← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 110

Sashe 18

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga Alƙalamin
FirstLady 🙌
Gimbiyar taskira 👑
Fa'eeh 💞

*_Typing_*

*💋KURMAN ƘADDARA💋*

*©®Faiza Almustapha Murai*

*FA'EEH BG*✍️

*BOOK ONE*

free pages👌

P..0️⃣9️⃣

>>>>>>>>>>>>>> > >>>>>>>>>>>>>>>

*CONTACT DIS LINE👉08069059746 FOR ADVERT.*

*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*

Channel link
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y

Posting room link
https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn

*LITAFFAN MARUBUCIYA*
*A MAFARKI NA SANTA*
*RAYUWAR MU A YAU!*

🍃🍃🍃

Haka aka kwashi A bukar sai gadon asibiti.
Har aka yi komai aka rufe margayiya Sakina bai farka ba sai dai Yan uwan ta ne suka yi jagora aka rufe yar uwar su.
A wannan rana wannan ahali biyu sun shiga tashin hankali matuƙa dan har zuwa lokacin A bukar bai farfaɗo ba.Haka ma jikin Mama ya tashi ita ma sai da ta ga likita dan Bpn ta ya tashi wanda ya same ta tun rasuwar mijin ta Saleh.
Su Sada sunyi kuka matuƙa haka ma A Bukar da ya farfaɗo a kwana na biyu yayi kuka kamar zai rasa ransa na rashin mata mace mai haƙuri da alkunya,da Biyayya wadda yake ganin ba zai taɓa samun maye gurbin ta ba a gare sa.
Bayan anyi zaman makoki Bukar ya sanar da Wasiyyar da Sakina ta bar masa duk da bai ce zai cika mata ba amma ya ji a zuciyar sa idan wannan zai saka ta farin ciki dole sai ya aiwatar ya cika mata burin ta.Dan ya san wannan shine burin ta tun farko ta bawa ɗan uwan na ta ya guda idan su samu rabo mai yawa sai gashi yanzu ta roƙi a ba su duka.
Bai nuna komai ba haka duk dangin suka amince mahaifiyar sa ma ce ta so ta hana wanda aka shirya da ƙyar idan sun yi wata ɗaya zuwa biyu za,a mayar da su wajen su ɗin.
Farin ciki kuwa Familyn Saleh sunyi shi kuka Uwani da Usman Saleh suka zauna suka ɓarza cike da kewa da Tausayin yar uwar su da zafin rabuwa da ita dan mace ce mai ƙima da daraja alkunya haƙuri.Haka Sadam da su Saleh, Ibrahim sun yi kuka matuƙa saboda shaƙuwar da ke tsakanin su da ƙanwar mahaifan ta su.
A haka yara suka taso cikin Gata da kulawa ta kowane ɓangare suna cika wata ɗaya kamar yadda aka tsara aka damƙa su hannun Uwani kamar yadda mahaifiyar su ta nema Uwani itace ta cigaba da shayar da Aisha da suke kira Maamaaa dama chan madara a ke bata.Barirah kuwa take ta sake dan bata fahimci komai ba ko chan baya koken ne da ta ga kowa nayi sai neman mahaifiyar ta ya sa ta kuka amma ba dan ta fahimci akwai wani abu ba,sai dai duk dare sai tayi kukan mahaifiyar ta.A haka har suka share watanni ta ƙarasa sakewa.Aka cigaba da rainon su a gidan Usman Saleh wanda tare da Sadam ake yiwa Maaamah komai saboda ƙaunar da yake