← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 116

Sashe 19

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ana gobe auren Mama da makociyarta suka je gidan suka kai gumbar da suka yi da nono da siga a cikin manya kwala shar shar shar da ledar goron HAJIA suka tare a bangaren Hajiar dan kuwa basu je direct wajen Mamansa ba, wajen Hajiar suka sauka makociyar Mama sai mamakin wai dama nan ne gidan su TAUFEEK take yi, domin irin yadda suke ganninsa bajaja a anguwarsu sun zata da kudin ama bai kai haka ba, saima da ta ga abin mamaki kyautar nan da suka zo da ita kamar sun kawo duniya guda, domin HAJIA haka take murna tana farin ciki ta saka yan aiki suka dauka ta ja su Maman suka nufi ciki wajen matan nan wani kallon yacewa makociyar Mama gyara kar ki kifa, ga abin gyare gyare na tarban baki da murnar babar rana, ga yannayin matan kowace da irin nata salo, sai katon falon ya bada kala babu wajen da ba abin kallon talaka ba

A haka suka karasa sama wajen Mama suka wuce Hamdiya da bakuwarta ta sha kunshi da kitso kai kace itace amaryar dan a yau dinma dinkin dake jikinta an watsa da zinari ba kannanun kudo bane dan a yagawa kishiyoyi da bakinsu sai yadda hannu take tana karbar baki ta ko'ina dan sun yi gaya sosai ko dan su caji aljihun Elhaji wanda murnar wannan rana ta saka ya bude bakin aljihu fiye da da mikawa yake yi du abinda aka bukata ba kauron hannu

Sosai Mama ta yi farin cikin gannin sakon nan, nan take ta saka aka ringa sakawa a frij tana fadin an taimaketa ba sai ta yi ba, ta kuwa manta da maganar dan faro faro mai sanyi na baki, haka take yiwa Mama godiya har sai da ta ji kunya ta lulubeta sannan ta rike su Mama aka shiga hada hada har dai dare ya yi kafin ta sake su tana faman maimaicin fadin" Maman KAUSAR dan Allah fa a zo da wuri goben, kuma ki cewa KAUSAR na ga ta zo yau, koda yake TAUFEEK yace dazu ya leka ya kai mata shadarsu ta diner kuma ya ajiyesu wajen kunshi, ni dai kii fada mata saura gobe ta yi zamanta sai ta ga an hantse na ganta a nan"

Mama kam dariya take yi aka saka direba ya dawo da su gida da tarin alkhairi irin na girke girken gidan bikin da ake tata yi ana zubawa baki

Bayan tafiyar su Mama, Maman TAUFEEK na cikin hidindimu kira ya sameta daga wajen mijinta

Tana shiga ta same shi tsaye a falonsa na farko yannayin fuskarsa a hade tamkar wani abin ya bata masa rai

Tun kafin ta zauna ya tareta da yannayi na bacin rai ya ce" Me nake ji haka a wajen yan uwanki ne Umin Boy?, Yaya zaki ki saka su a lamarin hidimar auren nan bayan sunna nan sunna kaf kaf da ransu sunna fatan birgeki? Me yasa komai sai dai ki tare ko dan ke kika haifi Elhaji karami ne?"

Da mamaki ta kafe shi da ido, sai kuma ta sauke dubanta a kan matansa, sun sha kwaliya tamkar zasu je gasar kyau, kowace sai walwali take yi haka kuma fuskarsu a sake ainun da suka yi ifo hudu
A hankali ta ja numfashi muryarta a raunane ta ce" Ka yi hakuri, ba za'a sake ba, in bandama abin iyayen Elhaji karami har sai an saka su abu nasu? Ni a sama nake ina fama da bakin da suka zo daga gida ai gidan baki daya a hannunsu yake, inace harta masu dafa abincin maza da aka dauko kannin hajia ne ko menene?"

Wani irin makuku ya zo ya tokare wuyan Hajiar, har ga Allah ta tsani in ana kwatance a ringa nuna kanninta dan tuwo tuwo ne dan a habaicin da suke mata har nunawa ake yi kamar dan daudu, wani takaici ya kamata su da suka zo dan su saka yau ranar da ta fi kowace rana mahinmanci a duniyarta mijinta ya fatataketa ta yadda har a daura auren ba zata fahimci komai ba dan bacin rai su ga ta tsiya sai gashi dan bakin munafurci irin nata ta wani bashi hakuri tana sinne kai bakar munafuka

Elhaji kuwa sai ya cire kai daga yannayinta ya ce" To a kiyaye, taron nan shine na farko a gidana kuma shine mafi daraja da zan gabatar dan auren yarona ne baba kuma namiji daya kwal, babu wace zan saurarawa idan ta dagan hankali ciki harda ke mahaifiyarsa, ku je ku bani waje dan baki ne da ni kuka kirayeni na zata wani abin ne mai mahimmanci, in sha Allah gobe daurin auren safe zamu yi ina son gama abinda ke gabana na zo na dan huta"

Wannan shine bata lokaci bukata bata biya ba, a haka suka bar wajen nasa baki dayansu kowace ta nufi inda ta fi wayo, Mama kuwa ta ki nuna fushinta ta ci gaba fa hidindimunta sama da kasa domin su dakunnansu suka wuce , hakan ya sa ta rungumi abinta hankali kwonce ta ci gaba da hada hadarta da fatan du wani abu da suke nufi da ita ya kare masu dan ba zata biyewa fitintinnunsu a irin wannan babar ranar ba

