← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 116

Sashe 25

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni ce dai Fareeda Abdallah, na sake dawo muku da tallen magungunanmu da zuwa yanzu bazan iya ƙayyade yawan waɗanda suka dace da biyan buƙata sanadiyyar amfani da maganinmu ba. Alhamdulillah! Ƴar'uwa ki gwada, wataƙila warakarki na tattare da maganinmu.
Haihuwa ce baki taɓa yi ba ko kuwa jinkiri kike samu sanadiyyar planning ko kuma haka kawai? Muna da ingantaccen maganin rashin haihuwa ga mace da namiji, wanda za ki bada sadakar 2k ga matsalar ko wane ɓangare. In sha Allah za ki dawo da godiyarki bayan amfani da maganinmu.
Sanyi (infection) ne yayi miki yawa yake saka ki ciwon mara, zubar farin ruwa, ƙaiƙayi, ƙuraje, ɗauke ni'ima, har ma ya saka mijinki ya dinga miki gani-gani saboda bakya gamsar da shi? Da naira 3k zamu haɗa miki magungunan da za kisha ke da Oga in dai kika yi amfani da su ku da sanyi har abada in Allah ya yarda.
Muna sayar da ingantaccen haɗin sabaya, wanda zai sa nonuwanki su cicciko, hatta fatar jikinki sai ta murje sanadiyyar shan kunun sabayarmu. 2500 bokiti 1litter.
Muna da maganin wankin nono ga mai ciki da mai shayarwa, wanda indai kikai amfani da shi yaronki zaiyi tubarakallah, ba ruwanki da laulayi. Muna da ingantaccen maganin Daji (Cancer), typhoid, maleria, yaron da yayi nauyin ƙafa, da sauran cututtukan da ban ambata ba.
Muna aika maganinmu ko ina tsakanin Nijar da Nigeria, ga masu buƙatar magani da gaske su tuntuɓeni akan lambar wayata 07039080978, ko 09077591726

Noted: *MAI SON MAGANINMU IDAN BA A KADUNA YAKE BA, SHI ZAI YI KUDIN MOTARSA HAR ZUWA INDA YAKE, BABU INDA BAMA TURAWA IN SHA ALLAH.....SAI KUN ZO*
💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

*DA CIWO A ZUCIYATA*

💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

_MALLAKIN_

*SAJIDA NIJAR*

*FREE BOOK NE* 1️⃣5️⃣

LITATAFAN MARUBUCIYAR

Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Neman na kaina
Bani da zabi
Bak'a ce
Kutkale
Makauniya ce
Mage
Duk nisan jifa
Idan ka raina inda kake
Dutse
Alkalamin kadarata
Bani da zabi
Dakika Biyar

Now

*Da CIWO A ZUCIYATA*

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata💃💃💃💃💃

Kanta ta dauke a hankali daga dubansa ta kama marfin motar itama ta fice du jikinta wani sakaka ta nufi soron gidansu kunnayenta basu jiyo mata tashin motarsa ba har ta shige cikin gidan

A hankali ya dan dafe gabn goshinsa cike da tunanin abubuwa da yawa da suka shafi rayuwarsa a yau din nan

Ajiyar zuciya sanyayiya ya sauke sannan ya tayar da motarsa ya nufi gidansu, zuciyarsa cike da tunanin wanka ne ya dace da shi da kuma nutsatsen hutu, ama wani abu a cen kasan zuciyarsa na fada masa cewa eh lalle wanka da hutu mai sunnan hutu ne suka dace da shi, a yau shima Taufeek bayan dogon jira da dogon daukan rayuwa irin ta gwauraye ya zama ango, ya zama magidanci...........tabas wannan rana ya dace ya yi hakuri da duk wani abin da zai iya taba masa zuciya ya fuskanci sabuwar rayuwar dake gabansa

Bai samu isa gidansu da wuri ba, sai da ya yi yan biye biyensa ya samo guzuri irin na cikaken ango sannan ya karasa

A cikin motar ya bar komai ya fice ya nufi bangaren mahaifiyarsa dake cikin zuciyarsa

Mutanen dake falo baba basu fi a irga ba, dan kowa gajiya ta kai shi ya nemi waje ya tsugunar da hakarkarinsa dan samun hutu

Sama ya haura ya karasa kofar dakin mahaifiyarsa

A nutse ya bubuga sannan ya yi salama ya kuma saurara

Jin muryarta tan amsa salamar ya saka shi bude kofar ya shiga yana sake dan dubawa har ya dawo da dubansa kanta yana dubanta

Murmushin ya saki shima, kamar yadda fuskar mahaifiyarsa ta fitar da sansanyan murmushi mai tafe da sakwani kala daban daban

A hankali ya karasa ya zauna daf da ita ya harde kafafuwansa ya ce" Barka da warhaka Umana"

Murmushin ta yi itama tana sake dubansa ta ce" Daga ina kake haka? Ko guduwa ka yi irin na Fulani?"

