← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 116

Sashe 73

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Huci ta sauke tana share hawayen fuskarta ta ce" Innalilahi Wa inna ilaihi raj'une, kar dai idonmu ya rufe mun biyewa Yumnah da son da take yiwa yaron nan mun aura mata marar mutuncin dan kasuwa? Ki duba ki ga kaf dinmu ya kora ba jin nauyina yace zai kawo min y'ata kennan yana iya sakinta ba damuwarsa bace ko?, Kin kuwa ji me iyayensa ke fadi? Wai bari su yi su koma kar ya dawo ya same su ya wulakantasu, wai ya saba, to ya wulakanta su su, Ni wacece da ba zai min ba? Uwa uba y'ata? Innalilahi Wa ina ilaihi raj'une kar dai mun shigo rigimar da ta fi karfinmu, d'an baba da so ne ubansa ya masa aure ko shekara y'ata bata rufa ba a gidansa ba shawara ba komai kuma kakarsa ta zageni tasss? Ba zai yiwu ba, Allah ba zan iya yarda ba, sai an saki yarinyar nan ba za'a hadata kishi da Yumnah ba, ko ni uwarta ba'a min kishiya ba bale ita!"

Ita dai Akilah kanta a kasa, har ta gama kira ya shigo wayarta mahaifinsu bai tsaya sauraronta ba ya bata umarnin kasancewa a gida yanzu yanzu yana jiranta

Da kyar ta yarda suka tafi tare gidan suka bar Yumnar a asibitin, a gaban idonsu Nurse ta shiga da kayan kula da ita da komai , itace mai jinyarta kuma likitocin sai lekowa suke ana fadin matar docter ce ba lafiya, ita ya san za'a kula da Yumnar fiye da du inda zasu kaita, fatanta mahaifinta ya ci karfin wannan fitinar dan babu inda zata kai su sai dana sani

Sosai ya samu hutun shima a asibitin a ranar, barcin da bai samu ba jiya ya samu ya dan rama sannan ya sauka ya koma dakin Yumnah ya dubata sosai da karin ruwan da aka jona mata da abinda aka rubuta za'a ringa mata har ta warware sannan ya yiwa nurse din dake tare da ita salama ya nufi gida

Ko da ya isa gidan part dinsa ya wuce ya shige wanka, Yana gamawa ya je wajen mahaifiyarsa ya zauna suka dan taba fira sannan ya je wajen mahaifinsa, daga nan ya yi tafiyarsa bangarensa ya kwonta dan zai je aiki ne goben da wuri dole

Washe gari karfe takwas da yan mintina

Sauri take yi tamkar zata zura da gudu sakamakon yan mintinan da ta dora a yadda ta saba zuwa asibitin, a cen kasan zuciyarta kuwa fada take yi kamar zata ari baki na irin tsayar da Itan da direban ya yi da irin yadda Mama da kanta ta sakata saka wannan suturar ta jikinta kuma ta rufeta da fadan wai ta saka turare da yawa bayan yanzu matar aure take, ita abinma ya so bata dariya, ama kuma da ta duba tsantsareren kunshin hannayenta sai ta ji wani dadi dan kunshin ba karya ya zanu Allah ma kuwa

Da dan gudu kadan cike da tsoron kar sabon takalmin nata ya kayar da ita ta saka hannunta ta hanna lft din rufewa sannan ta shige da sauri tana dan haki a hankali tana duban mutanen ciki ta furta" Barka da safia"

Docter Aliyu , da sister Bahija ne suka amsa, Sister Bahijar na rike da wata yar akwati baka a hannunta tana duban Khausar sunna dan jiran ta danna wajen da zata sauka dan ya rufe su tafi ta ce" Dubiya kika zo ne? A wani etage zaki sauka ne? Yi ki danna muna tare da Sir muma bangaren dubiyar muka nufa"

A hankali ta ji gabanta na neman yankewa ya yi faduwar da bata taɓa ji ba, sakamakon mutumen dake tsaye ya bada baya ya dan juyo , ashe waya ce yake amsawa , fuskar nan tasa cike da kamilalan saje, bakinsa dan ciwat da shi, idannuwansa dauke da farin tabarau, rigar jikinsa baka ce sidik sai abin wuyansa ruwan kasa mai duhu, ama rigar da wani tsabar sabon salo da rashin jin magana boturanta uku reras a bude suke, da hannunsa daya yana dan alamun balawa yake yi, watau ya fito ya ratso doguwar tafiyar nan bai Bala ba sai a nan, hannun dake rike da wayar kuwa agogo ce shekekiya dai Wali take irin na rashin mutuncin nan Wada ke nuna wanke hannunka ka taba ne ya wani kafeta da duban da ta tabata shima bai zaci ganninta ba da bai dubeta ba dan abin kunyar da aka launa masu su , wai su din nan

