← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 116

Sashe 21

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baban faranti mai dauke da kula biyu masu marfin kwalba rantsarsu ne Mama ta saka aka miko mata, a dan gagauce Maman ke bayanin dan yannayin taron kuma dama zata fita ne ta samu wanda ta yarda da shi ya kaiwa TAUFEEK abincin sai ga KAUSAR din, hakan ya sa ta juya da abincin su kuwa su A'isha suka bi bayan Maman domin ta ja su ne tana fadin" Ku zo ku kuwa yayana kafin ta dawo a shirya na bakin, ga mamanku cen a dakina da baki idan mun gama kwa gaisa"

A nutse take nufar hanyar bangaren Hajiar har ta karasa ta saka kafarta a hankali ta bude tana ta Adu'ar Allah ya kaita lafia domin takalmin kansa da take kai da kyar take rike kanta a sama, ga alkyaba ga kuma kwaliyar da take jin kunya kamar me wace tana ji a jikinta da wahala ta iya wuni da wannan hodar a fuskarta da sauransu

A hankali ta saka kanta falon tana yin salama

Jin salama ya saka Hajia dakatawa wace ke shirin shiga kicin sai fada take yi tana yadda hannun anma rainata a kan me za'a bar mata jika da yinwa har sha biyu? Lalle zata iya sabawa uwar ɗan nan, shine fa zata shiga ta ga abinda zata sama masa koda danwake ne kafin a jima a bashi tuwo sai ta ji salama

Da farko furkar ta zubawa ido, sai kuma ta shiga binta tun daga kanta har zuwa inda ya fi tsole mata ido da sakata zarro ido kamar zasu fado kasa

Da sauri ta yi ribasss ta juyo ta karasa shigowa ta zo inda TAUFEEK kw zaune da Alhhusain sunna dan zantawa ta zauna daf da shi hadi da riko hannunsa na hagu ta jimko da bakinta ta shiga nuna masa abinda take ganni yau ra'ayne da ayne

Alhhusain ne ya amsa salamar a bayane sosai yana juyowa, sai kuma shima ya dan zarro ido kadan dan har ga Allah da farko bai gane fuskar ba da yannayin har sai da ta saki murmushi tana idasa shigowa gaba dayanta ta nufo falon bayan ta cire takalman ta ce" Ka ga abokin ango, menene nake gannin ka yi wani laushi ko yinwar ne kaima?"

Hajia ta saki hannun TAUFEEK da ya irin cire kan nan ya ki kula KAUSAR ko kallonta bai yi ba shi kam wai fushi yake yi sai yanzu zata zo aurensa dan wulakanci, ta tafa hannayenta tana tare gefen kuncinta ta hade da dan kunnen zinarin dake kunnenta ta ce" Na ga annabi in na yi hali na gari, yar nan Ke ce? Dama haka kike ama kike lumbukewa a hijabi bakya ko shafa fankeke? Lah ha ila ha ilalahu muhamadu rasululahi sallalahu alaihi Wa salam ku duba ku ga halitar ALLAH a yanke masha Allah kamar kamar lah kamar mema zan ce ke ama kina kokari haka kike tafia ras irin nawa.......?"

KAUSAR wani irin tsuru tsuru ta yi tana kallon Hajia, TAUFEEK ya zubawa hajia ido kafin ya juyo da dubansa dan gannin meye wai ya saka hajia magana haka?, Alhhusain kuwa sai ya mike ya amshi farantin dan yadda ta yi sai ya so bashi dariya ta yi tsuru tsuru kar ta saki abincinsu , shi da kansa mamaki ya kasa barinsa haka kuma idannuwansa sunna matukar son kare mata kallo duda ya san hakan kamar ai ba daidai bane kau?

Ido ya zuba mata, fuskarta ita ta fi bashi mamaki, kwaliyar dake zane a saman fuskar nata ta fi bashi mamaki, sai dai bai san cewa abin mamakin a gaba ba sai da ya dan so gannin meye yankawar da Hajia ke fada ya dan kalli yannayin shigar jikinta a dan gurguje ba da nufin komai ba sai dan ya ga wani hijab ne ta saka wai HAJIA ke wannan surutun sai ya ga wani ikon Allahn da ya so sakashi kyatsa rantsuwar sam bamaa ita bace ta hanyar dauke kansa da sauri ya juyo barin hajia , sai dai yanna kallon Hajiar ya ga ta tsatsareshi da ido da duba wani kala daban irin marar kyau din nan kuma da ido tana aniyar neman yin tsegumi da shi bayan cin naman wani haramun ne dan haka ya kauce idannuwansa ya hade fuska sannan ya mike tsaye daga zaunen da yake ya daga kafarsa zai karasa sai ya ji hannunsa rike taf a na hajia,

Dubanta ya yi sannan ya kalli hannun nasa ya ce" Sakeni mana"

Sai a lokacin Hajia ta saki hannun tana sakin harare ta ringa lekawa ta ga ya karasa inda KAUSAR ke tsaye ya mata nuni da ta wuce ciki, sumui sumui ta yi cikin ta tsaya shi kuwa ya karasa ya tsaya gabanta da sauri yana hade fuska ya bude baki zai yi magana ya ga HAJIA ta masu tsuru tsuru sai zarro ido take yi hakan ya sa ya sake jin wani takaici ya lulube shi ya ce" Hajia meye wai?"

