← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 116

Sashe 60

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata💃💃💃💃💃

Aba ya ja numfashi yana jinjina kansa cike da madaukakin mamaki ya ce" A'a Elhaji, ko daya, idanma AKOY din gaskiya Ni dai ban san maganar manya a ciki ba, bayan wannan Khausar ai budurwa take ba bazawara ba, alhakin zaba mata miji a kanmu yake mu iyayenta miji na fari, abinda nake roko daya ne tal a bani dama na je na fadawa Allah sannan na sanarwa mahaifiyarta, ko menene na san zai zo da wurin ama a bani kwana uku na je na kadaice kaina na barawa Allah zabi, na san ai zaka dauki sati biyu zuwa uku kafin ka tafi ko?"

Elhaji ya bashi amsar cewa eh zai dauka, daga karshe suka ajiye maganar nan da kwana ukun Aba zai sanar masa abinda ya tsayar, tsayawar kuwa a kan abu daya ne daidaito kan daurin auren KHAUSAR din, maganar biki zata biyo baya ne da yardar ubangiji da maganar tarewa

Tunda Aba ya shigo gidan fara'ar fuskarsa ta kasa boyuwa , har sai da Mama ta gaza hakuri ta yi tambayar shin me aka samo ne mai girma haka? Duda kasancewarsa mutun mai sakin fuska da fara'a, ama ta yau din baba ce sosai

Bai boye mata komai ba ya sanar mata, sannan ya bata damarta itama ta uwa kan ta sanarwa ubangiji ya yi masu zabi na aalkhairi

Sosai itama ta cika da yannayi na farin ciki da kuma fata mai kyau, ta sani ne idan Allah ya yi an yi abin a yanzu dama shine mijin Khausar din sai yanzu ya bayyana, dan haka itama ta kame bakinta ta shiga sanarwa ubangiji, sai dai abu daya tak da ta gabatar kamar yadda Aba ya sanar mata shine dogon zaman da suka yi bayan sallar asubahi ita da Khausar, zaman ya kunshi magangannu irin wanda Khausar din ta jima da yi, cewa ta jima da bada wuka da nama a hannun mahaifinta kan ya zaba mata mijin aure, tun daga lokacin da ta fara sarewa lamarinta da soyayya ta yi wannan sadakarwa,
Sosai abin ya zo mata wani iri, domin ba'a kuma maganar nan ba tunda ta sanarwa iyayenta cewa ita ko wanene in dai ya kwonta masu a zuciya to ita din mai biyayya ce, daga nan basu kuma tada magana makamanciyar wannan ba, nan da nan ta sakawa ranta cewa eh lalle da gaske Salis yake bai zo da wasa ba kamar yadda ya sanar mata, ya fada mata cewa zai turo mahaifinsa da wuri a tsaida komai dan yana so a yi komai kafin tafiyarsa, a cen kasan zuciyarta babu abinda ya cika mata zuciya sai tarin farin ciki da zumudi da kuma adu'ar Allah ya nuna mata ya kuma tabbatar mata da alkhairin hakan, ta kuma tabatarwa iyayenta cewa tana kan bakanta, koda a rashin sani aka daura mata aure ya dauru dan su suke da ita ba ita take da su ba

Daga nan ta shirya ta wucewarta wajen aiki, zuciyyarta cike da tunani kala kala , abinda ya fi komai tsaye mata a rai shine farin ciki, sai dai ko TAUFEEK ba zata sanarwa ba , sai ta ga abinda yake faruwa ya tabbata kafin kowama ya ji,
Haka ta wuni aiki cike da tunani har yama ta yi ta juya gida a ranar ko haduwama basu yi ba da Taufeek dan bai shigo asibitin ba, sai dai tana ji a cen kasan zuciyarta da wahala yauma ta iya kwontawa ba tare da ta dan sanar masa abinda ke tafe ba, ta rasa ta yaya take iya wannan abin, sam bata san wani abu wai shi sirri tsakaninta da shi ba, ga yan uwanta mata dai, sai ta boye masu abu dubu bata boyewa TAUFEEK ba

_____________________________________

Firar dare suke yi su uku a saman baban filin wajen hutun Aba, watau da Aban, da HAJIA sai TAUFEEK

