← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 110

Sashe 33

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ayya kuwa da sauri ta kaɓe hannun ta tana furta " ke tafi chan yar neman ga,Wanda bai san ciwon kan sa ba zaki saka kan ki dole kula dashi,shekarar sa nawa,Mahajjaci ai ba yaro bane,ada na wahala dashi amma yanzu babu garjejen ƙaton da zan wahala akan sa ta tafi ta bar mana jaraba,duk halin uwar shi ya gado " mstww taja mugun tsaki tana juyar kan ta gefe taana cigaba da kallon tsohon Film na hanyar Kano da ake haskawa a tashar ta Saira movie tana jan charbi a hannun ta.

Samra hawaye ne suka wanke mata fuska nan ta fashewa Ayya kuka,dama ta san ba lallai ta samu magana mai daɗi ba amma ta san yadda yake mugun jin maganar Ayya akan takowa a gidan.Ba ta san dalilin da ya sa Ayya take tsangwamar sa ba tun bata gane abun da ke yi wa ya yan na ta ba daɗi har ta kai ta fahimci inda ta dosa dan kai tsaye take nuna bata son sa duk da irin biyyayyar da yake mata saboda rabin rayuwar sa a hannun ta yayi ta,kuma tun yana ƙaramin sa yake cikin matsin Ayya har bai gane ba ya gane dan haka dai dai da rana ɗaya bai taɓa nuna damuwa saboda kallon uwa yake mata koda yaushe.

Miƙewa tayi da sauri bata ƙara cewa komai ba ta fice daga sashen tana Sharar hawaye.Sai dai tsaye tayi ganin wanda ya ke tunkare gaban ta,ta tare da jin ƙamshin sa da ya mamaye ko ina.Shi ɗin ne dai ya ke saukowa yana zuba ƙamshi ya sanya wasu irin kaya masu kyau da tsari kamar dai na sport riga da wando ash color da suka ƙara haska farar fatar sa mai sheƙi da ɗaukar ido.Cike da murmushi take bin shi da kallo har ya sauko.Ɗan sake fuskar sa yayi dake ɗaure kafin ya sakar mata lafiyyayen Murmushin sa yana shafa kan ta cike da son yar uwar ta sa da yake jin mugun Tausayin ta saboda yadda ta ke damuwa da lamurran sa dan ta kawai wasu lokuttan yake fitowa ya saka ma cikin sa wani abu dan ya san ta da naci yanzu haka ma.da ya ga hawaye a fuskar ta ya san daga inda ta fito dan haka babu tambaya,ya nuna mata shafaffen tumbin sa da kai kace bai taɓa samun wani abu a cikin sa ba.Fahimtar alamar da yake mata ya ci abinci ya sa ta sakin yar dariya ta jin daɗi ko bata tambaya ba ta san Chocolate ya ci saboda akwai shi da shegen son kayan zaƙi fridge ɗin sa duka sune shaƙe aciki babu kalar da babu.Ficewa yayi saboda yayi shirin sa tsafff dan zai ɗan motsa jikin sa ne da yake jin har yanzu yana masa babu daɗi.Dan haka yana tashi daga bacccin mara nauyi,ya ƙara watsa ruwa dan akwai wanka kamar moɗa.Chan baya inda field ɗin wasa yake ya nufa yana ɗan haɗawa da ɗan gudu.Dai dai lokacin suma su Salma da Sajida sun fito daga gurin sun gama buga ball kowaccen su da ɗan guntun wando.Kai ya ɗauke daga gare su tun kallon da yayi musu na farko.Su ko tsaye suka yi cike da jin haushin sa na share su da yayi gashi har haɗa baki suke yi wajen faɗin Sunan sa dan basu san ya dawo ba sai yanzu da suka gan shi.✍️

Duk abinda kuka gani kuyi Haƙuri ko editing na tafi ɗaya tafi uku nayi saboda yau ban samu na zauna ba.ngde

