← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 116

Sashe 30

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A nan a zaune tun tana saka tana warwara har ta ringa gannin kamar ta yi wauta ne ko menene? Kamar ta yi gagawa ne ko menene? Haka kawai zuciyarta ke son nuna mata ta yi azarbabi ita da ya dace ta bi a hankali ta raba wannan banzan tsakanin sai gashi ta yi magana wata iri bayan ta san yana son a ringa tausasa harshe?
A hankali ta dafe kanta dake sara mata ta shiga zubar da hawaye msu zafi
Shin da wani harshe zata yi kwatance a gane cewar a tsorace take
Da wani yare zata yi kwatance a gane irin zafin da take ji a cen kasan zuciyarta?
Itace ke wahala, ta fi kowa shiga wani hali a kan mijinta a kan maganar kawarsa
Wai kawarsan ce ta kasa yarda cewa kawarsa ce
Shin wani abu take bashi wanda ita bata iya bashi ne?
Du irin kwaliyarta da zumudinta sai suka dakushe, domin babu abinda ya fi daga mata hankali irin ta ga nasa ran a bace koda wani ne ya bata masa bale ita da kanta
Jin kanta zai tsage ya saka ta mike da kyar ta shiga hautawa bata iya koda dauke kayayyakin da suka yi anfani ba, dan so take yi ta je ta same shi ta bashi hakuri

Tana shiga ta tarda shi saman salaya , dan haka sai ta nemi waje ta zauna saman gado tana jira ya gama ta bashi hakuri dan bata tunanin ko zata iya dangana ta iya barci da shi haka ba

Tun tana tunanin zai gama da wuri har barci ya kwasheta

A hankali ya kai dubansa inda take dukunkune ya zuba mata ido, sai kuma ya sauke ajiyar zuciya ya rufe alkur'aninsa ya kai ya ajiye shi a wajen kilacewa sannan ya haura saman gadon yana sake binta da kallo

Ya yi haka ne dan baya so yanzu yanzu ta dauko masa maganar
Ya yi haka ne dan yana so ya saba mata idan ransa a bace su kiyaye abinda ya bata masan kai tsaye, a bari zukata su huce
Dama bashi da niyar tabata a yau, domin ya fi so su saba a hankali kafin ta san shi wanene shima ya san ita wacece

Sai dai baya tunanin in har zuciyarsa zata iya lamunce masa sauraronta da murya irin wannan da kalamai ire iren wadinnan
Bai san inda abin zai kai iya kaisu ba, gwara su kiyaye
A ganninsa idan wani abu ya hadata da Khausar in ba zata iya zumunci da ita ba, to kar ta zageta, dan Khausar a kulun burinta ta faranta mata, ko anguwa suka fita in ta ga abin yan mata sai tace sai an siyawa Yumnah, itace ta koya masa kyautar soyaya ta fada masa a soyaya fa kyauta ake yi ba'a zama ba kyauta dan kyauta itace mai ciyar da soyaya.......

Murmushi ya yi ya rufa mata sabon blnkt sannan ya kwonta gefenta kadan bayan ya kashe fitilar dakin

*ALLAH BAI SAUKAR DA CIWO BA SAI DA YA SAUKAR DA MAGANINSA*

Ni ce dai Fareeda Abdallah, na sake dawo muku da tallen magungunanmu da zuwa yanzu bazan iya ƙayyade yawan waɗanda suka dace da biyan buƙata sanadiyyar amfani da maganinmu ba. Alhamdulillah! Ƴar'uwa ki gwada, wataƙila warakarki na tattare da maganinmu.
Haihuwa ce baki taɓa yi ba ko kuwa jinkiri kike samu sanadiyyar planning ko kuma haka kawai? Muna da ingantaccen maganin rashin haihuwa ga mace da namiji, wanda za ki bada sadakar 2k ga matsalar ko wane ɓangare. In sha Allah za ki dawo da godiyarki bayan amfani da maganinmu.
Sanyi (infection) ne yayi miki yawa yake saka ki ciwon mara, zubar farin ruwa, ƙaiƙayi, ƙuraje, ɗauke ni'ima, har ma ya saka mijinki ya dinga miki gani-gani saboda bakya gamsar da shi? Da naira 3k zamu haɗa miki magungunan da za kisha ke da Oga in dai kika yi amfani da su ku da sanyi har abada in Allah ya yarda.
Muna sayar da ingantaccen haɗin sabaya, wanda zai sa nonuwanki su cicciko, hatta fatar jikinki sai ta murje sanadiyyar shan kunun sabayarmu. 2500 bokiti 1litter.
Muna da maganin wankin nono ga mai ciki da mai shayarwa, wanda indai kikai amfani da shi yaronki zaiyi tubarakallah, ba ruwanki da laulayi. Muna da ingantaccen maganin Daji (Cancer), typhoid, maleria, yaron da yayi nauyin ƙafa, da sauran cututtukan da ban ambata ba.
Muna aika maganinmu ko ina tsakanin Nijar da Nigeria, ga masu buƙatar magani da gaske su tuntuɓeni akan lambar wayata 07039080978, ko 09077591726

