← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 110

Sashe 101

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Ke kar ma na ƙara jin maganar a zumin nan bakin ki ibada ce ta zama dole gare ki,dan haka ki rufe mini shi ko na haɗa dake da shi na zane ".
Inna ni ta kai ƙarshen zancen tana haɗe fuska.
Shatou kuwa ganin tana neman tono rigima hakan ya sa ta yin shiru tana ƙyafƙyafta idanun ta tana ƙara cunna bakin ta gaba.
Baffa na dai murmushin kawai yayi.
" Ke zo nan ma na huta da shirmen ki riƙa mun aikin nan ".
Cewar Inna ni dake aikin Yankan ganyen Alayyahu na miyar sahur.
Baki tunzure ta miƙe ta matsa ta ɗauki kabewa ta fara feɗewa sai dai Inna ni na lura da ita yan kan kabewar da ƙeta ake mata shi dan cizgar ta take yi kamar Allah ya aiko ta da wuƙa mai kaifi da aka heƙo musu ɗazu dan haka duk ta kusa zabce rabi da nufin tana ferewa ita kuwa Inna ni kai kawai take girgiza wa tana mamakin yadda za,ayi ace kamar Shatou bata son yin A zumi duk da ba laifin ta ba ne na mahaifin ta ne domin kuwa da ace ya saka mata hannu tun chan da,ai da tuni ta gwane,ta saba da juriya Amma yanzu budurwar yarinya da jinin ta da komai balagus duk wata ace a tana rakin a zumin da ko ɗaukar sa ba,a yi ba.Har take iƙirarin ba zata yi ita dai ba.
Kai Inna ni ta girgiza tana sakin murmushi a cikin zuciyar ta idanu ta zaro da ƙarfi ganin yadda aka mayar mata da kubewa yar ƙarama yar cika aiki ta zabce rabi aiko babu arziki ta ce " Ta shi je kai geron dawo na furan gobu, wannan aiki dai babu niyyar yin sa Nagde " .
Summ summ haka shatou ta saka hijab ɗin ta, tana turar baki tare suka fice Da Bibu sai dai ko kafin su isa ta wartsake ta saki jiki fushin ma na Inna ni ya sauka.✍️

Maganar gaskiya ba zan ɓoye muku ba Maman Abba na so na ƙwarai da gaske.🥺
Ita kawai ta damu da shiru na na kwana biyu.Ta zata ko ciwon na wa ne ya tashi lallai wannan itace soyayya ta gaskiya.
Naji daÉ—i sosai lokacin da naji muryan ta.
Ina godiya sosai uwata rubutu ya bani mutane masu daraja da ƙima a rayuwata.
Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana ya raya Miki zuriyar ki.I Love you uwata wallahi ina jin ta kamar mamata da ta haife ni Allah ya bar mu tare har a gidan aljanna.✨🙏❤️❤️💕

To subscribe yours contact this number
08069059746

_*KURMAN ƘADDARA*_

*_©®Faiza Almustapha Murai_*

_*FA'EEH BG*✍️_

P________4️⃣ 6️⃣↔️4️⃣7️⃣

*BOOK ONE*
*_FREE_*

*Follow me on*
*Wattpad@Faizamurai*
*Arewabooks@Fa'eehbg*
*Facebook@Fa'eehBg*

*Channel link*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y

*Posting group link*
https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t

_*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*_

💫✨💫✨💫

# Shatou/Iro
# Aiyah
# Mahaj
# Abbu
# Faiza Almustapha murai#
# fa'i✍️

Suna kai geron suka kamo hanyar gida.
A tare suka shigo gidan Bibu a gaba ita a baya suna dariya.
Da gardamar wanda zai je ya karɓo dan Bibu ne yaɗauki geron yanzu da zasu fita.
Ganin su haka ya sa Inna ni shanye murmushin ta na yar maganar da suke yi da Baffa na dan kar shatou ta samu damar ta.Ta ƙara samun damar wata magana.
" Inna ni mun dawo "
Cewar Bibu.
ÆŠan kallon sa ta yi ta saka murmushi kafin ta ce " Allah yayi muku albarka ".
" Amin Inna ni ".
Shatou ta amsa da ƙarfi tana sakin murmushi.
Inna ni dai bata bi ta kan ta ba sai yar hararar da ta sakar mata.Kafin ta ce
" Kamar fa jiya ne aka gama Ramadan Baffa na,Yau gashi cikin ikon Allah wani ya sake zuwar muna lallai lokaci babu wuya wajen Ubangiji,Allah ya nuna mana ƙarshen sa lafiya,ya yaye muna damuwowin mu ya kawo muna ƙarshen su ".
Ta kai ƙarshen zancen cikin wata raunatattaciyar zuciya wani shuɗaɗɗen lokaci na dawo mata da take ta ƙoƙarin ɓoyewa kan ta.
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ɗan ƙaƙalo murmushin ya ƙe jin shatou na furta " Kuma Allah ya sa Inna ni ki haifa mini yar ƙanwa ".Ta kai ƙarshen zancen tana dariya.Haka ma Bibu.
Baffa na ma ɗan numfashi ya sauke fahimtar duk inda addu'ar ta ta nufa da kuma abun da yake masa kai kawo a kullum da take ɓoyewa da yake ƙara shigar da ita damuwa.
Amin ya amsa cike da tausayi.
Kiran Sallah ne ya fitar da su daga gidan shida Bibu.Basu dawo daga masallaci ba sai bayan Sallahn Isha'i sannan suka dawo .
Koda suka dawo Su Inna ni sun gama komai har tuwon ta tuƙe abun ta wanda ta sha fira har ta gaji dan shatou kamar an buɗe bakin ta.
Sai kuma ta koma firar kayan Sallahn su da ke wajen É—in ki da kuma irin wankan da zata yi ranar.
Kafin kuma aka koma bata labarin Mahaj da ake kira Bature tana yi tana Harare Harare " Wai ni zasu yiwa turanci,nace musu turatu uwar Turai ai nima na iya"...
Shiru tayi jin Inna ni na cewa " You are not serious shatou ".Kafin kuma a hankali ta ƙara furta " You are too funny ".
Zuba ma Inna ni ido tayi kamar yau ta saba ganin ta kafin kuma ta buga tsalle ta ce " Inna ni turanci kika yi fa kema yau ".
Wani farin ciki ne ya ƙara bayyana kan fuskar shatou ita kuwa Inna ni ɗaure fuskar ta tayi kamar ba ita tayi furucin ba kafin tace " ke ban son shashanci,ni da ko aji ban ta ɓa zama ba ina zan ji Yaren Bature ai sai ku ".