yiwa jinjirar.Haka Barirah tana matuƙar son yar uwanta.A haka rayuwa ta cigaba da tafiya yara suna ta girma musamman ma Maammaa da take ta sowa itama gwanin burge wa kowa na ƙaunar su ita da Barirah sai dai tafi Barirah samun kulawa sosai saboda tafi ta saurin shiga rai.Da kuma sabo da sakewa ga mutane da faranfaran.Sunyi karatu na Arabia da boko a ƙarƙashin mahaifin Su da suke mugun so da ƙauna tun bayan fahimtar shine asalin mahaifin na su kasancewar ba,a bar shi baya ba gurin kula da ya'yan na sa abun son sa haka ma duka dangin na sa.Dan haka Suka ta so cikin gata basu san wani abu shi maraici ba.Kuma Basu taɓa nunawa Uwani da Usman Saleh basu ne suka haife su ba suna musu kara matuƙa musamman maama bata taɓa zancen mahaifiyar ta gaban Uwani saboda tana da fahimta da wayau,tana fahimtar yanayin da Uwani take shiga suka nuna damuwar rashin mahaifiyar su,suna kiran Uwani da Ummu,kamar yadda su Sadam ke kiran ta.Haka suka cigaba da rayuwa cikin yan uwan su har girman su.
Shekaru sun shuÉ—e dan lokacin Sadam ya gama karatun sa da ya yo akan kasuwan ci.Ita ma kuma Barirah ta kammala Tata makarantar a secondry.
Mama da Sada suka yanke hukuncin haɗa Auren zumunci a tsakanin Sadam da Barirah tare da shawarar mahaifin su dan dama su matan su basa karatu mai zurfi dan ko sakina da ƙyar suka barta tayi diploma a economics....
Lokaci mai jaaa idan akwai rayuwa a yanzu Saleh Sada ne mai tarin dukiyar da ko shi kan sa bai san kan ta ba,A yanzu yana da mata uku ta farko itace Hajiya Asma'u suna kiran ta da (momy)tana da yaaa ƙwaya ɗaya itace Hamrah,mai shekara goma sha ɗaya da rabi tana a ji ɗaya a junior sec,Dan su Reena suna gaban ta dama kaɗan dan dama sun girme mata kaɗan. Sai mai bi mata Hajiya Sa,ada ita bata samu rabo ba har yanzu.Suna kiran ta Mamy Sai kuma Hajiya Barirah ita tana da ya'ya uku na farko shine Bilal ma,aikacin soji ne yana matsayin Captain shekarar sa Ishirin da biyar sai yan biyu Alina da Sarina,suna da shekara goma sha uku suna aji uku a junior sec sch,Ibrahim Sada kuwa yana da Mata biyu ta farko Sunan ta Maryam Suna kiran ta (Hajiya)tana da ya'ya uku Maza,na farko shine Samir,yana aiki a Custom service,yana da shekara ashirin da huɗu,Sai na biyu Abdul jabbar,yana da shakara sha tara yana Ug II I a Wata Babbar University dake nan jahar su wadda ake zube ma Naira,sai Ayman mai shekara goma sha biyar yana aji Biyu ne a University wadda Abdul jabbar yake yi.Sai matar sa ta biyu sunan ta Ramlat suna kiran ta Momcy tana da ya'ya biyu Junaid,mai shekara sha tara yana aji biyu a University tare da su Abduljabbar suna mataki ɗaya sai dai kowa field ɗin sa daban.Sai Amina (Ninah) mai shekara sha uku suna matakin karatu ɗaya da su Reena.

