← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 110

Sashe 67

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ɗan jimm Ummah tayi kafin ta sakin iska mai zafi cike da wata sabuwar damuwa yanayin alamar ɓacin rai na bayyana akan fuskar ta.
Hannun ta riƙa wata ƙara LEENA ta saka tana batun sumewa Ummah wajen saboda ta taɓa dai dai wajen da yake mata ciwo.
Cike da damuwa da tashin hankali Umma tayi kan ta tana rungume ta kafin ta riƙo hannun ta ɗaya mai lafiya, zauna wa da ita tayi kan kujera har lokacin tana rusar kuka.
Rarrashin ta Ummah ta fara yi wadda take tunanin REENA ta samu Bone dislocation
Wayar ta,ta fara ƙoƙarin dannawa domin kiran Abba sai ga REENA ta fito tana faman cin chocolate hankalin ta kwance.
Fuskar nan Tata ɗaure kamar an mata mutuwa musamman yau da take jin Haushin kowa saboda dawowar ta Bilal dan har yanzu basu shiri tun maganar da suka yi akan wayar Samir ba su ƙara magana ba,bata nemi shi ba shi ma haka ya fita iskan ta,Ummah da Abba duk suna lura sai dai babu wanda ya shiga cikin faɗan sun san daya dawo gidan zata sauko dan shi sun san ayyukan gaban sa,yanzu haka ya ma manta da suna faɗa dan duk yayi waya da ɗayan su yana yawan tambayar ina LEENA da REENA Sai dai duk Suka yi waya da REENA itama takan ce ga LEENA ita kuwa da ta fahimci dashi Reena ke waya sai ta bar wajen dan dashi har Reena ɗin haushi suke bata dan cewa take yafi son Reena.
Sai dai cikin Wannan É—an lokaci abun ya É—an yi sanyi sai dai sukan yi sati basu yi magana ba sannan kowaccen su ta na Bedroom É—in ta sai kwanan nan ne ma aka samu dai dai to bayan Ummah ta shiga lamarin ita da Abba.
Kuma hakan bai da na saba da ƙoƙarin Samir dan kafin ya wuce daga hutun na sa da ya ɗauko ganin yawan faɗan na su ya tayar masa da hankali hakan ya sa ya sanya aka yi musu sauka dan samun saukin wannan lamari wajen Ubangiji da ya jarabce su dan yanayin da suke ciki ɗin jarabawa ce Babba Yadda suke hantarrar junan su ko kashe juna suna iya yi ga dambe take hakan shi ya ɗaga hankalin Samir ba tare da ya sanar wa kowa abun da yayi ba ya aiwatar cikin yardan Ubangiji kuwa aka samu sassauci sai dai gabar haka kawai da suke yin ta babu dalili LEENA zata ɗaurewa Reena, yar uwar ta tayi ta bibiyar ta jin meta mata,ita kuwa bata faɗi sai ta share ta dan babu dalili,sai wata rana da Reena ta matsa kai tsaye LEENA ta ce mata ta tsane ta duk da ƙarancin shekaru irin na REENA ta ji zafin kalamin sai dai bata faɗawa kowa ba amma ya zauna ranta duk da ta san cewa yar uwar ta ta faɗa ne kawai bada wata manufa ba,kuma ba tana nufin abun da ta ce bane a gare ta.Kuma tun daga lokacin itama Reena sai ta fita iskan ta dan haka kawai ta ji ita kan ta bata buƙatar magana ko da Leena ɗin ne bare zama inuwa ɗaya dan haka kowaccen su ta koma ɗakin ta dake sama.

"Ina tunanin SARINA ta samu Gocewar ƙashi Abban su,gashi sai kuka take yi"

REENA da jin haka kuwa ta ƙara fashewa da kuka dan sun taɓa Rakiyar Hamrah da ta goce aka yi mata gyara sai da ta yi fitsari a wando saboda a zabar da taji su kan su sai da suka koka duk rashin jituwar Leena da Hamrah ɗin sai da tayi mata kuka bare ma ita Reena uwayen kuka.

