← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 110

Sashe 52

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau kwanan ta ɗaya biyu a asibitin dan riƙe ta Suhail ya sa aka yi ta ƙara samun sauƙin raunukan ta,sai ka sallami rabi kawai sannan suka Bata hutun kwana biyu.Dan haka suke bata allura mai ƙarfi bayan lokaci zuwa lokaci dan brain ɗin ta ta samu hutu mai kyau.Tunda ta buɗe idanun ta ta ga haske tar ko ina ta fara kiciniyar ƙwace kan ta idanun ta na rikiɗewa suko ma jajir da su kamar an baɗa mata barkono.Babu kowa ɗakin dan haka ta samu ta ɓalle duk jone jone dake a jikin ta Wanda Likitawa suka yi.Su Suhaila dake waje basu san abunda ke faruwa ba sai dai ganin mutun kawai suka yi ya fito a guje,cikin kiɗima da razana suka bi bayan ta cike da tashin hankali ita kuwa gudu take ta rusa akan babban coridor ɗin da zai fitar da kai daga sashen su.Ta ke hular kan ta,ta zare gashin kan ta ya barbaje har akan fuskar ta saboda kafin su zo nan an walwale kan ba,a samu aka kitse ba aka bar shi haka dan ba ta ma bari aka taje shi ba.
Dabb haka kan ta ya bugi ƙirjin sa,ɗan rufe idanun sa yayi kafin ya buɗe su,ita kuma a lokacin ta samu ta zare jikin ta ƙara fallawa a Guje sai lokacin ya an kara da su Suhaila dake kuka sun zo sun gifta ta sa ita da Nurse Mira sai nurses guda biyu mace da namiji su ma a bayan su ɗan yanayin gefen fuskar ta da ya ɗan gani yake son hasasowa tare da tunanin wace ce cike da tausayin ta yanayin ta dan yanayin da take ciki ya nuna Zallar Hauka ce,yanayin da ya samu kan sa ne a lokacin da jikin su ya haɗu ya san ya shi sauke a jiyar zuciya da numfashi yana mamakin abun da ke tattare da wannan mara lafiya da tausayin ta ya dabaibaiye shi kiran wayan shi da aka yi ne ya sa ya cigaba da tafiya ba tare da ƙara kawo tunanin komai ba sai dai zuciyar sa cike take da tausayin take,haka kawai ya ji ina ma yaga fuskar ta.
Gaba yayi yana amsa waya hankalin sa kwance.
A ɓangaren su Suhaila kuwa da suke cikin tashin hankali da gigicewa dan yaune rana ta farko da ta samu damar yin irin wannan gudun wanda take nuna alamar ɓacewa daga gida dan tana nuna son guduwa sai dai yau ne kawai ta samu dama dan chan iyakar ta compound saboda tsaro.
Da wani irin karfi ya fisgota bayan ta ɗan gota shi kaɗan daga tsayen da yake,dan ya daɗe tsaye wajen yana kallon tafowar tata a inda yake saboda bai daɗe da shigo wa ba sai dai a ƙafa yake dan taxi ta sauke shi a bakin gate dan ƙa'idar su ce ba,a shiga da ita,dan dawowar ta sa bai sanar ma da kowa ba bare a je ɗaukar sa ko driver ban sa bai sanar ma ba.
Ƙammmm haka ya rungume ta a jikin sa yana sauke a jiyar zuciya cike da tausayin ta ga wasu hawaye masu zafi da ciwo da yake jin suna neman sauka akan fuskar sa.Su ko su Suhaila chak suka tsaya zukatan su na musu wani irin raɗaɗi da ƙuna ga su kowaccen su fuskar ta tayi haja haja saboda kuka da fita hayyaci dan sun san muddin ta hau hanya su kan su ba su san yadda za,a iya kama ta ba.
Numfashi suka sauke ganin wanda ba su zaci gani ba a lokacin,Nurse Mira Murmushi ta saki haka ma Suhaila Rayyan ma da ya shigo yanzu murmushi yayi cike da farin ciki dan ya na shigowa ya hango su a Guje itace gaba kafin ya san abun yi sai aka yi sa,a shima Ya na kusa.
Kiciniyar ƙwace kan ta take yi sai dai ya ƙi bata damar hakan dan riƙo yayi mata bana wasa ba.
Daga ƙamshin turaren sa ta fahimci shine sai dai a idanun ta a wannan yanayin babu abun da suke da buƙatar gani face ta tsince ta a inda take ganin kan ta a cikin idanun na ta.Addu,oi yayi ta tofa mata dan ƙara take ta saki ta na gaɓɓatan dariya kafin kuma a hankali hawaye masu zafi suka silalo mata suka sauka aƙirjin sa idanun sa ya rintse da ƙarfi da suka yi jaaa abun ka da farar fata fuskar sa tayi jaa na damuwa da baƙin ciki na yanayin da ƙanwar ta sa take ciki.
Jin da yayi jikin ta ya saki hakan ya tabbatar masa da cewa tayi bacci dan haka ya durƙusa ya ɗauke ta dai dai nan aka kawo kujerar marasa lafiya daura ta yayi ya gyara mata zaman kafin ya bi bayan Nurses dake kula da ita.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya amsa sannu da zuwa da Rayyan yake masa.
Su Suhaila ma sannu da zuwa suka masa bayan sun isa inda Sashen na masu ciwon ƙwaƙwalwa yake.

" Captain manya yau nake ganin idon ka ".

Murmushi matashin da aka kira captain yayi kafin ya shafa kan sa.Hannu suka haÉ—e waje É—aya cike da murmushi.

