← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 110

Sashe 7

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai dai me kakkausar Muryar sa ce ta shiga Kunnuwan ta yana cewa " Don't dare try to move "
Numfashin ta ne take jin yana shirin yin sama bayan tabbatar da shi ɗin ne.Tsinewa Malam Adamu ta fara yi a cikin zuciyar ta tun kafin ta iya dawowa cikin natsuwarta,dan mugun tsoron yayan na su take yi matuƙa saboda yadda ya saka mata ƙahon zuƙa saboda rashin jin ta.Zama tayi kamar kace ƙyar ta gudu musamman da ta san bata da gaskiya.Da ta san yana cikin motar Nan da tuni ta bar faɗan nan har haƙurin ma zata iya bawa REENA har ƙasa ma ta duƙa mata idan ta kama.
REENA da ta shiga gaba itama da sauri ta juya tana kallon bayan motar bayan jin ƙamshin na sa cikin farin ciki take kallon sa tana " Wel come back Ya B. " Shima da Murmushi ya Kalle ta yana furta ya " How are you girl ". "I'm fine ".
Ya studies ya mata ta amsa masa cikin sakin fuska kamar ba yanzu ta gama kuka ba.Shima haka ya saki ta sa fuskar.
Shiru ne ya ratsa motar bayan gama gaishe gaishen na su.
" LINA wai baki ga Ya B. Ba kika yi shiru ".
REENA tayi zancen kai tsaye ita har ta manta da faÉ—an da suka yi ma murnan ganin ya'yan na su ya gusar mata da zafin jibgar da tasha.
LINA murmushi ta ƙaƙalo kafin ta ce " na gansa ai har na gai da shi,amma bari na ƙara masa sannun da zuwa ".Ta yi zancen a ɗar ɗar.REENA bata ƙara tankama ta maba sai ma sautin ƙira'ar Alqur'ani da ta fara bi da ya ke tashi daga cikin motar kaɗan kaɗan.
Ganin kamar hankalin sa bai kan ta hakan ya sa a hankali ta furta " Ya .B Barka da dawowa Ina wuni ".
Yi yayi kamar bai ji abun da take faɗa ba ya share ta har sai da ta ƙara maimai ta sunan na sa kamar zata yi kuka cike da Haushin da ta ƙunsa na share ta da yayi.
" Kunnuwa suke ji ba " Kuma kika saka mini kuka na ci uban ki yanzu wajen nan ƙatuwar banza mara hankali ".Shiru tayi kamar ruwa ya cita jin yadda ya jefo mata magana kamar jiran ta yake yi dama kuma ta san za,a rina tun da ya gan ta da idanun sa kan ruwan cikin REENA yar gaban goshin sa tama jibgar ta kamar ta samu aikin yi.
ÆŠiff tayi kamar ruwa ya cita tana turo baki gaba haÉ—e da gunguni tana kallon glass É—in mota da suka É—ai suke iya hango na waje tinted ne glass É—in motar shi yasa basu lura da Bilal É—in a cikin motar ba.
Har suka isa gida babu wanda ya ƙara furta komai sai dai hankalin LINA ya ƙi kwanta wa ko kaɗan burin ta ta samu ta gan ta kusa da Ummah lokacin ne zata san ta tsira.Wata ƙatuwar mension ce mai tsari da burge wa wadda take cike da gidaje na alfarma masu kyau motar ta kutsa Hancin ta bayan wangale mata gate.
Tsarin gurin gwanin burge wa irin yadda kuka san estate take ko ina ƙalƙal sai sojojin da ke wulgawa kaɗan kaɗan saboda a ciki saboda mai gidan su da yake gari.Ganin sojojin da yawa ya ƙara tabbatar mata da ya dawo kenan,kuma da alama zai daɗe gida,dan ƙwarori ne suke tsaron estate ɗin amma daka gansu da yawa to yana gari.
Dai dai mazaunin motar ya yi parking motar wanda ko ida dai dai ta parking bai yi ba ta fara kiciniyar fita motar da iya ƙarfin ta.Baba Adamu da ya fahimci saurin na ta sai ya cire lock ɗin yana sakin guntun murmushi.Aiko kamar jira LINA take yi ta banka aguje cikin wani gidan da yake ɗan kusa da parking lots ɗin.Yana dai dai ta Parking ɗin REENA da ke ta sakin murmushi tana jiran ya'yan nasu su fita tare yana fitowa itama ta fito tana tsalle tsallen ta tana jin kamar yanzu ta ga ya yan nasu da ya kan ɗan kwana biyu bai garin saboda yana yin aikin sa Kasancewar sa Land army na ƙasa bai cika zama ƙasar ba ma.
Guntun Murmushi ya saki yana kallon REENA kafin ya riƙo hannun ta ganin yadda take ta tsalle tsalle sannan ya furta " Ki Nutsu kinji " Natsuwa kuwa tayi kuwa tana cigaba da sakin murmushi.A tare suka shiga cikin ƙaton falon jakar ta sargafe a bayan ta ga datti jikin ta duk ya bayyana.
Da gudu ta faÉ—a jikin Matar da ta fito daga kitchen tana kitchen tana amsa waya Fara ce tass kamar Bilal da REENA sai dai kama Bilal ya fi kama da ita sosai bisa ga su LINA da suke kama sosai da mahaifin su.
" Ummah I miss You "REENA tayi furucin tana dariyar farin ciki.

