← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 116

Sashe 22

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kausar ta saka hijab din bayan ta dubi yannayin hajia , a hankali ta zame dan kwalin dake ciki ta cire sannan ta iya mikewa tana jin wani nauyi na kwaliyar a ranta ta sake dakatawa tana dyban HAJIA

Hajia ta hade hannayenta wajen kirjinta kasa kasa ta ce" Je zuba masa abincin sai mu dinke a daka na gama baki shawara, kin san dama shi magidanci tuwonma sai an zuba masa, matarsa dai zata ga iya shege, jibi keya uwa mun aikata sabo irin yadda yake harararmu, je zuba masa sai mu gama maganar "

Ajiyar zuciya ta sake saukewa a hankali ta karasa inda suke zaune, Salisu na magana, Adamu na dariya yana duba abinda yake nuna masa, shi kuwa TAUFEEK din yana zaune ne yana kallon shima abinda suke yiwa dariyar wanda sam shi bai ga wani abin dariya a nan ba, wasu yan mata ne a tiktok ke tikr rawa tamkar zasu karya kaffafuwa sai kace wasu jakai, shine suka ga abin birgewa a nan

Plate ta karo a kicin din HAJIA ta zo cikin nutsuwa ta zauna ta bude abincin ta shiga zubawa a zuciyarta tana ta tunanin abinda ta masa da yake jin haushinta, bata san ta inda zata kamo ba, batama san takamaiman laifinta ba, ta yiwu dan ta fito ba hijab ne, bai san itama fin karfinta su Aisha suka yi ba, da bata fito din a haka ba, lalle tana tausayawa YUMNAH, koda yake ta yiwu kuma in dai mai saukin kai da jin magana ce ba zata wahala a wajen mijin nata mai tsatsauran ra'ayi ba
A hankali ta dago dubanta dan tana ji yadda abokanansa ke fira da raha,ama shi ya wani kyale su sunna ta zuba su kadai bayan gayar nan idan tana tune tasa ce

Da idannuwanta ta bi inda ya zubawa ido, wato hannayenta dake rike da cokali mai dan girma tana zuba abincin, Wa'inda suke dauke da jan kunshi irin na yan mata da aka yi kata itama ta cancana abinta

A hankali ta sake zuba idannuwanta a saman fuskarsa, hakan ya sa suka yi ido hudu da shi

Bata saba dan sun yi ido hudu da TAUFEEK, TAUFEEK din abokinta ta fauke dubanta ba, ko yanzu da suke kallon ido cikin ido sai bata janye nata ba bale shi da take fadin kulun bashi da kunyar kallon idon mutun ya janye
A saman labanta ta iya budawa kadan, kasa kasa sosai ta ce" Me yake damunka ne?, Fushin me kake yi? Wate ya bata maka rai?"

Har ta ajiye maganarta yana kallon yannayin da ta yin, bai bata amsa ba ya janye dubansa a kanta ya maida wajen abokansa dake tataunawa sunna ta sako shi a ciki daga shi har ita

Tana gama zubawa ta so zama, sai dai da ido TAUFEEK ya mata alamun ta tafi, hakan ya saka ta shaka, shaka irin ta jin haushi harma ta gaza hakura ta sauke masa duba mai shige da harara kasa kasa sai dai a kausashe ta ce" Malan in nice baka son gani a taron naka na yi tafiyata mana? Me na maka tunda na zo kake bina da kallo irin na tsana?, In wani ya taba ka ka huce a kansa mana sai mu dake tare da kai kuma a rana baba irin wannan? Karma ka kula nin TAUFEEK sai me?"

Tana gama fada ta yi gaba da tafia irin ta sauro mai bayanar da irin tata baiwar wace ba kowa keda ita ba ama kuma idon kowa na iya ganni

Wani takaicin ya sake shaka har ya saka hannunsa ya talabe habarsa dan takaici da rashin madafa
Abincin sama sama ya iya cinsa dan ya riga ya gama fice masa a rai da abubuwan dake faruwa da shi a yau din

Sai da suka gama suka fice da abokansa wajen da taron ya fi yawa yana ji kamar kansa zai buga dan ciwo, domin hayaniyar tana nema ne ta fi karfin kwakwaluwarsa

Kusan karfe hudu na yama a dole ya mike ya shiga cikin gidansu dan irin hayaniyar dake ta tashi sama sama

Ikon Allah ta tsaya yake kallo a lokacin da ya ga iyalan mai kwanoni sunna raba hali tamkar an aiko su, fada ne ko mema zai kirayi abin? Shi dai ya ga abin tamkar ba na masu hankali ba kuma kunnayensa na nema su sanar masa wace ake son takalowa

Idannuwansa ne suka sauka a kan Maman su KHAUSAR dake tsaye da waren takalmi a hannunta , takalmin da ya san mamalakinsa , watau mahaifiyarsa