Yanke wayar ta yi cike da damuwa kafin ta ƙwalawa Rabi kira wadda ke kitchen suna aiki.
Da sauri rabi ta zo.
Sai da ta gama sauraren Maganar Ummah kafin ta ce " Subhanallah Alinatu baki kyauta ba samm ji bi yadda yar uwar ki ke kuka ".
Tana jin abinda Rabi ke faÉ—a amma bata ko kalli sashen da take ba sai ma cigaba da cin chocolate É—in ta,tayi tana turo baki gaba wanda ke nuna tana jin ta sarai.
Ummah ce ta katsa mata tsawa hakan ya sa ta É—an zabura dan ta fahimci iskancin LEENA gaba yake yi.
Sai kuma ko me ta tuna sai ta sassauta murya cike da Rarrashi ganin yadda LEENA tayi Narai Narai da idanu alamar kuka zata yi.
" Haba ALINA dubi yadda kika ji ma yar uwar ki,yanzu kenan nasihar da na ke muku a ban za,ace akan chocolate da gashi nan a ko ina an saka muku shine kika karya mini hannu Yarinya, Alina kin kyauta kuwa,Dubi yadda take kuka ita kaɗai ta san zafin da take ji dubi yadda hannu ke walƙiya har ya fara Kumburewa ".

" Ummah ai Chocolate É—in ya Samir ne kuma itama ai ya bata nata shine ta shanye nata,kuma zata shanye nawa mayyar ".
Bakin ta Ummah ke ƙoƙarin kaiwa bugu Rabi ta hana dan ta ji Haushin kalmar mayyar da ta kira wa Reena ɗin.

" Wato ke Bakin ki bai da saiti ALINA,kin cewa Ya ta Ɓarauniya gashi ko biro ba bata taɓa ɗaukar min ba,yanzu Idan Bilal ya dawo sai ki masa bayani ,dan a wannan karon ba zan raba ki dashi ba tun da na gane har yanzu kin kasa yin hankali ko Tausayin ta ba kya ji kin ƙara daɓa mata wannan muguwar kalmar,kuma kar naji,ko na ƙara gani kin kira wa SARINA wayen nan sunayen ko makaman tan su,ko Abban ku wannan karon bana fatan ya ɗaga Miki ƙafa sakarya "

" Rabi riƙa ta ku tafi Driver ya kai ku bari na ɗauko kuɗin gyaran ".

Miƙewa Ummah tayi ta haye upstairs da ɗan sauri ko kallon Sashen da Leena take tsaye bata yi ba wadda ko gizau bata yi ba hawayen ma yaƙi sauka idanun ta sun bushe babu ko alamar hawaye a idon ta ko ɗigon Tausayin Abin da ta yiwa Reena dan a cewar ita ta nema tun da ta taɓa mata abun ta.

Rabi kuwa riƙa Hannun REENA tayi bayan ta karɓi kuɗin hijabin ta da ɗauko ta sanya tare da ɗaurawa LEENA gungun mayafi da Ummah ta ɗauko mata daga bedroom ɗin ta.

" Baba Rabi Zanje ".
LEENA Ta furta cike da ƙuruciya da rashin damuwa.
Rabi saƙaƙe tayi tana kallon ta ganin ƙarfin halin ta kafin kuma ta ce " fito muje ". A zuciyar ta kuwa tana mata addu'ar shiriya daga ita har Reena da samun haɗin kan yan biyun.

" Wallahi babu inda zata bi ku,ta zauna gida,gashi ma BILAL ya min saƙo ya iso lafiya,ina son ya karya da ita dan uban ta,bari ma na masa saƙon abun da tayi yana isowa yayi mini maganin ta sha sha shaar yarinya ".

Rabi kuwa jin Ummah ta rantse ga ɓacin rai da ta gani kwance akan fuskar ta hakan ya sa babu musu ta fice tare da REENA ɗin.
Wadda ke cigaba da rera kukan azaba.
Junaid ne suka ci karo dashi zai shiga Sashen su kuma sun fito ganin yanayin da REENA ke ciki hakan ya sa ya bi su tare a gaban sa aka yi komai dan kuÉ—in ma shi ya biya duk da rabi ta nuna masa Ummah ta bada kuÉ—in.
REENA ta sha kuka ƙiris ya rage ta yi fitsari a wandon ta saboda azaba.
Dukkanin su sun tausaya mata matuƙa fuskar ta, take tayi jaa idanu suka yi sutu sutu gwanin ban tausayi.
Junaid yayi ta tambayar Rabi matsalar ta auku.Sai dai ta yi ta masa kame kame.
Hakan ya sa ya share bai ƙara tambaya ya fahimci bata son sanar masa.
Chapter 67 · 0% Book details