← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 116

Sashe 99

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ta kalli rikon da ya yiwa hannayenta a kwoncen da suke yana kallonta ya ce" Me yasa kike kuka? In tashi in tafi bakya so na zo?"

Khausar ta turo baki tana yin yannayin tamkar yar karamar yarinya

A hankali ta ce" Ni ba kukan wannan nake ba"

"To menene? Baki da lafiya ne?" Ya fada a dan gagauce

Khausar ta zubawa fuskarsa ido, a hankali ta ce" Taufeek, aikina fa? Ka cema Hajia wai ba inda zan je, kuma ka ga na jima ban je ba, dan Allah TAUFEEK kar ka rabani da aikina, "

A bayane ya sauke ajiyar zuciya, da gaya ya dan tsareta da ido ya ce" To ki yi zamanki mana ba sai in ringa maki albashinki kina gida ba?"

A hankali Khausar ta girgiza kai ta ce" TAUFEEK ka fa san ina son aikina, kai shaida ne na irin yadda na kashe kaina na yi karatu, kuma kai shaida ne ina son aikin nan ko?"

Kai ya gyada yana kallonta
Khausar ta jimke hannayensa a hankali ta ce" idan ka rabani da aikin nan yaya zan yi? Ina iya yin kuka daga safe har dare fa, kuma zan daina cin abinci kwata kwata"

Ido ya zarro a hankali ya ce" Kin tabata? Cikin nan zai iya jurewa?"

Khausar ta ture hannunsa tana turo baki ta ce" Sai a masa dole ai , kuma in hau cen karshen karfen cen in fado in fashe!"

TAUFEEK ya idasa zarro idannuwan yana sakin dariya ya sake kallon karfen ya kalleta a hankali ya janyota jikinsa ya rungume sosai kasa kasa ya ce" Idan kika fashe Ni kuma in shiga ina?"

Khausar ta lumshe idannuwanta tana jin hannunsa na kokarin yawo a cikin rigarta, a hankali ta bude idannuwanta suka yi ido hudu kasa kasa ta ce" TAUFEEK washhhhh "

Tsigar jikinsa ta tashi d sauri ya sake matse mata waje muryarsa a shake ya ce" Khausar Please, i nd U"

Idannuwan ta mayar ta rufe tsoro na riskar kirjinta ama kuma ta ki hannashi, a hankali ta ce" Aikin nawa fa?"

TAUFEEK da ya fara yin nisa da kyar ya iya cewa" Zaki koma "

Khausar ta sauke ajiyar zuciya tana jinsa kamar zai haukata mata jiki
A hankali ta sake furta" TAUFEEK ina so in ga Abana kuma"

TAUFEEK ya dago rinanun idannuwansa yana kallonta a hankali ya hade bakinsa da nata sannan ya koma daga barin da zai fi jin dadin sarrafa ta
Wato a jiya sharar fage zan ce ya yi mata? Ko kuwa dan ya ga har ta iya kula da kanta da kanta ne? A yau dai ainahin maza a yau Khausar ta ji maza, domin tun tana kokari irin nata sai da ta fara fita a hayacinta jikinta ya nemi saki , hawaye kuwa wani ke kokar wani

Tana ji tana gani ya kaita bayi , ko daga hannunta bata iya yi da kyau , idannuwanta kuwa har sun sundume dan azabar da ta sha
A yau ne ta samu ainahin gashi irin na yan mata domin sai da ya tara ruwan ya sakata sannan ya koma ya cenza shinfidar gadon dan ba zai kwontu ba, lalle jikawar ta jiku matar jikan Hajia

Da kyar ta iya rukunkume jikinta jin yana sake shafar hannayenta

A hankali ta rintse idannuwanta muryarta bata fita da kyau ta ce" Kasheni zaka yi? Ka karani fa"

Murmushi ya yi yana ta lumshe ido, shi kam da zai samu kari babu abinda zai hannashi sake wanke goma ya dangwala biyar

Sosai jikinta ya idasa rikicewa da zafi da kuma zafin ciwon haka da ta sha
Duk yadda ta so karfafa jikinta bayan fitarsa da safe ta mike gazawa ta yi domin ko sallah sai da ya taimaka mata ta yi kuma ya bata magani har sau biyu ama zafin zazzabin ya ki sauka

Kusan karfe takwas sai gashi dauke da ledar magani da kuma flask din abinci

Sai da ya matsa mata ta dan taba sannan ya jonna mata karin ruwa ya zauna yana dan shafa gashin kanta har ta yi barci sannan ya fita ya ja mata kofar ya sauka ya nufi bangaren abansa dake nemansa zuciyarsa cike da tausayinta, gaskiya ya mata zuwa ne na gaske baiwar Allah ashe zata iya raunata haka

Zama ya yi nesa da Hajia dan ba wani son surutu yake yi da safiyar nan ba

Mikewa ta yi ta dawo daf da shi ta zauna kasa kasa ta ce" Ina kwana magidanci?"

Kallonta ya yi ya mata shiru , Abansa kuwa ya sakar masa harara dan sarai ya ji Hajia ce ke gaishe shi ya ki amsawa

Murmushi ya yi yana sosa keya ya ce" lfy kalu"

Mama ta kalle shi a zabure, tana mamakin amsawa ne ya yi? Kai jama'a shin yaya zata yi da rikicin TAUFEEK da kakarsa?

Aba ya yi kwafa ya ce" Zaka yi bayani ne Elhaji karami, nace zaka yi bayani ne!"

Hajia ta kalli Aba ta ce" To fa, daga zuwansa me ya maka kuma?"