🍃🍃🍃

*MU KOMA LABARI.*

Suna gama gaisawa da Junaid ya matsa kusa da tsohon yana rusunar da kan sa ƙasa yana cewa " kaina a ƙasa Sir S S ".Saboda haka suke kiran sa da Sir gaba ɗaya jikokin na sa.
Murmushi Yayi yana jan kunnen BILAL yana furta " wane SS É—in ne uban ka ko ni "

"Ouuch Sir pls " Ya furta yana ɓata fuskar shi.
Murmushi yayi yana cewa " Laifi muka yi ne da za,a shigo aka sa zuwa wajen mu ka san yanzu ƙarfe nawa ne,ohh kana sane ma".
Ya furta jin yana bashi amsa da 4:30pm.
Sakin shi yayi yana riƙe hannun sa na dama yana furta " Ya aikin " ?
" Alhamdulillah Sir ya tsufa ".?
"Tsufa ai sai ku BILAL mu yanzu muke Tashe na bai fi naka ƙwari ba ne " Dariya Bilal yayi yana furta " Haka ne Sir ai yanzu kake tashe ma " Ya kai ƙarshen zancen yana sakin guntuwar dariya.
Dai dai isowar su Abdul Jabbar da Ayman a wajen suma fuska cike da farin ciki suka rungume Bilal É—in suna haÉ—a baki wajen gaishe sa.Shima cike da murmushi ya amsa musu yana musu yan tambayoyi game da karatu suna amsa masa gaba suka yi bayan sun É—an yi barkwanci tare da gaida Sir.

Har Sashen sa ya kai shi anan ya tarar da Hajo zaune tare da mama da tsufa ya mayar da ita kamar yarinya komai sai anyi mata Uwani da ita suna ƙoƙari akan su duk da yadda su kan su tsufan ya taso musu amma suna ƙokarin faran ta ran surukar ta su.

"Ja'iri sai yanzu ka ga damar shigowa ko,ai ko Badan mu ba kana shigowa ka ga Uwar ka " Tayi zancen tana Murmushi tana nuna Mama da ke tauna goron da Hajo take daka mata a wani ƙaramin dutse mai kyau guda biyu wanda aka sawo mata shi tun da ga saudia kuma idan ka ji kuɗin sa zaka jima kana mamaki,shi an yi shine kawai saboda tsofaffi irin su da ba komai suke iya taunawa ba saboda yadda haƙoran su suka yi taushi,suka koma kamar dasashi irin dai na yaro ƙarami.

Ƙasa yakai yana murmushi tare da riƙo hannun Mama yana furta " Tsohuwa mai ran ƙarfe,Allah ya ja da rai da nisan kwana,ya ƙarfin jikin ".

Fuskar shi ta shaafa tana furta " ÆŠan ga ne,ka dawo me ka yo mini tsara ba,ya aikin ka ".

Ta jero zantukan da sai ka kwantar da hankali zaka ji fitar su a bakin ta.

"Ina nan Mama".Yayi zancen yana riƙo hannun ta.
" Me ke kika so dan ban siyo komai ba,irin na ki keda Hajo ma,da Sir "

Da ƙuwa Hajo ta sakar masa tana furta " Ai mu bamu yi wannan tsufan ba,baka gan mu garass ba ko goro Bama ci ".

Ta kai ƙarshen zancen tana tauna goron da ke hannun ta wanda bata daɗe da fara cin sa ba.

Dariya yayi yana kallon Sir da ke zaune yana kallon su yana murmushi musamman mahaifiyar sa da ke ta mamular bakin ta tana tauna goron da Hajo ta ke daka mata tana Murmushi tana sauraron abun da BILAL yake faÉ—a.

Itama Hajo murmushin ta saki.

" Ina son kilishi Samiru baya nan dama shi yake sayo mini shi "." Bani son na nan gidan bai min daÉ—i "
Ta kai ƙarshen zancen tana ƙara damƙe hannun sa.
" Kilishi kike so Mama,gashi ance likita ya hana ki cin jan nama Ba zaki haƙura ba ".

" A'ah nidai ka sawo mini Likita bai isa ya kashe ni ba,sai lokaci na yayi,Koh Sada ".

Kai Sir ya girgiza kawai saboda sun yi sunyi su hana ta abun ya gagara saboda tana fama da sugar likitota suka yi suggesting tabar cin nama jaa.
Ga su da naman kowane iri a gida har kilishin da sabo da tsoho kullum sai masu kula da Sashen nama sun yi shi dan haka akwai sabo akwai tsoho.Amma bata son shi saboda rigima sai na waje.

" Sir me ya sa kuke barin ta,lafiyar ta fa na iya ragwanta ".

BILAL ya yi zancen yana kallon Sir .
Chapter 18 · 0% Book details