← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 116

Sashe 7

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wayar ta kife a hankali tana lumshe idannuwanta hadi da ambaton sunnan Allah...., Sai kuma ta yi shiru a zuciyarta ta shiga yi masa addu'a, duka kaf aduo'in da ta saba ta yi masa kafin ta mike ta karasa kusa da kilishinta, ta janyo ta zauna tana murmushi ta shiga ci

A bangaren mahaifinsama zama suka yi da bakin nan harda shi suka dan sake zantawa kan abinda ya shafi ci gana na harkar kasuwanci sannan bakin suka yi masu salama mahaifinsa ya masu rakiya shi kuwa ya zauna yana dan shan tea din da aka dafawa abansa

Dawowa MAI KWANONI ya yi yana murmushi ya zauna yana ta amsa wayar abokinsa

Yana gamawa ya maida hankali kan Ɗan nasa ya ce" Elhaji karami yau ina aka wuni ne?, Tun safe rabona da kai"

Yar dariya ya yi yana shafa gaban goshinsa ya ce" Aba ka manta da maganar dilolin gwonjon da suka sauka yau? , Sai dazu na gama daga cen kuma na leka wajen KAUSAR"

Murmushi mahaifin nasa ya yi yana rage amon TV dake watso labarai..........

Da kula ya ce" Masha Allah, an yi zumunci kennan, fatan du sunna lafiya"

Shima da kula sosai da ladabi ya amsa mahaifinsa sai kuma shiru ya dan ratsa

Shi mahaifin nasa tunanin da yake yi shine har yanzu da ace za'a bi ta tasa da ya kawo maganar wannan zumunci na yaronsa da KAUSAR, sai dai zamani ya zo da salo kala daban daban, shi din kansa ya yarda cewa kawance ne kawai dan kuwa an yi abubuwa kala kala da da ace ba kawancen bane da ya gane , sai abin ya nuna kawancen ne kawai

A hankali ya ce" Damgane da maganar YUMNAH, bana so maganar ta wuce bayan sallar nan, mun tsayar da mahaifinta bayan sallah da sati daya kawai a yi, yaya ka gani?"

TAUFEEK ya sake sada kansa kasa sosai...., Yumnah dai na daya daga cikin yan matan da ya tsaya ya karanta har ya ga eh ta cencenci zamowa iyali a wajensa, domin ta fito daga gidan datijai na kwarai haka kuma tana da tarbiya, uwa uba idan ya yi magana ko wace iri ce YUMNAH na yi masa biyaya domin tun daga lokacin da ya kai mata hijabai yace daga yau su yake da bukatar ta saka ta amsa take kuma sakawar......zai iya cewa eh yana iya auren YUMNAH harma ya rayu da ita a matsayin matarsa idan har alkhairi ce ita din a rayuwarsa......, Sai dai ya so ace bayan an gama exam dinsu an jima sosai ne, dan kuwa bayan sallah da sati daya koda an fitar da result din ba zai fi da kwana goma ba, ga ginnin clinik da yake kai, abin kamar zai dan cakule masa ne ko menene

Dan murmushi mahaifinsa ya yi, sada kan yaron nasa ya saka shi jin dadin hakan, TAUFEEK bai taba barin nagartatun halaya ba, shi yasa bashi da darr da yaron nasa, bashi da wani darrr a kan lamarin TAUFEEK

Abansa ya dora da fadin" ka yi magana hakan ya yi ko yaya?"

Dan murmurshi kawai ya yi a hankali ya gyada kansa

Mai KWANONI ya ce" Masha Allah, sai kuma maganar umarar Hajia, ka ga na so ta yi hakuri su tafi da su ISHRAT, ama ta kiya, bafa zata je da kowa ba sai da wanda ta saba zuwa, na dan so kwatanta mata abubuwa kamar zasu maka yawa ama firr Hajia ta ki Maganar dan da na nuna mata kana Dubai idan ka dawo ka gaji sai cewa ta yi to shikenan a bari badi idan ranta ya kai sai ku je"

Baki ya dan tabe yana ayana irin cazar tsohuwar cen da zai yi, ita me yasa ba zata barshi ya dan ji da abubuwan dake gabansa bane? A gidan nan bai isa ya yi barcin safe ba yanzu zata zo ta ringa taba masa wuya tana faman fadin bashi da lafiya ina manemi da barcin safe?, Idan ya ki yi mata abu sai ta hada shi da wace ta isa da shi ta koma gefe abinta, HAJIA sai ya yi maganinta saboda maganar zuwa umurar nan, zata yi bayani ne

