← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 116

Sashe 77

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

HAJIA ta ce" Da so samu na yi in da ace daga Ni sai ke ne sai mun tube shi mu masa wankan magani , to a wajen nan harda haramunsa , bayan wannan Magidanci da aka masa yanka ai Ni ke goye shi , Ni din ba damuwa bane ama kin ga gaya irin ta bakin ciki to yau ko Ni ko du wani dan iska a wajen nan , a kan Magidanci babu abinda ba zan aikata ba!"
A wajen wadda HAJIA take bakuwa a wajensa mahaifin Yumnah ne, shi kuwa tasa mahaifiyar ta rasu, tunda HAJIA ta fara magangannun nan ya samu kansa da jin wani irin girmanta a zuciyarsa, Walahi sai da ya ji yar kwala ta taru a idannuwansa, a ce kasan zuciyarsa kuwa sai yake ji inama inama ace tasa uwar ce yake kallo a haka,
A sanyyaye ainun ya dubi mai kwanoni dake duban yannayinsa ya saki murmushi a hankali ya ce" Allah ya karra mata lafiya, Allah ya sa ka rabu lafiya da ita, Allah ya sa ta yi dace da kasancewa a aljana gobe kiyama"

Mai Kwanoni ya yi murmushi sosai a hankalin shima ya ce" Amen ya Allah, Allah ya jikan HAJIA Laraba "

Aban Yumnah ya amsa da amen

Basu fara magana ba sai da aka gama turaren nan HAJIA ta dawo ta yi zaune a tsakiya saman kujera ta harde tana fadin" Kai zo daf da Ni"

TAUFEEK ya yi tamkar bai jita ba, sai da Baba ya masa alamun ya je fa, sannan ya mike ya je ya zauna saman kujera kafadar HAJIA kafadarsa, HAJIA ta wani riko hannunsa kasa kasa ta ce" In suka ce a basu takarda in baka basu ba ina iya daga maka nono"

Kasa kasan ya sake harararta ya ce" Tabas ta tabbata sai na maki aure a Saudiya, ki daga mana haihuwata kika yi yo?"

HAJIA ta masa zuru sai kuma ta cika hannun tana cika tana batsewa ta ce" Na ga ubanda zai Hanna a saki wancen laujen, iskancin banza da wofi"

Shi dai ya kyaleta yana sauraron salamar da mahaifinsa ya sake yi kafin ya ce" Elhaji Abdullahi ne ya nemi a yi zaman nan, a sanina na gayyaci HAJIA da mahaifiyar TAUFEEK ne, me yasa taron nan ya taru har haka?"

HAJIA marwa ta dauke kai a ranta tana ayana' sai dai ku yi du abinda za'a yi a wajen nan sai an yi shi da mu!'

HAJIA baba ta ce" Barsu, barsu ai ba komai, su zauna , ina son du wani makiyin ya ringa gannin ci gabansa a gaban idannuwansa, ku sani in har dayarku ce ta hadasa fitina kun yi aikin banza, Magidanci sai ya jera hudu sai dai a yi abinda za'a yi"

Yumnah dake kwonce jikin adarta harara tamkar idannuwanta zasu fita daga jikinta, a ranta kuwa addu'a take yi Allah ya karbi HAJIA KOWAMA ya huta, dan bata tunanin in har HAJIA na kusa zata bari su rayu cikin Salama ita da mijinta

Mahaifin Yumnah ya fitar da iskar bakinsa, a tausashe sosai ya ce" A yi hakuri HAJIA, a yi hakuri, Ni dama na nemi zaman nan ne dan na bada hakuri, domin ban san iya girman abinda mahaifiyar Yaren nan ta aikata ba, sai dai kamar yadda kika sani wani lokacin mata kan yi gaban kansu su manta du wani girma da ALKHAIRI su aikata aiki irin na son zuciya, Aure babu inda zai je, wannan yarinya Allah ya kadarta matar Elhaji ce, babu mai raba auren nan sai in Allah ne ya hukunta, in banda son kai irin nata da ace Tata ce aka aura zata so a maishe mata ita karamar bazawara?....."

"Elhaji, Walahi, Walahi Walahi da a mata irin wannan auren gwara ace ba'a yi ba ka ji na rantse, nawa take ne Yumnar? Gata da yaron ciki, ba'a duba halin da take iya shiga ba shikennan sai ace an mata kishiya ko sanar mata ba'a yi ba?, To Walahi in saki take so a sakar min y'ata cen ya karata da uwar matan!" Mahaifiyar Yumnah ta fada tana fashewa da kuka tana duban mijinta, wanda ya yi mutuwar zaune harda dafe baki

Da mamaki ainun HAJIA ta ce" Ahaf, Allah dai ya sa ba irin yan iska ka auro ba Magidanci!"

