Sashe 50
Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da ya san abinda zai karra balowa da kyaletama ya yi ta tafin ya bita gida suka sasanta, domin a yanzun sai take gannin bakinsa, rai bace ta dakatar da shi tana fadin" Kana nufin, a zuwanka dan yin aikinka ka zo ne dan ka samu munafukan makarantarmu, sai ka taka ta kaina ka shiga jikina Ni balagazar makarantar wace take gaisawa da kowa ta san kowa take zumunci da kowa ta kuma san halin kowa dan ka cima burinka?, Wato Ni wawuyar nan wace ke iya fada maka komai Bama sai ka tambaya ba cikin saukin nan?, Ni wace bata san inda ta nufa ba da nake iya fayyace maka aikinka cikin saukin nan? Shine ka shiga jikina ka saka na sakankance harta iyayena suka sanka suke mutumtaka, ka saka na je gidanku na saki karina harda kwana Ni mai aboki dan uwa a gareni? Kana nufin a cikin aikin naka ne nake budar bakina in sanar maka matsalata a bayane ba a boye ba?, Sirrin da Umana bata sani ba a kaina ka sani, idan ina kuka burina na jika na sanar maka , ashe du rayuwar ture kake da Ni ban sani ba....? TAUFEEK ka ci amanar zumunci, kuma ba zan yafe maka ba!, Na godema Allah da na gani a yanzu ina mai tabbatar maka in sha Allah daga yanzun an gama, ko menene ya wuce, Taufeek zan ci gaba da zuwa in na samu an daukeni zan yi aikina cikin JAJIRCEWA, domin idan baka manta ba na sha fada maka ina karatu cikin JAJIRCEWA ne dan na san iyayena zasu gajiya wata rana, kanaina nice mamansu....., Zan yi aikina kamar kowace ma'aikaciya, ko ba komai a zamana da kai na karu ka taimakeni sosai cikin nuna min ba kai ka yi ba, Allah ya baka ladan haka, ama ka sani *CIWON DAKE ZUCIYATA* ya goge alakata da kai, ba zan yi zumunci da kai ba again, dan ban san yanzun a kan wani mataki za'a yishi da Ni ba, kar aje Ni din ta kaina ake bi ana cimma mutanena...."
Daga haka ta sake mika hannu ta ja mayafinta, wannan karro tun kafin ta ja mayafin ya sauka daga hannunsa , ta janye a hankali ta dora shi a gefen kafadarta sannan ta juya wajen motar nan ta dauki jakarta ta rataya ta kama hanyar tafiya tana share idannuwanta har gabanta na mata ruwa ruwa kamar wace ta sha wani abu
A tsaye yake, yana binta da kallo har ta bacewa ganninsa gaba daya
A hankali ya dan ja numfashi a kirjinsa ya sake rintse idannuwansa ya bude ya kuma bin hanyar da ta bi da kallo
A cen kasan zuciyarsa kokarinsa ya ba kansa tabacin cewa ranta ne ya baci iya bacewa shi yasa har ta yanke wannan hukuncin, ya san yadda zai bi ya bata hakuri ta sauko
Dan murmushi ya yi a hankali yana juyawa dan ba sauka ya yi ba su doctors ya takawa sai ya ganta tsaye , a sanyaye ainun ya dan sake sakin murmushi, yana so lalle sai ya kori wani gefe na zuciyarsa dake fada masa kamar ba wasa take yi ta hanyar tabbatarwa ransa cewa to ai kadan daga aikinta, in dai Khausar ce idan ranta ya baci tsaf take wanke shi abinta, bata ko duban girmansa abinta, uhum abin haushi wai mayafin da ya mata magana kansa karshema a kafada ta yafa Bama rufashi ta yi ba, ai zai ga in zata iya tafiya har gida da shi a gefen kafada
Yana shiga office dinsa ya ciro wayarsa ya zauna a hankali ya shiga kiran numbarta
Kira na farko ya shiga, ama na biyu sai kiran ke dawo masa
Ido ya dan zarro dan hakan na nufin ta saka shi a Black list kennan
A hankali ya ajiye wayar yana furta " Uhum Allah shi kyauta ya shirye ki"
Daga haka ya ci gaba da yan aikace aikacensa, duda hankalin nasa a rabe yanzu, ama haka ya ringa aikin dan dole ne ya gama abinda ke gabansa a yau
Khausar bata isa gida ba sai kusan magariba
Koda ta je ta tarda Mama bata nan ama ta Bara mata ky a makota, dan haka ta amso ta zo gida ta cenza kayanta sannan ta shiga kimtsa gidan ranta a matukar bace
Tana gamawa ta dora masu yar makaroni ta koma ta zauna ita kadai tana cije lebe da kuma tarin jin haushin da ya daskare mata a cen kasan zuciyarta
Yanzu ita? Kennan waye ya dauketa da mahinmanci ne a duniya bayan iyayenta? Bata taba tunanin zata iya riskar wannan gagarumar surprise daga mutun mafi kusanci da duniyarta ba irin TAUFEEK
Ita fa babu wani uzuri da zai gabatar mata ko za'a fada mata ta saurara ko ta gane
A zamantakewarsu ya dace ace ya fi kowa Sannin wacece ita, idan tace wacece ita tana nufin koda aikin sirri yake yi a yadda ya gama karantarta in ba dan yana anfani da ita dan cinma aikin nasa bane da ya sanar mata sirrin dake boye a tsakaninsu
Ita me ta boye masa ne?