" Wallahi ko ayyuka sun yi yawa yanzu ma dole ce ta kawo ni nan Yaqub ".

" Kuna da patient ne anan halan " ?

"Eh wallahi wani ma'aikacin mu aka kawo sun samu accident to abun kamar ya taɓa brain ɗin sa shine na shigo,idan ka lura tafiyar ma ta wa ce ni kaɗai "

Kai yaqub ya jinjina kafin yace " Allah ya bashi lafiya,Nima na zo ganin Patient ɗin mu ne ta kwana biyu nan Ni sai yau Allah ya kawo Ni dan bana ƙasar na yi tafiya kwana biyu,Yar wajen Yaya na ce itama tana fama da matsalar ƙwakwalwa abun ba,a cewa komai gashi na ta tun tana yarinya har yanzu babu wani cigaba "
Ya karasa zancen cikin alhini.
Cike da tausayi saurayin da aka kira Captain ya ce " Allah ya basu lafiya ya sa kaffara ne ya kawo karshen wahala ".
" Amin ''
Yaqub ya amsa
" Bari kawai muje na gan ta sai na wuce tunda har mun haÉ—u sai ayi zumunci ".
Kiran wayar sa ne ya katse maganar da Yaqub zai yi.
Cike da ladabi ya gama wayar kafin ya sara yana kashe wayar.ya kalli yaqub da ke jiran sa su wuce yaga patient É—in ta sa ya ce " Sorry Yaqub Wallahi na samu kiran gaggawa sai wata haÉ—uwar idan kuma na samu time zan zo na ga mara lafiyan ,Allah ya bata lafiya "
" Amin bakomai Captain sai mun yi waya " .Hannaye suka tafa kafin suka yi Sallama kamar kar su rabu,dan an kwana biyu ba,a haÉ—u ba.
Matashin da aka kira yaqub Shima gaba yayi yana caɓa car keys sama yana ɗan waigen Motar Captain da ta bar asibitin yana murmushi cike da kewar abotar ta su da suka yada kwana biyu kasancewar su class mate suna ɗan chat sai dai yanzu sun jaa baya.
Tsaye ya isko su cirko cirko Ganin Rayyan a kusa ya sa shi cewa " Lafiya Rayyan ko Jikin Isha ne ya tashi kuma ? Na gan ku cirko cirko ".

"Sannu da dawowa Uncle,Wallahi Uncle shine yanzu abun ya motsa mata ta fita ba tare da sanin kowa ba Allah ya taimaka Ya ya Suhail ashe ya dawo yau shi ya tare ta da bamu san inda zata je ba inda Allah ya takaita sai ya zamo a kwai mutane a kusa ".
Rayyan yayi zancen cike da damuwa da raɗaɗin da ke maƙare da zukatan su.
Cike da damuwa ya dafa kafaÉ—an sa yana cewa in sha ALLAH zata samu lafiya komai zai zama tarihi ganin hawaye sun kwaranyo a idanun Rayyan.

" Ina Suhail É—in " ?
Ya tambaya ba tare da amsa sannu da zuwan da yayi masa ba.

" Yanzu ya wuce office É—in sa " .
Kai Ya gyaɗa kafin ya matsa ya gaisa da su Suhaila da Nurse Mira ya musu ya mai jiki tare da ƙara musu ƙwarin guiwa dan kowa chan gida haka ya baro Amoh sai a hankali damuwa ta mata yawa dan ma sun hana ta zuwa ne da tana wajen.

Da Sallama ya shiga office É—in yana samun wajen zama dai dai shima Suhail É—in ya fito daga toilet yana gyara hannayen rigar sa da ya tattare hannayen da danshin ruwa da alama alwalla yayo.
Cikin É—an sakin fuska ya ce " Uncle Yaqub yaushe garin,? Ina wuni " ya faÉ—a cike da girmamawa duk da Uncle É—in ba zai wuce ya bashi shekara É—aya ba.

Murmushi yaqub yayi kafin ya ce "lafiya lau,ai Jiya na shigo tafiyar dare nayi dan haka ban faÉ—a ma kowa ba ".
" Naje gida ganin ku aka ce baka nan,suma su Rayyan suna hospital tare da Suhaila Saboda jikin Ishaa da ya tashi ".
Zama Suhail Yayi Yana Sauke Numfashi

" Ai da sauƙi ma dan yanzu tana samun isasshen bacci yanzu ma bacccin aka mayar da ita amma zuwa anjima zan mayar da ita gida kawai dan ma akwai wani likita da zai taimaka mini mu haɗa hannu mu cigaba da lura da yanayin nata sai dai ba nan ƙasar bane Canada yake dan haka nake son muje da ita idan mun gama shirye shiryen,ban ma yi magana da su Daddy ba ".

" Allah ya bata lafiya,jarabawa ce kowanne bawa da kalar ta sa ita wannan ce ta ta damu baki É—aya,Allah ya bamu ikon cinye wa ya kuma bada ladar É—awainiyya Allah kuma ya saka muku da Alkhairii ".

" Amin Uncle Yaqub ya hanya,kuma " ?
Suhaila ya faÉ—a bayan ya sauke ajiyar zuciya mai cike da wani irin rauni wadda Uncle ya ji ta sai dai bai wani damu ba dan ya san akwai damuwa sosai a yanayin sa zuciya dole sai ta hakan take rage nauyi musamman ga re su maza tun da basu cika zama su yi kuka ba.............
Chapter 52 · 0% Book details