← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 116

Sashe 85

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bai wani ja dogon Zama ba ya nuna zai tafi, nan Khausar ta mike tana fadin" Ina zuwa Besty"
Ta juya ta haye sama, shi kuma ya kalli TAUFEEK yana masa murmushin shakiyanci dan Khausar ta ce masa besty

Jim kadan ta sauko hannunta rike da wata bakar leda mai sirri, ba komai bane a ciki sai yan kannanun humura masu dadin kanshi da saka nutsuwa ta bada tana fadin sakon madame ne sannan ta koma ta zauna
Har ga Allah bata yi haka dan ta birge TAUFEEK ko dan ta ba matarsa haushi ba, a ranta ta ji ya dace ta yi hakan dan tana da damar hakan, ko a da idan ya zo takan daka su kuli, su miyar Hausa da yajin dadawa ta bada a kaima madame, yanzun kuwa gannin bata da su sai ta bada humura dan ta san itama abu ce da take iya birge wanda ke kasar waje

Sai dai wannan kokari nata ya matukar birge TAUFEEK duda ba yau ta fara ba, matarsa kuwa sai ta ga kamar wace ta yi da gaya dan ta bata mata, ita dai tana zaunenta har ya mike suka tafi Yumnah sai addu'a take yi da fadin a turo mata numbar madame din sa ringa gaisawa idan ta sake waya , shi dai Husaini ya yi godiya sosai kafin ya fice TAUFEEK ya sanar masa yana zuwa dan sai ya kaishi aeroport du kuwa da irin yadda ya ki ama yace sai ya kai shi

Dawowar da ya yi ba ta komai bace sai ta tsokana da son cinma burinsa cikin ruwan sanyi

Zama ya yi a saman kujerar yana fadin" Wai yau me zan ci ne? Wifeyyyyyyy"

Har ga Allah ita ta kalle shi ne ba dan ta saka a ranta da ita yake ba, sai kuma gannin ba ita yake kallo ba ya saka ta zuba masa ido a ranta tana jin to wai wannan kamar an cin mata fuska ko ana daf da raina mata hankali

Yumnah kam wani sanyi ta ji a ranta, cike da rage murya irin karma a ji tan nan, irin maganar nan ta wasu matan idan sunna yiwa miji a gaban kishiya cike da kisisina ta munafurci ta ce" Oh sorry my hero, yau baka ci komai ba? Bari in shiga kicin in sama maka wani abin"

TAUFEEK ya yi dan murmushi har ta mike tana layi dan ba fa karfin jikinta take ji ba ya riko hannunta yana kallonta ya ce" A'a, a haka ba zaki iya girki ba, bari idan na fita in shigo mana da shi, zan raka Husaini"

Yumnah ta dawo ta dane cinyoyinsa ta dora kanta a kirjinsa, nan ne kuma Khausar ta mike dan ta kula ana daf da aikata rashin mutunci a gabanta ta juya da dan sauri bayan ta warci kaskon turaren wutarta ta haye sama tana jin wata tafarfasa da ranta ke yi ta kai ta ajiye kaskon ta kashe wutar sannan ta ringa kai kawo cike da jin wani haushi a ranta kafin ta nemi waje ta zauna tana karkada kafa cike da jin kewar iyayenta yau har kwana na biyu bata ji su ba, bata da waya, ga wayar nan layin baya ciki, kuma babu litatafanta daga ita sai ranta dan ko Alkur'ani babu a dakin nata bata san ba kuma akoy wajen Ajiyesu a falon masu yawan gaske ma kuwa bale ta dauko ta yi karatu, sai kawai ta ringa sake sake har ta ji ranta na tafarfasa yana bacewa sosai kan irin abinda TAUFEEK ke yi mata a gidansa

Kwonciya ta yi tana ta huci har ta dauki lokacin da ita da kanta bata sani ba sai da ta ji bude kofar nata ta mike da sauri dan bata san cewa bata rufe dakin ba ta dago ta zuba masa ido

Yanzun bata da hijab din rigar ce kawai a jikinta, kuma bata da rigar mama sai kafecen pant dinta a kasan rigar wanda tsaf ya bi sawun rigar tunda ba yar a rufe asiri bace mai santsin nan ce kuma link color ya zamto harta zannen yan mulalan Mamanta ana gani tsaf ga wanda ya kalla dan ya gannin

Ledojin dake hannunsa ne suka so kubcewa daga hannun nasa

Da kyar ya iya tarewa ya rike yana dan dafe bango kadan daga makogwaronsa kuwa yana fitar da wani irin huci mai dumin gaske ya sake zuba mata ido

Da kyar ya cira tafiyarsa ya karaso inda take tsaye ta rike kugu tana sakar harare gefe da gefe

Ajiye ledojin ya yi ya dago ya sake zuba mata ido
Dukkan alamu na masifa sun bayyana a tare da ita, wa'inda sam bai so ganninsu a yanzu ba, bai san dalili ba, harma yake daf da manta abinda ya yi mata take fushi

Ledar ya juya ya kalla ya sake juyowa yana kallon yadda kannanun kitsonta suka wani yarfu abin dai ba'a cewa komai ya dan yi gyaran murya dan maza ne ai kar ya bada kansa a tausashe ya ce" taho mu ci abinci Khausar"

Ledar ta bi da kallo zuciyarta na mata wani irin tukuki

A hankali ta maida dubanta kansa, yanzun bata daga murya irin na dazu ba, ama a sanyayen sai ya ji inama Muryar ta daga yadda zasu yi ba dadin
A hankali ainun Khausar ta samu kanta da fadin" Ni acici ko? Taufeek Ni acici ko? Bana ci barci nake ji"
Daga haka ta karasa bakin bed dinta a nutsen da bata san tana da nutsuwa har haka ba ta hau gadon ta juya bayanta ta kwonta tana janyo abin rufa a hankali ta rufa jikinta da shi

Tunda ta bashi baya har ta kwonta din kallonta yake yi yana tunanin me yake faruwa ne? Me ya sameta ne? Ko bata da lafiya ne?