WANNAN LABARI NA KUÆŠI NE A MANHAJAR WAHTSAPP
*PAID BOOK 1k*
8069059746
Opay
Faiza Almustapha
Payment receipt
08069059746

Daga Alƙalamin
FirstLady 🙌
Gimbiyar taskira 👑
Fa'eeh💞

Commente,and like pls 🙏

_*💋KURMAN ƘADDARA💋*_

_©®Faiza Almustapha Murai_

_FA'EEH BG✍️_

P..1️⃣7️⃣

*BOOK ONE*
PAID

*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*

*Channel link*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y

*Follow me on*
*Wattpad@Faizamurai*
*Arewabooks@Fa'eehbg*
*Facebook@Fa'eeh Bg*

Not edited🥺

✨✨✨

Cike da murna ta faɗa ɗayan falon na Amma da yake ta upstairs ɗin da yake gefen hagu.Ganin ta hakan ya tabbatar ma Àmmah da ta samu abun da take so dan haka ta girgiza kai cike da murmushi dan ba ma sai ta mata bayani ba ta fahimci komai.
Ƙaramin tsaki Sajida ta saki,ita kuwa Salma murmushi ta yi na farin ciki ko ba komai ai sun samu ganin sa tunda tsada yake yi dan shi ma suke yawan fitowa wajen wasannin basu san dalilin da yasa bai sake musu fuska kamar yadda yake sakewa Samrah ba har Sajida zata bi bayan sa Salma ta riƙo hannun ta tana girgiza mata kai.Kallon ta tayi kafin taƙwace hannun ta tayi gaba hasale dan ta ji zafin wulaƙancin da yayi musu,ita ba kowane ta ke ɗauka ba dan ma bata ga fuskar raini ba da tuni MAHAJ ya ga rainin ta.

***

A ɓangaren SHATOU yau ta tashi da wani irin mahaukacin ciwon ciki da ya ke neman ganin bayan ta,duk murnan bikin sunan da zasu tafi na maman ramata bata sami zuwa sabo da yadda ciwon ya sako ta gaba ko maƙiyin ta sai ya tausaya mata.
Ta zama Abar Tausayin Inna ni da Baffa na iya kar ƙoƙarin su kawai suke yi har ɗan chemist da suke dashi ya je ya siyo maganin ta sha banza dan yana lafawa da mintuna ƙalilan yaƙara tashi dan haka suka zuba ma sarautar Allah ido domin kamar ciwon bai jin magani gashi baiwar Allah duk ta ƙara lanƙwashewa.Shatou tayi Kwana kusan huɗu tana fama da wannan ciwon babu wani sauƙi sai ana biyar ne ta samu da ƙyar ta miƙe ta shige toilet wajen fitsari bayan ya ɗan lafa mata sai dai,me ƙara ta saki ganin abinda yake fita a jikin ta bayan fitsarin.Inna Ni dake tsakar gida cikin ɗan jin daɗin miƙewar da tayi ta taso da sauri dan ita kaɗai ce a gidan,sai SHATOU.

" SHATOU lafiya kuwa,ko jikin ne ".Inna ni ta furta bayan samun kan ta tsakiyar makewayin.
Miƙewa tsaye Shatou tayi dan kamar an zare mata ciwon jikin ta lokaci ɗaya haka ta ji sai ta ɗan samu sauƙi.

Idanu Inna ta zaro cike da farin ciki kafin ta riƙo hannun ta tana ayyana wa aranta wata sabuwa.Dan wani sabon aiki ne ya same ta bata taɓa tunanin Shatou zata iya shiga wannan yanayin yanzu ba ta yi tunanin sai shekarun sun ƙara yin gaba duba da yanayin ɗan jikin na ta.

" Ji rani nan "

Inna ni ta furta fuskar ta cike da murmushi.Kafin ta fice daga bayin.