Kusan firar ta fi yawa tsakanin TAUFEEK da Aba, domin Hajiar zaune ne take sai kada kafa take yi abinda ke bakinta mai yawa ne ama zuwan TAUFEEK ya sa ta kame baki dan yana mata fadan irin hakan, yana hannata kawowa mahaifinsa karar matansa, bayan ita tafe take da magana mai mahimmanci ta abinda bata tunanin zai haifi ɗ'a da ido, domin ita ke gannin take taken iyalinsa a kan sarakuwa daya tak da ta fara shigowa gidan, yarinyar sam bata da wayo, in ba rashin wayo ba ta yaya zaki zo gidan da sarakuwarki a ciki ama tsakaninta da ke in ta sauko ta ganki ku gaisa shikennan, koda yaushe kina nanike jikin kishiyoyinta kina aikata me Kennan? Da ace kin tarar da wata fahimta bayananiya da sai kice ai kansu hade kika tardo su, ba'a hannaki musu biyayya ba ko yin zumunci da su da zama inda suke ba, ama ta yaya zaki fifitasu a kan mahaifiyar mijinki? Dama ita HAJIA kaka ba ta kanta take ba dan kuwa Yumnah ta gaisheta bata gaisheta ba du ita ta gano, ama mahaifiyar taufeek da ta zamto kunnu huce in shaka ba zata yarda a ringa raina mata wayo ba gaskiya, shi yasa take zaune sai sake hade baki take tana turowa cike da gundura da jin firar tasu, kuma ta tabbata da gaya Magidanci ya ki basu waje suke firar kasuwanci shi da ubansa, dan ya san mai kwanoni da son fira da shi yake takalo maganar nema, ai kam yau ko ita ko su an ga wanda zai gaji dan kuwa a harshen zanninta akoy goro daure tun dazun da ta ji alamun za'a raina mata wayo takan ciro ta kantsa sannan ta daure tana binsu da kallo da harara

Wayar Aba karama dake kuka ce HAJIA ta kawo masa, da kyar take tafia domin a dazun anma zata zata haihu ne sai kuma nakudar ta dan lafa, ama yanzu haka cikinta take shi yasa ta tahowarta bangaren mijinta dan ba wani yarda zata yi dayarsu ta ga gazawarta a wajen nakuda ko haihuwa ba bale kishiya ta yadda mata magana

Wayar ya amsa yana mikewa ya dan yi gaba, dan maganar da zai yin yana bukatar ya dan matsa

Jim kadan ya dawo yana dan murmushi gannin Hajia ta sakar masa harara tana dauke kai ta dubi TAUFEEK ta ce" Wai Ni ko meye abin munafurci a waya kuma? Salon a yi gaba a yi da ni, to ahir dinka inma aure zaka yi ba dai uwar Magidanci zaka karawa ba , ah to , ko mema yace a wayar Allah na tuba?"

Taufeek ya hade fuska yana mata duban nan nasa idan tana abinta tana sako ubansa, hakan ya sa ta sake tabe baki ta dauke kai ta ce" Dadin abin mai kwanonn nice nan babarsa ba wancen sanyi karai din ba, ina da damar daukeshi da mari in ta raya min babu mai ce min na marar masa d'a ehe!"

Aba ya saki kawatacen murmushi yana kaiwa zaune ya ce" Allah ya huci zuciyarki HAJIA, dama maganar auren KHAUSAR ne "

A tare da ita da TAUFEEK din suka zuba masa ido, sai dai cikin ikon Allah Aban ya kame bakinsa ya shiga dan duba wayar hannunsa

Kallonta TAUFEEK ya yi a hankali gannin ta yi shiru bayan Aba dai ai d'anta ne kuma ya fara magana ya yi shiru bai gama ba? Ai Bama kyau fara zance a kyale,

HAJIA kuwa da kufula ta karɓe wayar Aba sannan ta nuna shi da wayar ta ce" Kai zaka bani magana a bude a bayyane ko sai na rotsa wayar nan ne Ni?"

Aba ya zuba mata ido, sai kuma ya saki murmushi ya ce" Au, HAJIA dangane da maganar auren KHAUSAR din ?"

HAJIA ta gyada kai ta ce" Eh mana da nawa?"

Aba ya girgiza kansa da sauri ya ce" dama maganar ce mahaifinta ya sanar min cewa nan da yan kwanaki goma haka za'a daura mata aure ta samu miji a anguwarsu"

Kusan a tare bakin HAJIA da TAUFEEK suka yi magana, TAUFEEK da subutar harshe ya ce" Khausar din?"
Chapter 60 · 0% Book details