Ama sai ya ce da mahaifinsa" Ba komai Aba, in sha Allah zamu tafi harda su Ishart dinma"

Murmushi mahaifinsa ya yi ya ringa saka masa albarka, shi dai idan har TAUFEEK na duniya baya tunanin zai hadu da damuwa ko ta mecece, idan ta shigo kuwa da yardar Allah TAUFEEK zai gushe masa ita ko ta wanene, shi yasa a duniya bayan mahaifiyarsa baya hada soyayar yaron nan da kowa, kuma baya jin akoy abinda zai iya malaka ya masa shamaki da shi a nan gidan duniya, babu shi

Dan hira suka taba sannan ya mike ya karasa bangarenta yana jin gajiya sosai

Dan dage labule ya yi , ai kuwa karaf suka yi ido hudu da ita tana faman auka turaran wuta na jiji a wani makeke kasko dauke da rabshi tari guda

Murmushi ta saki hadi da fan bangalar da dariya tana dan matse ido dan ta ganshi da kyau ta ce" Shigo mana magidanci zo ka sha kanshi, ka san shi turaren jiji bayan kanshi da dadi kuma maganin mayu ne da aljanu"

Harara ya sakar mata yana jin zai kware, dan har ga Allah turaren nata kauri ne yake yi na tashin hankali ama sai faman fadi take wai kanshi, wai wani maganin aljanu, ai itace aljanar ba kowa ba!

Sakin labulen ya yi ya yi tafiyarsa hakan ya sa ta sake zuba idannuwanta tana kallon kofar kafin ta kallo Hamdiya da ta yi kamar ta suma zuciyarta na bugawa tana kallon hanyar da ya yi tafiyarsa yau ko shigowa ya dan zaunan bai yi ba bale har ta kare masa kallo ta ce" Ke Hamatu yaron nan ya tafi hala?"

Hamdiya ta dan sauke ajiyar zuciya ta ce"

💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

*DA CIWO A ZUCIYATA*

💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

_MALLAKIN_

*SAJIDA NIJAR*

*FREE BOOK NE* 5️⃣

LITATAFAN MARUBUCIYAR

Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Neman na kaina
Bani da zabi
Bak'a ce
Kutkale
Makauniya ce
Mage
Duk nisan jifa
Idan ka raina inda kake
Dutse
Alkalamin kadarata
Bani da zabi
Dakika Biyar

Now

*Da CIWO A ZUCIYATA*

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata💃💃💃💃💃

Hamdiya ta hadiye yawu da kyar tana sauke ajiyar zuciya ta ce" Eh HAJIA ya tafi"

Hajia ta shiga kiciniyar tashi tana fadin" Kai, to me yake damunsa? Nifa bana son na ga magidanci a haka, yaro yana tafe ana harararsa kar aje an shiga gaban jikana ina nan zaune, ke Hamata bani lawurjena na bi bayansa, cikin jakata kuma akoy dan damaso hado min da shi da kulin kaka ka yi ka fito na je na turara masa, aniyar kowa ta bi shi in sha Allahu yaron nan sai ya zama shugaban kasa sai dai maki gani ya mutu!"

Mikewar ta yi domin idan har bata yi gagawa ba HAJIA na iya wanka mata mari, a kan lamarin Yayansu bata ji bsta gani, harta mahaifiyarsa na kiyayewa dan kuwa a kan TAUFEEK ko Aba sai ta batawa bale su

Yana kokarin zama a luntsumemiyar kujerar falonsa, wayarsa a kunnensa dan kiran da YUMNAH ke yi idan bai daga ba har ta yi kuka ya santa sarai ya kai dubansa wajen hanyar shigowa dan jin motsi

Abubakar ne ya shiga shigo masa da kayan abinci

Kansa ya dauke daga dubansa a hankali ya ce" Sorry YUMNAH ba zan samu zuwa ba yau na gaji"

Har ga Allah sai da ta ji wani irin hawaye na neman tsinke mata, da wani irin daci a cen kasan zuciyarta na tunanin abu dayan biyu
Chapter 7 · 0% Book details