Mama ta kalli Hajia da mamaki ta ce" Hajia kece zaki gaishe shi ya wani amsa ko kunya baya ji?"

Hajia ta kama haba tana kallonsu, sai kuma ta maida kanta kan TAUFEEK ta ce" Shi yasa nake maka maganin baki, kai fa farin jinin ka mai kwanonina da matarsa sun saka maka ido, wato bakinmu ake kallo a ga me muka ce, ta Allah ba ta mutun ba jikana ya fi karfin yawan maganar yan uba!"

Daga maman har aba suka kalli junna, Mama ta soke kai Aba kuwa mai zai yi banda murmushi
Ya gyada kai yana al'ajabin mahaifiyarsa

A hankali ya ce" Uhum, Yaya maganar tafiyar ne?"

TAUFEEK ya dago ya kalli Aba, sai kuma ya kalli Hajia, kasa kasa ya ce" Ba nace maki ba zamu tafi ba wannan shekarar?"
Hajiarma kasa kasa ta ce" to in na mutu kafin badin fa?"

TAUFEEK ya harareta a fakaice dan ƴaƴanta na nan ai, a hankali ya ce" Na fada maki ai da saura mutuwar in sha Allah, kuma Khausar fa bata da lafiya yaya zan tafi nan da yan kwanaki in barta? "

Hajia ta washe baki tana zarro ido ta ce" Kai haba, shafa min fada min ya faru ne?"

TAUFEEK ya tsareta da duban mamaki, kasa kasan nan ya ce" Me ya faru?"

Hajia ta zabga masa harara ta ce" Bafa na son wulakanci ka ji na fada maka!"

Shima ya daure fuska ya ce" Ni dai ki rabani da su, ke da zamu je yawon gannin turawa da ke? Abinda ga umura na zuwa ba sai mu je ba? Haba tawan"

Hajia ta yi shiru tana nazari, sai kuma ta kalli su Aba dake kallonsu kowane na so sai ya ji me suke tataunawa ama basa ji dan magana ce kamar ta munafunci rada rada

Sai da ta wani ci magani ta ce" Ni mai kwanoni zuwana hajin nan nawa?"

Aba ta kalli Hajia, shi yaya zai yi ya iya irgawa abinda tun mahaifinsa da rai ake zuwa ?

Da ladabi ya ce" Hajia ai an jima ana zuwa alhamdulilah"

Hajia ta ce" Masha ALLAH, wani abinma ai sai ya zama kamar barna, kudin bana a ciyar da marayu badi ma je Ni da Magidanci dan ba zaka hadani da matanka su batar da Ni Ko su buden tagar jirgi na fado ba, bale ita wannan tana kallo sai su zane Ni bata da karfi ko kadan bale ta kwaceni!"

Aba ya kalli TAUFEEK da kallo irin mai tafe da gargadin nan

TAUFEEK ya sada kai yana kikifta ido

Aba ya sauke ajiyar zuciya ya ce" to Hajia shikenan Allah ya saka da alkhairi ya bada kadan niya"

Hajia ta ce" Amen"

TAUFEEK ya sauke ajiyar zuciya ya kalli mahaifinsa ya ce" Aba, dama ina so na maka maganar su Yumnah ne, ina son raba masu gida idan har ba damuwa in sha Allah"

Hajia ta yi turus tana kallonsa , ta kalli Aba tana kikifta ido , sosai ta so kamewa ta ki shiga ama ta kasa ta ce" Yo a kan wace masifa, Allah na tuba ubaanka ba su uku ne a jere ba! A kan me zaka raba masu muhalli?"

TAUFEEK ya zuba mata ido, kasa kasa ya ce" Tashi ki bar nan kin ga ba da ke nake ba"

Hajia ta ja tsaki tana mikewa ta koma daf da Mama ta ce" Aikin banza kai babu fa yar da ta isa ta juyan jika ina raye, a kan wani shegen dalili zaka wara iyalinka iyi? Ni kuma a kaini wani gidan to? Aikin banza kawai!"

Aba ya rasa ta inda zai fara, mama kam dama ba cika tofawa ta yi ba idan ana irin haka, sai ya zamana Hajia da TAUFEEK sunna kallon junna ne kowa da abinda ke ransa

TAUFEEK ya gyara zama a ladafce ya ce"

Ku ji, kunna ji? Saura kiris🤗😂
💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

*DA CIWO A ZUCIYATA*

💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

_MALLAKIN_

*SAJIDA NIJAR*

*FREE BOOK NE* 6️⃣0️⃣

*GARABASA, GARABASA, PROMOTION, PROMOTION DIN LITATAFAN MARUBUCIYAR A KAN FARASHI MAI SAUKI 1K, YAN NIJAR KUWA 1000 FRANCS CEFA*

1: Duk karyar kada

2: Yar mahaukaciya

3: Neman na kaina

4: Bani da zabi

5: Bak'a ce

6: Kutkale

7: Makauniya ce

8: Mage

9: Duk nisan jifa

10: Idan ka raina inda kake

11: Dutse

12: Alkalamin kadarata

13: Bani da zabi

14: Dakika Biyar

15:Wata kokowar

16: Aure yakin mata

17: Ni zan ladabi

18: Daga tafia daukar soja

*Dukansu a kan farashi mai sauki, zaka saka dubu guda ne domin promotion ne nake yi, ka tuntubeni kan layina kamar haka +227 93 81 16 18, Sajida Nijar*

Now

*Da CIWO A ZUCIYATA*

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_
Chapter 99 · 0% Book details