Noted: *MAI SON MAGANINMU IDAN BA A KADUNA YAKE BA, SHI ZAI YI KUDIN MOTARSA HAR ZUWA INDA YAKE, BABU INDA BAMA TURAWA IN SHA ALLAH.....SAI KUN ZO*

💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

*DA CIWO A ZUCIYATA*

💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

_MALLAKIN_

*SAJIDA NIJAR*

*FREE BOOK NE* 1️⃣8️⃣

LITATAFAN MARUBUCIYAR

Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Neman na kaina
Bani da zabi
Bak'a ce
Kutkale
Makauniya ce
Mage
Duk nisan jifa
Idan ka raina inda kake
Dutse
Alkalamin kadarata
Bani da zabi
Dakika Biyar

Now

*Da CIWO A ZUCIYATA*

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata💃💃💃💃💃

Koda ta tashi da asubahi bata ganshi a gefenta ba, duda ta ga an rufata sai ta kasa barkata wani abin kirki, a tunaninta baima kwana a cikin gidan ba ya koma inda ya kwana jiya
Wannan tunani ya karra saka mata tunanin lalle sai ta yi da gaske, banda hanya irin ta kirsa da zata ara sai ta jajirce ta fadawa Allah ya raba mijinta da wannan fitinaniyar,
In ba asiri ta masa ba ta yaya za'a yi a kalli mijinta rikaken namiji mai jini a jika a dangantashi da Khausar?, To ita bata iya bin bokaye ba, ama zata yi dukan abinda ya dace dan gannin ta rana wannan alaka mai wuyar fasara, in Khausar ta iya ruwa bata iya laka ba, da izinin ubangiji zata san tana bibiyar mata miji dan kiri kiri sai ya fi karfinta walahi!

Da wannan ta samu ta dira ta yi bayi
Ta yi wanka ta kuma dauro alwallah
Zuciyarta du bakin kirin na tunanin yau kwana har biyu cif tana matsayin matarsa aman komai bai shiga tsakaninsu ba? Ina ba haka take hango tarayarsu ba, ba haka take hango zamantakewarsu ba

Sallah ta yi du rabin hankalinta a waki wajen
Tana gamawa bata tsaya yin adu'ar ba ta yi wajen kayan kwaliyarta da sauri ta shiga kimtsa kanta
Niyartama tana gamawa ta fice ta yi bangaren manyan ta gaishe su ta yiwu yana cen, inda dai ta san ba zata saka kafarta ba bangaren Hajia ne, dan matar ta tsaneta bata san abinda ta yi mata ba

Bayan ta gama kwaliyar ta dauko wata rigarta ta ajiye doguwa ta lesh tana kokarin nemo abinda zata hada mata aka turo kofar aka shigo

Da salama ya shigo yana dan shakar kanshin dakin da ta baza na turaren jikinta da ta fesa, sai kuma ya sajke dubansa a kanta a inda take tsaye da doguwar rigar barci da ta saka dan yin sallah da safen

Idannuwansa ya dauke a kanta bayan ya ga irin kallon da take binsa da shi idannuwanta na neman kawo ruwa

Bakin gadon ya karasa ya zauna a hankali sannan ya sake dubanta a lokacin da ta nufo shi a hankali kamar wata mai jin tsoronsa
Yannayinta ya saka shi sasaura fuskarsa sannan ya miko mata hannu

A sabauce ta karasa jikinsa ta fada cikin fafadan kirjinsa hannayenta na yin rawa rawa, muryarta na rawa ainun ta ce" Fushi kake yi da ni?, Dan Allah ka yi hakuri, ka yi hakuri ba zan kuma ba, idan na bata maka, ama Yayanmu sai ina jin tsoro, kamar dai baka yi murnar kasancewata matarka ba? Du bana gannin murna a fuskarka"

A hankali ya rungumeta bck, idannuwansa a lumshe ya ce" Murna? Yumna ina murna mana, kin san shekaruna nawa ne yanzu? Na fi kowa murnar kasancewarki a rayuwana....."

A hankali ta dago tana kallon fuskarsa , hankalinta na sake karantar mata yannayinsa, alamu na farin ciki na son bayana a fuskarta

A tausashe sosai ya ce" Shin akoy wani abu da Khausar ta maki kika boye min ne?, Idan akoy shi ki fada min ni zan dauki mataki dan ba zan taba amincewa a wulakanta min ke ko a ci zarafinki ba....."

Wani dadi ne ya ringa ratsata, ita? Ashe? Wani irin luuuu ta yi tana kallon fuskarsa, bakinta na nemo laifin da ya dace ace ta fada ama tana ta kai kawo tana tsayuwa a waje daya, laifin da shine kawai take gani kuma shine bata so

A tausashe ya ce" Tell me, an yi wani abin da bannsanu bane? Ta maki wani abin da bai dace ba kika boye min ne?"
Chapter 30 · 0% Book details