Hajia ta tabe baki ta ce " Meye kuwa, miya ce, me zaka fada mata ne?"

Ikon Allah....., Ya ayyana a zuciyarsa ya zamto sunna kallon kallo su ukun

Yannayinta da sanyi ta ce" Ka yi hakuri besty gidan kwaliya muka tsaya shi yasa fa bamu karaso da wuri ba, ka tambayima su Aisha "

Da bacin rai ya ce" Haka fa, gama katt na gani, yanzu meye anfanin haka KAUSAR? Kefa ba wata yarinya bace da zaki biyewa yara ki je ki yi wannan abin ki biyo titi, yanzu ko kunya bakya ji???"

"Yo kunyar uban wa kake so ta ji ? Yau ga jaraba auren wani shegen ke kanta da za'a hannata yafe ta zaga gari? Da yafen nan take na rantse da huwa rahamanu ɗan nan na tabata da yanzu y'ar nan ta yada na biyar ko na shida ta dauki wani cikin dan bana tunanin akoy shahashan da zai iya hakura da y'ar nan,kuma nice nan makaryaciyarka zaka ga yadda zata yi kasuwa, dama abinda ke hijabin nan kennan???" Hajia ta fada, hankali kwonce har tana dafe haba

Gaba daya wata irin kunya ce ta nemi halaka KAUSAR
A tsayen da take sai ta duke tana rufe fuskarta a cinyoyinta ta furta" innalilahi HAJIA, na shiga uku aa fa"

TAUFEEK dake tsaye ya rasa wanene ya dace ya yiwa wa'azin jin tsoron Allah a tsakanin Hajia da ita wannan yarinyar da ta tashi tana rufarta a kamilance ta wani saki jiki kamar ba KAUSAR ba? Kai wannan abu ya bakanta masa rai menene wannan shashancin?

Rai bace ya juya, har ya nufi falon ya dawo ya nunota da yatsa ya ce" kin ga daga falon nan in kafarki ta fita waje sai na saba maki KAUSAR, ba zan kyaleki da mutuncinki ki ringa yawo haka ba, shirme kawai kin iya sakani gaba ki wankeni in na dan yi wani abin kamar wata ta Allah kece ke yawo haka, an ji kunya!"
Ya idasa fada ya yi gaba

Hajia dake rike da haba al'ajabi na neman sakata marmaren yan maye na iya shegen Elhaji karami ta duko ta gyara daurinta ta nuno KAUSAR da yatsa ta ce" ki ji ni da kyau , ni nan nice uwar uban elhaji karami, kin ga kuwa na ga duniya gannin idona, nice zan fada maki mai fisheki, in bamu maki aure ba kwadaki zamu yi mu cinye ne? Kin ga kwaliyarki ba rashin kunya ko rashin kamun kai a ciki, Allah na tuba yo alherin nan ai ba kowa ke samu ba, tashi maza kada su baza su ki shige jama'a babu abinda za'a yi, in banda bakin hali irin na Elhaji karami in aka hannaki kwaliyar kika rasa mijin shi zai ji dadi ne! Ana abu ba tsoron Allah sam? Tashi maza wataya bikin amini kike shagali maki gani ya mutu dan bantan uba !"

To fa, Hajia kin kuwa zo da tsoron Allah anya?😁😁😁😁😁😁 Hajiar shagali

💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

*DA CIWO A ZUCIYATA*

💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

_MALLAKIN_

*SAJIDA NIJAR*

*FREE BOOK NE* 1️⃣3️⃣

LITATAFAN MARUBUCIYAR

Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Neman na kaina
Bani da zabi
Bak'a ce
Kutkale
Makauniya ce
Mage
Duk nisan jifa
Idan ka raina inda kake
Dutse
Alkalamin kadarata
Bani da zabi
Dakika Biyar

Now

*Da CIWO A ZUCIYATA*

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata💃💃💃💃💃

Dawowarsa da hijab din hajia na sallah rike a hannunsa ya saka hajiar yin shiru da bakinta daga hudubar da take yiwa KAUSAR ta zuba ido tana kallonsa

Fuska a daure ya ajiye mata hijab din gefenta, murya cen ciki ya ce" I'm hungry,,,,"

Daga haka ya juya ya koma wajen zamansa fuskar nan tasa zaka rantse wani mugun abu akai masa
Chapter 21 · 0% Book details