Irin yadda take yiwa umarninsa biyayya kuwa tana tunanin su Aba kadai suke gaban furucinsa
Wata kwafa ta yi tana amsa salamar su Salma yarinyar dake bayan layinsu ta mike daga zaunen da take a zuciyarta tana ayana' hijab ko?, Zan saka ama na rantse maka ba dai irin wancen ba, kai ba zan kuma maka biyayya ba, ba Ni ba kai! Zan kiyaye adinina ama bi izinillah nima zan dauki wasu shawarwari da ake bani a matsayina na budurwa kuma musulma dan gyaran kaina ba dan batawa ba na kasance kamar kowa!, Wani sa'in harma da gudun kar kace yace nake bulumtun nan! A yanzu ka jima baka ce ba, koda yake Bama sai na kuma haduwa da kai ba bale har ka iya bani opinion dinka a kan abinda yake nawa! Domin daga yau Ni nice Ni daya ce kuma, du wani bestyma ai cuta ce, kwarai Hajia ta yi gaskiya ashe amincinmu akoy wata a kasa? Watar kuwa ba komai bace face cuta tsagwaronta!, Wasu mutanen dai sun ji kunya'
Tabarma ta shinfida masu, sunna neman zaunawa sai ga Maman ta dawo a gajiya tilis, dama daga gidan rasuwa take kuma na kusa ne sosai tarema suke da Aba,
Jin rasuwar da aka yi ya sakata kin fada masu abinda ta ƙunso take jira ta sanar masu, saima ta shiga hidimarsu ba tare da ta gane cewar salmar nan wajenta ta zo ba har sai da Maman ta kireta daka ta ce" Khausar, yaya zaki bar bakuwarki zaune ita daya ne haka?"
Khausar da mamaki ta ce" Mama bakuwata kuma? Na zata ko aikota aka yi wajenki?"
Maman ma da mamaki ta ce" Wajena kuma? To wa zai aikota Wajena?, Da aikotan ne aka yi ai da ta sanar min ko?, Na ga tare na tardo ku kuma Ni bata nuna Wajena ta zo ba ki je ki dan saurareta mana ?"
Khausar ta fito zuciyarta cike da mamaki, abinda ya sa mamakin ke damunta Salmar nan dai na farko ba sa'arta bace, dan a kadan tana iya bata shekara shida ko fiye, sannan irin rikakun yan ji da kan nan ne na anguwa wa'inda ko gaisuwarka basu cika amsawa ba don mahaifinsu na mai kudin anguwa, a gaskiya a gidansu ana fadin sun cika girman kai, kuma daga mahaifiyarsu suka dauko domin kaf layin nan da bayanshi babu wanda mahaifiyarsu ke hulɗar arziki da shi, ita ta fi karfin ajinsu, mahaifinsu dai da sauki dan shi ko me ake yi a anguwa in dai ya ji ana yi da shi yana zuwa fatiha na sunna ta aure ko zana'iza
Zama ta yi yanzun du a takure ba kamar dazu da take sake ba, dan dazu a tunaninta wajen mahaifiyarta Salma ta zo
Salma kam ko a yanzu da Khausar ta dawo ta zauna tsaf ta kare mata kallo,.kallo irin na son Sannin shin da gaske ƴaƴanta matar nan ta masa ne har da ya nace haka da son samun kusanci irin na zuciya da zuciya da ita ko da akace likita ce ita din yake so ta zamto a cikin ahalinsu?
Dan murmushi ta yi tana mikewa ta saba jakarta a kafadarta ta yan gayu tana kallon KHausar ta ce" Sister, zan juya, ki dan ban numbarki dama fira na kawo maki"
Sosai Khausar ta so cewa Fira kuma? Ta me fa? Sai dai ta kasa fada saima hijab da ta saka a shigarta dakin dan bata cika son kallo irin wannan ba a rayuwa yana damunta ainun
Wayarta ta dauko ba wata damuwa ta ba Salma numbar tata harma ta dan taka mata bakin kofar gida sannan ta dawo da sauri tana ta hade rai dan a dan fitar nan ta san ta sake cirarwa kanta magana, ana iya cewa bata mu'amala da mutane talaka sai masu kudi, shi yasa batama tsaya har Salma ta shiga motarta ba ta dawo da sauri
A wannan daren abincin kirki kasa ci ta yi, danma juwa ta fara nusar da ita menene yinwa, da tana iya kasa cin abincin kwata kwara dan cin amanar da akai mata, wani sashe na zuciyarta kuwa kuka yake yi sosai na decision dinta, sai dai ta ja ta tsaya zata ga waye keda iko cikin ita fa shi!
____________________________________
Karfe bakwai na safe
*TAUFEEK*
Zaune yake saman table yana karyawa kira shigo wayarsa, kira ne mai mahimmanci dan haka ya dan mike ya shiga amsawa, Yumnah kuwa ta bishi da wani irin sansanyan kallo tana jin wani irin nutsatsen kusancin zuci da idannuwa idan tana ta kallonsa
Idannuwanta ta lumshe, tana matukar jin tarin kauna da girman mijinta a zuciyarta
Dawowarsa ya sakata sake zuba masa wani shayin sannan ta koma ta zauna tana kallon yadda yake dan sha yana duban screen din wayarsa dake ajiye a saman table din
Dubanta ta kai itama, sai ta ga kamar call ne yake aikawa
Har zata cire kanta sai ta sake dubawa dan haka kawai ta ji idannuwanta sun sake likuwa a saman screen din wayar