Da karfi KHausar ta juya bayan ta zarro ido jikinta na rawa ta saka kafa ta fita daga lft din da gudun balaki ta saki yar wayar salular Tata a nan da rigarta ta Nurse ta karasa bakin matatakalar hawa ta zauna tana haki zuciyarta tamkar zata buga da tashin hankali

A hankali ya lumshe idannuwansa, ya dan girgiza kansa da idannuwansa ya yiwa docter alamun ya rufe su tafi, sannan ba nuna kyankyami ko wani abin ya duba ya dauki wayar nan da rigar daidai abin ya tsaya ya fice gaba sunna biye da shi ya yiwa sister Bahija shiru a lokacin da take tambayarsa ya bata kayan ta rike, dama kayansa ne a hannunta, ama ya yi kamar kurma yake ya bude dakin da Yumnah take ya shige

A bangaren Khausar kuwa hannaye ta saka ta talabe tana jin tsararen kukan dake neman zuwar mata

Innalilahi Wa inna ilaihi raj'une, yanzu itace take tsoron kallon besty? Ita da ta zo da kudirin su hadu ta sanar masa su fa samawa kansu mafita tun wuri? Shin yaya zata fara masa zancen nan ne? Ta tabata shima abin ya wuce tunaninsa, ina ita ina shi? Me zata ce masa ne? Kai bari ta mike ta je ta yi jiransa kofar office dinsa su zanta, ya bata takardarta ta koma ta kaima Aba, wannan magana ta Aba cewar a zauna da wahala Bama zata iya zaunawar ba gaskiya

Tana mikewa ta ji ana fadin".......

☹️☹️☹️☹️🙃🙃🙃🙃🙃🙃🙃

💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

*DA CIWO A ZUCIYATA*

💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

_MALLAKIN_

*SAJIDA NIJAR*

*FREE BOOK NE* 4️⃣5️⃣

*GARABASA, GARABASA, PROMOTION, PROMOTION DIN LITATAFAN MARUBUCIYAR A KAN FARASHI MAI SAUKI 1K, YAN NIJAR KUWA 1000 FRANCS CEFA*

1: Duk karyar kada

2: Yar mahaukaciya

3: Neman na kaina

4: Bani da zabi

5: Bak'a ce

6: Kutkale

7: Makauniya ce

8: Mage

9: Duk nisan jifa

10: Idan ka raina inda kake

11: Dutse

12: Alkalamin kadarata

13: Bani da zabi

14: Dakika Biyar

15:Wata kokowar

16: Aure yakin mata

17: Ni zan ladabi

18: Daga tafia daukar soja

*Dukansu a kan farashi mai sauki, zaka saka dubu guda ne domin promotion ne nake yi, ka tuntubeni kan layina kamar haka +227 93 81 16 18, Sajida Nijar*

Now

*Da CIWO A ZUCIYATA*

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata💃💃💃💃💃

Ta ce" Khausar Muktar? Alhamdulilah, zo maza kama wannan ki hau cen dakunan VIP ki jona mata wannan allurar, yi gagawa zan kai hoton cikin da akai mata ne waje Docter tana jirana, kar sai na je na jona mata ruwan kuma ran sir ya bace"

Magana take yi da dan gagawa da alamun azalzala , sai kuma ta dan dakata tana kallon KHausar din

Da dan mamaki ta ce" Ke wai lafiya? Ina rigarki da takalmin ki na aiki? Ko dubiya kika zo yau?"

Da sauri Khausar ta girgiza kanta tana kama kanta ta ce" Aa aunty kayan na bari a adaidaita sahu shine nake jira a kawo min"

Kai ta dafe, sai kuma da dan sauri ta cire Tata farar rigar tana mika mata ta ce" Saka bani abayar nan ki je ki yi aikin nan Ni inada wata a office dina in an kawo maki taki kya kawo min"

Tana fada ne tana taya Khausar cire abayar jikinta, da sauri Khausar ta dora rigar auntyn tasu ta tare kwanon silbar mai dauke da maganin ta sakarwa auntynsu abayar da ta ɗora saman riga da sket dinta sababi masu masifar kyau wa'inda suka kama jikinta dasss da su

Juyawa ta yi ta koma lft din tana adu'ar Allah ya sa har ta gama ta koma kar su hadu da shi, ta fi ganewa ta tarda shi da kanta

Lft din na tsayawa ta fito a nutse ta nufi VIP na dakunan ma'aikatan asibitin a ranta tana tunanin waye ba lafiya a cikin ma'aikatan asibitin, dan kuwa waje ne da ake saka manyansu ko ahalin manyansu

Tana daf da karasawa dakin ta dubi madubin dake ajiye sai walwali yake
Chapter 73 · 0% Book details