da ke ɗan tashi.Kafin a hankali jiki mace Abbu ya miƙe ganin bata da niyyar cewa komai.
" Na tafi sai na dawo "
Abbu ya furta a hankali jikin sa mace.
" A dawo lafiya ".
Aiyah ta furta ba tare da ko ta kalli fuskar Abbun ba dan ta tsani ganin Damuwar sa ko kaÉ—an shi ya sa ma take ragawa mahaj a gaban idanun sa.
Har ya cire rai da tsammani ya kai tsakiyar falon jikin sa mace yana gyara Babbar rigar sa ya tsinkayo Muryan Aiyah na furta " Allah ya sanya albarka ".
Ajiyar zuciya ya sauke a hankali kafin ya furta Amin yana ficewa daga sashen gaba ɗaya dan ya san da wa take wannan addu'ar,wanda ita kan ta Addu'ar ya san bata da zaɓi ne yanayin sa ta duba Damuwar da ta wanzu akan fuskar sa.
Sashen Ammah ya shiga bai jima ba sai gashi ya fito dan dama sunyi Sallama ya shiga ya ƙara duba jikin Samrah ne da take fama da mura kwana biyu na sanyin ice cream da MAHAJ ya ke ɗan fita da ita tana jido shi.
Direct yana fitowa ya shige ɗai daga cikin danƙara danƙaran motocin sa da suke Parkey a gefe gwanin burgewa.Bayan motar ya shige kamar ko yaushe bayan bude masa motar kafin suma suka fice tare da mota ɗaya ta sauran masu kula da shi da suka rage.
A ɓangaren MAHAJ kuwa yana fita mota ya faɗa yana gyara zaman sa tare da jingina da seat dan dama masu wankin motocin sun gyara komai an kimtsa sa da duba lafiyar su dan fitar ta su da ta Abbu ɗin.
Muby kuwa da zuwan sa shima fuskar sa kwance da murmushi ya shige motar tare da kunna ta suka bar harabar compound É—in tare da mota uku sai budaÉ—diya guda da Abbu ya tilasta masa fita da su dan kariyar lafiyar gudan jinin sa abun son sa da farin cikin sa.
A jere suka fice gwanin burgewa bayan wangale musu ƙaton gate ɗin da aka yi koda suka iso dai dai fankacecen gate ɗin estate ɗin take aka wangale musu shi ganin tambarin motar ta sa da duk inda ta shiga sun san mallakin ta duk da ƙarancin shekarun sa ko Amma suna bashi girma sosai kasancewar sa mutun mai tsare gida da kame kan sa ga kowa bayan mahaifin sa.