Dayar ledar mai dauke da kwalin wayarta wace yanzun ya ajiyewa Yumnah Tata da abincinta kafin ya mata salama ya shigo nan din ya dauka ya karasa a hankali bakin gadon yana mika hannunsa ya yaye rufar a hankali ya ce" Hey, menene? Waye ya taba ki? Taso in ji waye ya bata maki rai?"

Khausar dake boye hawayen dake neman tarun mata a idannuwanta a hankali ta girgiza kanta tana rike abin rufar ta ce" a'a babu wanda ya bata min TAUFEEK barci ne nake ji Please "

Wani irin tashin hankali yake jin zai damu zuciyarsa, har ya kasa ciro wayar tasa

Khausar ta dan juyo tana kallonsa kasa kasa ta ce" Ka tashi in rufe dakin dare ya yi "

Dakin ya bi da kallo, a hankalin shima ya samu kansa da fadin" Ni kuma fa, in kwana a ina?"

Khausar ta maida idannuwanta ta rufe tana ji kamar tace masa ka je dakin matarkan mana, sai kuma ta kwabi kanta ta ce" Ai dai ba a nan ba zaka kwana ko?"

TAUFEEK ya mike tsaye yana fadin" A ina kike so na kwana?, Bari in dauko computerna kar ki rufe min daki"

Samun kanta ta yi da bin bayansa da kallo kafin ta maida idon nata a hankali ta rufe tana jin ta kasa mikewa ta rufe dakin, ko kuma bata so ta rufe din ne? Kai kamar wace take gudun ta rufe din ya je wancen dakin ya kwanan, haka kawai take jin idan ta yarda aka yi mata haka kamar an wani wulakantata ne ai! Sai kawai ta lumshe idannuwanta tana sauraronsa har ya dawo din ta sake yin shiru tana sauraron dan motsinsa kadan kadan har ta ga ya hayo gadonta, hakan ya sa ta dan dago tana kallonsa sai ta ga sam bai dubeta ba ya dauko filo yana jerawa a tsakaninsu har kusan kafafuwa sannan ya tafi cen karshen gadon ya wani rabe da computarsa ya yi kamar bai san tana kallonsa ba ya shiga aikinsa yana waya hankalinsa a kan wayar gaba daya

A hankali ta kara komawa tsinin gadon ta makure jikinta kwakwaluwarta cike da tunanin to yaushe zai saukar mata a gado?
Tun tana hangen bayansa da jiran gannin ya saukar mata a gadon har barci ya ringa fizgarta gaba daya ya dauketa jikinta ya saki sosai idannuwanta a lumshe ta yi filow da dayan hannunta dayan kuma yana daf da abin rufar ta sake shi da barcin ya dauketa

A hankali ya ajiye computarsa sannan ya juyo ya ringa janye filo din yana sauke su gaba daya daga gadon, dan bai ga amfaninsu ba, sam basu da waje a gadon nan

Yana gamawa ya sauka ya je ya kashe fitila sannan ya hayo saman gadon ya kwonta ya haska yar karamar wayarsa ya zubawa fuskarta ido

Kasa kasa sosai ya ce" Khausar, my dream, my life, ......"
Idannuwansa ya lumshe yana jin nutsuwa na shiga zuciyarsa, a hankali ya matsa bayan ya cire rigar jikinsa ya janyota jikin nasa ya rungumeta ya zamto rabin jikinta a saman kirjinsa ya zagaye sauran jikin nata da hannunsa ya tofa mata adu'ar barci ama shi masa barcin ya ki zuwa da salama kamar yadda ita ta samu
Bukarta yake, so yake yi ya ji lebenta a saman nasa ta yadda zai iya samun nutsatsen barci
Sai dai kashhhh
Ba zai yi mata gagawa ba, ko a haka ya san ya godewa Allah ya samu wani baban abin daga ita bayan dogon jira da cire tsamani

A hankali barcin shima ya dauke shi, har ya ji karancin barcin a lokacin da kiraye kirayen asubahi suka farkar da shi ya zubawa fuskarta ido gannin yanzun itace ta masa riko irin na filo tana barcinta hankali kwonce

A hankali ta fara alamun motsawa saboda kiraye kirayen sallah, shi kuma ya ki sauketa a jikinsa dan yana so ta farka ya ga reaction dinta

Idannuwa ta fara budewa sannu sannu kafin ta laluba hannunta a inda yake ajiye daf da gemunsa
Lalubawa ta sake yi tana mai tabatarwa kanta eh lalle gemu gashi ne dan haka da sauri ta dago idannuwanta suka shiga cikin nasa
Chapter 85 · 0% Book details