Mahaifin Yumnah da mamakinta ya ce" Kennan du irin nasihar da na maki bata shiga kunnenki ba? Du irin rarashi da ban baki da nuna maki cewar hakan ba laifi bane tunda ba haramun aka aikata ba baki ji ba? Na nuna maki cewa ki guji janyowa yarki wulakancin namiji wani auren yake karawar ya kuma zane matar gidan a zauna babu abinda za'a yi baki yarda ba Kennan? Nan na fada maki in me kike takama da shi ke da y'arki ku ringa jin tsoron Allah a mu'amalarku ta yau da kullum baki fahimta ba Kennan?, In me kike takama da shi Akoy wace ta dama ki ta shanye, ke dinma da kike wannan ikirarin an fada maki tsoronki ya hannani karra aure? Bani da halin hakan ke kin san dalili da inada hakan da na karra , shine kike jinginuwa da wannan kina neman yiwa kanki mugun abu? Saki ko? Ba laifi, in sakin take so ya saketa ta tashi mu je, kema ki kwashi naki kayan ki barta a nan tunda nine ubanta ki tafi kema gida ki koyo hankali, Ni zaki mayar mutumen banza? Ni zaki wulakanta dan ina rarashinki? Bari ki ji in har Elhaji nada wata wace yake son karawa na rantse maki da Allah sai na yi gaya na tara jama'a kin dora abincin taron karin aurensa, da ke kika haife shi ai ba zaki ce haka ba, kuma da ke kika haifi KHausar din ba zaki ce a zaba ko ita ko matar gidan ba!, Ki kula in bakinki ya kuma budewa kika furtan shashanci a nan zaki gane shayi ruwa ne!"

Shi yake fada HAJIA na sakin murmushi harda mikewa, su Baba kuwa hakuri suke bashi harda Akilah, su HAJIA nawarah kuwa kawunnansu nema suke su fi karfin gangar jikinsu dan kunya da tsoron wannan lamari

Yana huci ya maida dubansa kan TAUFEEK ya ce" mun fi karfin mu zauna muna tambayarku daya bayan daya zata zauna ko a'a, gakanan gata in ta ce ka saketa na rokeka ka saketan ta zo gidan ta sameni ina jiranta, kuma ina neman alfarma Elhaji dan girman Allah yarinyar da aka aura masa ta tare gobe ko jibi, tunda ai ba wata bazawara bace bale ta kama zama a gidansu, dan Allah ka taimaka ta tare , itama mutun ce idan ya so in ta zo Yumnah ki hadiye zuciya ji mutu!"
Daga nan ya mike yana kade babbar rigarsa ya umarci Akilah da HAJIA su mike su tafi

Du yadda baba ya so dakatar da shi kiyawa ya yi a haka suka tafi suka barsu sai su ya su

Ajiyar zuciya Baba ya sauke yana kallon Yumnah dake duke yanzu a tausashe ya ce" Tashi daga duken nan y'ata ki je kusa da Mamanku tashi kin ji?"

Yumnah ta mike daga duken, maimakun ta je kusa da Mama sai ta je kusa da HAJIA ta zauna jikinta har rawa yake yi

Baba ya sauke numfashi ya ce" Allah ya sanyaya, a yi hakuri dai, in sha Allah ko menene ALKHAIRI ne, ku ku tashi ku je bangaren ku tunda an gama, Allah ya sawaka"

Jiki ba karfi su HAJIA suka tafi, aka bar su Mama da HAJIA baba, da Taufeek da baba da Yumnah

Baba ya mike shima yana fadin" Sai da safe bari in je inada aiyuka a gabana, ka sameni da sasafe in sha Allah in baka takardun gidajen nan"

"Kai d'an nan maganar tarewar fa?" HAJIA ta fada tana kallon Baba,

Baba ya dakata ya dan juyo yana rage tsayinsa kadan ya ce" eh in sha Allah zan yi kiran Malam din abinda yace sai a yi"

Mama kanta wasai take jin ranta, baba na ficewa ta mike tana gyara lafayarta ta dan rage tsayinta ta ce" Sai da safe HAJIA "

HAJIA ta ce" Allah ya tashemu lafiya, ki yi addu'a dai kafin ki KWONTA kuma ki rufe dakin da ky, wannan kiyayar fa ta fara bani tsoro kar a bi dare a kasheki in shiga uku, baiwar Allah dubeta Magidanci solo solo da ita tsaf fa ake iya zane maka uwa dan da wahala in tana da karfi"

Mama kam tafiyarta ta yi tana murmushi

TAUFEEK ya juyo ya zubawa HAJIA ido bayan Yumnah ta mike ta haye da gudu gudu tana sakin kuka hajiar ta wani bankare ta ce" Ji abu ana guduma basa juyawa, wai Magidanci haka kake shaƙar bakin ciki?"

A kausashe ya ce" Ke dai ki ji tsoron Allah, kina waje maimakun ke baba in kika buda baki kika yi magana dan ki kashe wuta ne, a'a, kina buda baki dan ki asasata ne, tsufa kike yi kina masifa, ki tuba kar ki mutu a haka !, Kuma ki yarda ki bi Ni Saudiya ban san yaya zan jijigaki kafin na sake ki a zagaye ba, kuma da kike cewa zaki aura min mace hudu kika kuskura kika karan aure sai dai ki zauna da su , a tsaya ana min auren dole dan an ga bana cewa komai, to Mama kika haifa da mai kwanoni ba Ni ba, dilla tashi ki tafiyarki Ni in je in bata hakuri kin wani rikitata"

HAJIA ta yi zuru tamkar ta summa tana kallonsa ya mike yana harhada mata kayan turarenta
Chapter 77 · 0% Book details