A lokacin da su Maman KAUSAR suka dawo gida nan suka baje ana ta raraba abincin ana mikawa makota sunna ta maida kirki da datako na wannan ahali, lalle abin ya ba makociyar Mama mamaki kuma irin yadda ta ringa maganar cewa take yi ai komaima sai a yiwa bayin Allan nan sun san darajar dan Adam........ Su Kausar kam kowace na nata uzurin ama kuma sunna jin firarakin su Maman har dare ya yi sosai ta mike ta shafa sabulun nan na wajen FUSAM ta barshi ya dan huta a fuskarta sannan ta wanke tana shafa fuskar ita da kanta cike da mamakin irin santsin da fatar nata ke yi, wannan dan fari farin na fatarta du ya fita yanzun sai wani sheki da fatar take yi ko bata shafa mai ba bata mata futu futun nan

A nutse ta kwonta a wajenta zuciyarta cike da farin ciki da fatan gannin babar ranar amini, dan uwa, aboki, yaya a wajenta, lalle wannan rana tana daga daga cikin ranakun da take fatan gani a duniya na alkhairi,

Murmushi ta yi tana dafe kitson da kai mata na hannu kora baya kannanu rass tana tunanin wai atach irin na kitson nan suka siyo rauda rauda za'a saka masu a keya, ita kam bata san ko zata iya yarda da wannan bidi'ar ba, sai kuma ta sake sakin murmushi a hankali ta furta" Gobe dai in sha Allah zan raka ka dakinka Besty, ina farin cikin hakan, Allah ya nuna mana ya da matarka ce har aljanna"....

A'isha ta yi murmushi itama tana jin Adu'ar yayar tata, a hankali ta lumshe idannuwanta tana tunanin gobe, watau gobe idan da rai da lafia sai sun kafawa yayarsu tarihin da bata shirya ba, domin sai sun yi mata kwaliyar da bata taba yi a fuskarta ba, har fata take yi safia ta yi a yi ta ga yaya fuskar zata dawo, har aunawa take yi a zuciyarta shin yaya kwaliyar zata amshi yayarsu? Ta tabata wanda baya kwaliya idan ya yi yana yin kyau, to ama ita yayar tasu zata amince ne?.....haka dai kowa da irin zumudin dake zuciyarsa suka yi barcinsu sunna dan tsinkayo firar mahaifinsu dake ta murnar an yi murnar kyautarsu duda ba wani taka kara ta yi ta karya ba..............

Da safe kusan karfe tara Aba ya fice a gidan da nufin wucewa wajen daurin auren direct, Mama kuwa ta gama kimtsawa ama jira take yan matanta su gama hada kayansu su fita tare ita zata je da yan anguwa ne su kuwa zasu wuce wajen kwaliya ne

Karfe tara da minti arba'in da yan kai suka sauka a gidan Usaina da akwatin kayansu madaidaiciya mai dauke da suturun da zasu cenza suka ajiye kayan sunna kallon yadda dakin kwaliyar nata ya kawatu masha Allah kamar ba a kasar hausa ba, har sai da KAUSAR ta ji tana sha'awar malakar dakin kwaliya

Rukaya ce aka fara dandasawa kwaliyar, KAUSAR na kallo tana jin anya zata iya kuwa wannan hoda haka? Ana tsaka da yin kwaliyar ta lalubo wayarta gannin karfe goma ta gota sosai ta shiga gwada neman layin TAUFEEK tana tunanin zuwa yanzu ai ta yiwu har sun dawo gida dan karfe tara ne daurin auren

Kiran farko ba'a daga ba, sai a na biyu ne aka daga

Muryarsa a hankali, cike da kamala ya furta" Asalamu alaiki wa rahamatullah"

Cike da murmushi ta furta" Wa iyaka, Sanar min abin farin ciki Ango....."

A hankali ya yi dan murmushi yana dan tare hularsa da abokinsa amininsa kuma bakonsa ke son ja dan tsokana , ya ce" KAUSAR...."

KAUSAR ta yi dan tsai jin muryar nasa wata iri, a hankali ta ce" Lafiyarka kuwa? Ko kukan angwaye ka yi da aka daura?"

Murmushi ne ya subuce masa jin abinda ta fada, sai kuma muryar abokin nasa na fadin" Bani ita, KAUSAR yaya aka yi kika yi wannan rashin kirkin kika ki zuwa ki rakamu wajen daurin auren bestynki? Bestyn kennan? Gayanan yana ta kuka muna rike shi wai ango ne shi"

Yar dariya ce ta subuce mata tana zarro ido ta ce" Lah, ka zo? Na shiga ukuna yau da tsokana, ai ganinan na fi so in ya dawo na wuni inai masa nasiha sannan da ni za'a rakashi dakinsa danma kar ku cutar min shi"

Kasancewar sun saba dama, idan sun hadu ko a waya ne sai sun yi ta tsokanar junna sunaiwa junna neman rigima mai ban dariya shi yace shine bestyn TAUFEEK, ita tace yaushema ai shima ya sani ya kauce ya bata waje bata son rigima dai da sauransu , hakan ce yanzunma , tana ta murmushi ta ce" Gaskiya ni ka bashi wayar sai nake jinsa kamar a takure, me ka masa ne dan bana nan?"
Chapter 19 · 0% Book details