Ɓata fuska shatou tayi kafin ta ce " Na fa jiki Inna ni ".

" A gidan wa kika ji ni shatou ".?

" Me na ce " ?

" Ce wa kika yi yom no siriyes sai kika saka suna na gaba "

Shatou ta yi maganar tana dariya dan ta kasa faÉ—a,itama ta san shirme ne ta haÉ—a duk da kalmar ta É—an shiga kan ta.
Dariya ce Inna ni tayi wadda ta jima bata yi ba.
Kafin kuma ta É—aure fuska ta ce cike da tausayin Shatou " Gaskiya ba ki ji dai dai ba shatou ".
Ɓata fuska shatou tayi jin furucin Inna ni.
Shiru tayi kamar mai nazari chan kuma sai ta ce " Haka fa kika ce to sai in Aljannun ki ne ko Inna ni ".
Baki sake Inna ni ke kallon ta kafin ta ce.
" Yau naga ta kaina ni matar salihin Bawa yau ni ce ake cewa mai Aljannu ".
Tsuru tsuru da ido shatou tayi wadda ta san ta kwafsa,tana tsoron Inna ni ta riƙo ta,dan haka ta zuba mata ido tana sauraren Inna ni dake ƙara furta " to wai gidan wa na same su "

" Ai ni ban ce fa kina da su ba,a gefen ki ƙila suke tsaye ".

Ɗan ja baya Inna ni ta yi kamar irin ta ji tsoro aiko shatou ta ƙyalƙyale da dariya tana cewa " Wallahi Inna ni kina da su " Ance duk mai tsoro yana da aljanu ".
Inna ni ma Murmushin kawai ta yi kafin ta girgiza kan ta sannan ta ce " Lallai ko ƙila sune kan,kiyi addu'a to".
Ai ko addu'ar ta fara dai dai lokacin kuma su Baffa na suka dawo nan suka zauna suna shan iska suna taɓa yar fira shatou na fara saka maganar firan su da inna ni akan turanci da ta ji ya fito bakin ta Inna ni dake lura da ita sai ta tare ta hana kuma duk wannan abun baffa na,na lura sai dai bai san me Inna ni take ƙoƙarin hana shatou faɗa ba,dole haka shatou ta haƙura,suka cigaba da wata firan har lokacin kwanciya bacci yayi kowa ya watse,kafin lokacin ma ta watsar da komai.
Koda lokacin Sahur yayi shatou da ƙyar Aka samu aka tashe ta sai da tayi nak sannan ta nemi waje ta kwanta.
Yadda kuka san taliya a wannan rana ta ɗai ga watan Ramadana haka Shatou tayi ta lauɗin yunwa kuma Inna ni na saka mata ido sosai ta lura shatou akwai tsoron Allah dan ta ga alamar bata sha komai ba ko cin wani a bu dan yau ma da asuba sai da ta ƙara nusar mata.
Yadda kuka san yini biyu haÉ—e haka shatou ta ga wannan rana.
Kowa ya kalli shatou sai ta bashi dariya dan haka ranar babu abinda ta tsinana wa Inna ni tun da suka dawo makaranta take sheme tana jin jiki.
Salloli ma da ƙyar take iya miƙewa ta yi su Ita dai Inna ni kai kawai take gyaɗawa cike da takaicin shatou.Da mugun tausayin ta da kullum yake ɗar suwa a ran ta.
Koda aka sha ruwa kasa miƙewa tayi saboda yadda ta shaƙe cikin ta tab Da ƙyar ta samu ta yi Magriba da isha'i ai ko,ko Fira yau bata yi ba bare ayi ashamm bacci ya kwashe ta yau ma da taimakon Inna ni ta kwanta,kamar jiya.
A ɓangaren Ishaa kuwa tun daga ranar ta ƙara zama shiru shiru babu ko alamar lafiya ajikin ta sai dai ta zuba wa waje ɗaya ido har Suhail da take ganewa yanzu ta daina kula shi dan haka yan kwanakkin nan duk ta fara ramewa saboda kafiya bata karɓan abinci ko kaɗan bare kallon sa.Idan aka matsa mata haukan ta ya ƙara ta shi tuɓuran.Dan haka yanzu komai da dabara ake lallaɓa ta domin babu wanda a yanzu baya yar ƙwalla saboda Tausayin MA'ISHA.Taimako kuwa babu wanda ba,a nema mata wanda ake mata amfani da shi cikin dabara...

A ɓangaren MAHAJ kuwa sun koma China kasancewar chan yake a zumi dama mafi yawan lokutta saboda karatun sa.
Sai dai ya kan dawo duk bayan É—an lokaci kafin fitar Ramadana wasu lokuttan kuma ya na yin sa gida.
Chapter 101 · 0% Book details