Wanzuwarsa a wajen ya saka yawanci kame bakinsu suka yi shiru, domin TAUFEEK bako yake a inda yake so a ganshi bako, sanane shi a hali na dabanci da jagaliya idan halin hakan ya kama, TAUFEEK mutun ne mai hali kala uku a rayuwa, a gaban tsagera shi din baban tsagera ne, a gaban iyayensa yana da ladabi da biyaya da kishinsu, sai mace daya tak dake taka shi ta masa rashin kunya son ranta, ita kuwa baya fatan a wayi gari ta ga kalarsa da yan gari suka sani, ya fi so ya ci gaba da kasancewa mutun mai matukar laushi, sanyi, rashin sannin ciwon kai a gabanta, dan tana da daraja da mahinmancin da baya so idan ta gane waye shi ta tsorata da shi,

Hular dake kansa ya cire a hankali yana sake bin yayar hajia da wani kallo mai kama da daf yake da budar bakinsa ya yi mata barin mahaukaciya komai girmanta da tsufanta kuwa, domin abu daya ne ta taka take fada daga bakinta wanda a duniyar nan baya tunani wuta ko mashi zasu hanna shi farautar mai zaginta, watau mahaifiyarsa, shi fa komai girmanka ka girmama iyayensa to fa zaka more shi fiye da tunaninka, idn kuwa ka yarda, ka kuskure, wata motsarariyar giyarka ta saka ka take masa martabar masu martaba babu abinda zai hanna shi aikata aiki irin na yaren da basu da tarbiya ta hanya watsa hannayens aa fuskarka ya ce da kai UWAKA ko kuwa ya ja baya ya shige ka kowa ya mutu a huta

Da sauri hajia ta kama hannun yar uwarta tana fadin" Wai menene kuka tsaya kunna kallon mutane ba zaku iya raba fada bane jama'a? Dan Allah kowa ya kama gabansa tunda abin hakane, yaya zaku taru kunna kallon abu na faruwa ama kowa ya ja ya hade hannunsa ya nade yana kallo? Wannan ai sam bai dace ba"

Da mamaki yar uwar tata ta kalleta jin furucinta, kasancewarta ita ta izata sosai kan su zo a yita ta kare kuma sai ta ji magana irin haka? Zata yi magana ta ga kula da abinda bata kula da shi ba da farko, watau TAUFEEK tsaye ya jinginu da abin labule idannuwan nan nasa sun kade sun yi jajir tamkar wanda ke shirin hadiye dan mutun yana bin kowa da kallo

Bata iya yin maganar ba sai hannunta da ta warce ta shiga haurawa cike da takaici

Hajiya Fatahiya ta saki yar guda tana sake yafa gyalenta ta ce" Wai rashin kunyar karya, ki ci gaba mana mu gani buge ko zobe zai ci nasara"

Hajia Nawarah da abin mayarwar ama ta yi shiru ta bari zata rama ne, saima kokarin korar mutanen da aka tara na arziki ta shiga yi tana fadin tunda hakane kowa ya watse ai an ci an sha sauran sa yi

A hankali ya dago daga inda ya jinginar ya nufo inda HAJIA Nawarah ke tsaye

Gaban Maman KHAUSAR kuwa sai da ya kwonci kwonci ya fadi, a dan firgice ta zuba masa ido tana tunanin abin yi, domin mahaifiyarsa ne ta sakata zuwa dan kar ta bari ya aikata wani abin a wajen nan in dai ya ji hayaniyar da ake yi

Har ya kusa cin mata da sauri Mama ta yi raf da hannunsa na dama tana cicira ido , muryarta a raunane ta ce" Aya D'an nan ina zaka je ne haka?"

Dakatawar da ya yi, niyarsa ya warci hannunsa da karfin da zai saka wanda ya rike masa watsuwa a kasa, sai dai muryar da ya ji ya saka shi sake ambaton Allah, sannan a hankali ya juyo yana dan kakaro murmushi ya ce" Mama, hajia ce zan cewa kar ta kori kowa, a ci gaba fa biki kawai"

Kai Mama ta gyada da sauri ta ce" To to to, ai ina iya fada mata ka je kawai abinka zan sanar mata in sha Allah "

Hannun nasa da ta rike ya sake kallo, a hankali ya sauke yar ajiyar zuciya sannan ya yi gaba bayan ta sakar masa hannun

Yana tafia Maman ta sake sauke ajiyar zuciya tana ta Adu'a a ranta sannan ta samu ta shiga bada hakurin laifin da bata san waye ta aikata ba

Tsaki Hajia Nawarah ta ja sannan ta haye ta nufi dakinta

Tana shiga ta tarda yayarta sai masifa take yi kamar zata tashi sama

Zama ta yi saman kujera tana kallon yayar tata da ta ce" a kan me zaki hanna ni magana dan wannnan ya shigo? Bakima son bata bikin nan na ga alama, in ba shi ba kina ji kina ganni a ringa tafka maki wulakanci dan ana auren dan so? Ke baki haihu bane ko shegu kika haifa? Da ki bari na fada na ci uwar babar tasa idan ya so na ga abinda ya is aya yi, in shine karshen marar kunyar duniya ya rama mata"
Chapter 22 · 0% Book details