" Oh ni Barirah bint Usman Wai yaushe SAREENA ta zata yi hankali ne ALINA ta shigo a hargitse,REENA kuma ta dawo da datti me ya ɓata jikin ki haka ne,Ke da kika fita tsafff ".Ta kai ƙarshen zancen tana sakin murmushi mai cike da natsuwa
Tana zare ma REENA school bag É—in tana kallon Bilal dake murmushi shima jin mahaifiyar su ta kira cikakken sunan ta.

" Ummah FaÉ—uwa nayi " REENA ta furta itama cikin murmushi.
Hararar wasa Ummah ta sakar mata kafin ta furta " naƙi wayon Wannan akwai alamar rashin faɗuwa jibi yadda kika yi busu su fa gashi idanun ki sunyi rau rau kamar sun yi kuka,anya kuwa ba halin kuka yi awaje ba keda wacchan shiryayyar ".

Kallon Bilal tayi tana tsoron ta faÉ—a wa Ummah ya kama LINA ya daka duk da ta san may be ya riga ya gansu.
Bilal kuwa yi yayi kamar bai san maganar da ake yi ba ya mayar da hankalin sa kan wayar sa.

" Ummah faɗuwa fa nayi,shine LINA ta mun dariya na yi kuka ".Ta kai ƙarshen zancen tana yar shagwaɓarta.

Murmushi kawai Ummah ta saki tana furta " to jeki ki watsa ruwa idan kuka yi sallah sai ku fito yin lunch ga ya yan ku nan bai ci komai ba ya dawo ya matsa sai ya fara ganin ku jeki, kuma LINA ta tabbatar ta fito yin lunch ".Ta san tsafff zata ƙin fitowa tunda basa ba maciji da ya yan na su.Duk yadda ake firar sa kullum baya nan da ya dawo sai ta fara ɓoye ɓoye na rashin gaskiya.

Dariyar farin ciki ce ta kama REENA jin ya yan su bai ma iya yin lunch ba sai ya fara ganin su hakan ya sa da gudu ta bar falon tana tsallen murna ya nason su sosai.
Idanun sa ya bita da su yana sakin murmushi a hankali kafin ya maida kallon sa ga Umma ya ce " Ummah Barka da hidima "
" Barka da dawowa Soja,na san kaga komai da ya faru faÉ—an suka yi ko ".?
Tayi mishi zancen cikin sanyin da jikin ta yayi ta sigar tambaya tana zuba masa idanun ta.

Idanun sa ya ɗauke daga na mahaifiyar sa yana sakin ajiyar zuciya saboda ya san sune Raunin ta matuƙa waɗannan yan biyun ya yan na ta ya rasa abinda yake damun su musamman LINA kamar mai ƙwanƙwammai haka take wasu abubuwan wata rana ma kamar mai taɓin hankali dan so da yawa ya sha kama ta tana wasa ita kaɗai tun bata fara kai haka ba,ita kuwa REENA sangar ta gashi saboda mugun faɗan su abun ya zamar ma mahaifiyar su faɗe a cikin familyn da kishin samrin ta da kuma kishiyoyin ta ta rasa yadda zata yi maganin matsalar amma abu ya faskara sai gaba yake yi.
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya furta a hankali cikin natsuwa " UMMAH dambe suka yi " nan ya labarta mata abun da ya gani da idanun sa.

Kai UMMAH ta jinjina kafin ta sauke ajiyar zuciya " tana furta kwana biyu naga an samu zaman lafiya amma ashe abun gaba yake yi ,Allah ya shirya mini su,Dan ALLAH Karka dakar mini "Yaa Kaji Soja,Addu,a kawai zamu cigaba da saka ta,gaba É—ayan su ma ".

Kai ya jinjina yana furta " Amin " Amma tabbas da badan Mahaifiyar su ta hore sa ba da sai ya hora LINA sai tayi kamun kunne wanda zata daɗe bata yi rigima ba,tuna cewa ya sha hora ta amma bai yi aiki ba sai Shegen tsoron ta ya sa shi girgiza kan sa kawai yana tuno wani lokaci da ta yi wa REENA wani irin duka kamar zata raba ta da duniyar ta kan kawai ta sanya hular ta tace ta cire bata cire ba.Ai ko ya wahalar da ita kamar yadda suke yi a wurin training na sojoji ta wahala sosai harda jinya amma bai hana ta koma ba.A.lokacin kaɗan ya rage ya sha mari ga UMMAH dan Abba faɗa kawai yayi masa na ya riƙa haƙuri,ƙucuciyar ta ce haka, LINA taci baƙar wuya da ƙyar take iya tafiya a lokacin har sai da tayi kusan sati bata iya tafiya lokacin suna da shekara takwas ciff a duniya.

miƙewa yayi bayan Sun gama maganar shima ya wuce na sa sashe dake part ɗin duk da yana da ɓangaren sa kuma achan yake sauka idan ya zo ko sashen Abba Babba duk da gidan ba kowa a cikin sa.
Chapter 7 · 0% Book details