SHATOU kuwa hawaye ne har yanzu suke silalar mata duk da yanzu ta tuno da wani karatu da wani malamin su yayi musu kan wannan abun da ya same ta sai hankalin ta ya ɗan kwanta yanzu ƙyanƙyamin kanta take yi sosai dan haka take tsaye hawaye na silalar mata musamman ganin yadda jinin ke bin ƙafafun ta saboda na farko ne yana mugun rushing sosai.

Ɗauke da wando ta shigo tare da Wani ƙaton tsumma da ta yanko wani zanen ta wanda bai ji jiki ba.
Nan ta kimtsa Shatou da ke ta hawaye bayan ta bata izinin yin wanka dan har da ruwan wanka ta haɗo mata tana gama yin wankan ta saka komai gaban ta kamar yadda ta nuna mata.Ganin hawayen yaƙi tsayawa ya sa Inni ni furta " Ni fa kin ishe Ni,haba,Girma fa ne ya kama ki,dama so kike ki ƙara girma ai, yanzu zai zo lokacin sa yazo,tunda baki son ana ce Miki ƙarama " Ta kai ƙarshen zancen tana sakin yar guntuwar dariya.Baki Shatou ta turo gaba tana jan majina.Kafin tayi gaba ta baro Inna ni cikin toilet ɗin tana wanke kayan ta da ya lalace wando da rigar.

ÆŠaki shatou ta shige ta yi kwanciyar ta saboda duk jin ta take yi a takure kamar an manna mata wani mugun abu ganin take yi motsi kaÉ—an zai iya saka abun ya faÉ—o dan haka ta takure waje É—aya.

Maganganun Inna ni kuwa da ta yi ta jera mata suna dawo mata kan kunne.Zantuka ne masu cike da gargaɗi da tsoratar wa.Dan haka taji ko wajen bata son fita domin Inna ni ta nuna mata kuskuren da ke ciki koda ace hannun ka ka bari wani ya taɓa wanda ya wuce Bibu da Baffa na.
Duk dai wani yanayi da kuka sani farin shiga yana samun kan sa ciki haka SHATOU ta tsinci kan ta cikin yanayin mai takura.Tana cikin tunanin zantukkan ne wani irin bacci ya kwashe ta.
Inna ni kuwa cike da tausayi haka ta wanke kayan na Shatou ta cigaba da ayyukan gaban ta dan ta samu É—an kwanciyar hankali ko ba komai ciwon ya tafi tunda dama wannan ne dalilin wahalar ta ta ita bata ma lura ba tunanin ba bai zo ga kan ta ba a tunanin ta ko ma wani abun ta ci a waje basu sani ba.
A haka koda Baffa na ya dawo shida Bibu sun ji daɗi sosai ganin Yadda Inna ni ta sake Sosai babu wata damuwa kan fuskar ta hakan ya tabbatar musu da Shatou ta samu lafiya,dan haka ya jikin ta kawai suka ƙara yi mata sannan.Nan ta sanar musu da ta ji sauƙi ta samu bacci ma suna tsaka da zancen kuwa sai ga ta ta fito tana yaƙune fuska tana wani haɗe ƙafafu.Duka zuba mata idanun su kayi cike da tausayinta ganin yadda ta ƙara yin fayau da ita har ja ta ƙara yi kamar wadda aka kwalhewa jinin jiki.

" Ya jikin SHATOU "?

Cewar Baffa na.
Cike da murmushi ta amsa masa tana zaro ido jin kamar abinda ke fita jikin ta zaya zubo ƙasa saboda yadda yake mata rushing.

" Adda SHATOU lafiya kuwa kike zaro ido haka kamar wacce ta yi ƙarya,gaban mai gari " Ya kai ƙarshen zancen yana sakin ɗan guntun murmushi.

Hararar sa ta yi kafin ta mayar da kallon kan Inna ni da take ta kallon ta tana tsoron ta ce musu wani kan halin da take ciki dan haka ta zuba mata idanu tana fatan kar Surutun ta ya kai ta sanar da su duk da ta san dole ma zasu iya sani wata rana.Duk da ba abun ɓoyo bane.
Chapter 33 · 0% Book details