Yar dariya ya yi yana girgiza kai ya ce" Su Khausar na mayar gida ai"

Itama ta yi dariyar , sannan ta sauke ajiyar zuciya a sanyaye ta zubawa fuskarsa ido
Bata da bakin magana a yau face ta godewa Allahu sarkin samai da kasai, wanda ya halici bawa ya kuma saka masa jarabawa kala daban daban a tsanin rayuwarsa
Ita dai jarabawarta abokanan zamanta ne a kan d'anta, a da zamansu sunna yi ne komai shawara guda, ita bata bin malaman tsubu ko bokaye bale ace a cen ta jiyo abinda ya tsotatata da su, yau da gobe ne d babu abinda ta bari ya saka ta wayi gari ta ringa tsintar abubuwan da suke yi a bayan fage wa'inda suka girgiza tunaninta suka tsotatata har suka saka ta dauki wannan dabi'a ta kadaice kanta ya zamto idan ka ji muryarta a falo mijinsu ya bukaci haka ko d'anta ya bukaci haka, sai ko idan baki ta yi , yawancin lokuta ta fi tarewa bangaren Hajia dan ta fi sakewa , ita din mutun ce mai gudun munafurci, idan ta zauna da kai da zuciya daya ka ringa munafuntarta lokaci daya zaka nemi wace ka sani ka rasa, sam zaka kasa gane kanta, tana iya shafeka a babin bil'adaman da idannuwanta suke da hurumin gani a gabanta, dalilin da yasa tsakaninta da matan baban Taufeek mutunci gaisawa bayan wannan kowa ya rike abinda yake hurumi a gareshi

A sanyaye ainun ta ce" *MAGIDANCI* "

Idannuwansa ya dago daga kunce agogon hannunsa ya dan zunawa fuskarta ido jin ta ambaci sunnan da hajia ke kiransa da shi

A hankali ta ci gaba da fadin " Yanzu na raka Hajia, a yau lakabin da take maka cewa MAGIDANCI ya cika Autana"

Dan tsai ya yi dan alamu da yake gani na tana son yin kuka
Kansa ya cire kasa kasa sosai ya ce" Bafa gidan miji za'a kaini ba fa ake son rikitani ina zaman zamana, Matar babana kuka za'a yi?"

Daria ta saki ta miko hannunta tana dungure kansa ta ce" kai ba zaka barni irin dan kukanma na taba ba?, Haba Baban yara"

Shima yana dariar ya rike hannayenta duka biyu yana dubanta ya ce" Da izinin Allah, in ina raye, kuma ina kusa, kuka sai dai idan ya shamaceni ya samu fuskar mahaifiyata"

"Allah ya yi maka albarka, tabas na yarda cewa daya tak gari ne, kuma mai albarka ake nema ba wai tarawar ba a tara mararsa albarka, Taufeek ina matukar alfahari da kai, ina kuma gannin kokarinka, kaine ASIBITIN KA, kaine KASUWAR MAHAIFINKA, kaine hidima wa al'umarka, ina matukar alfahari da kai, ina fatan Allah ya dafa maka duniya da kiyama........, Ka ga yau burina ya cika, a da idan na dan dubeka sai na ga shekaru fa ja suke, shekarunka tafiya suke yi, ama maganar aure shiru kake ji , ashe kamar yadda Hajia ta fada ne lokaci ne mu naka dama gashi yau Allah ya yi, Allah ya sa iyalinka ta zamto cikon farin cikinka duniya da kiyama" Maman Taufeek ta fada a sanyaye ainun tana mai dan jimke haannunsa dake karra tabatar masa maganar daga zuciyarta take fitowa

A hankali ya sada dubansa, sannan a hankali ya amsa da amen ya Allah, sai kuma ya sake dagowa yana dubanta a lokacin da ta ci gaba da fadin" Taufeek du shekarunka, da iliminka, wajibunmu ne idan muna raye mu ringa tunatar da kai da kuma yi maka nuni a kan abinda ya dace da rayuwarka dan samun rabauta a wajen ubangijinka, ka ga aure baa abin wasa bane, a yanzu wani nauyi mai girman gaske ya rataya a wuyanka, wanda ba wai iya ka ciyar kaa shayar ka tufatar bane kawai, harta maganar baki idan har domin Allah zaka zauna da iyalinka ya dace ka ringa tauna harshe kafin furucinka a gareta, kuma ka kiyayi shiga hakinta ko wani iri, ka yi kokari kaa koyar da ita yadda kake so ta kasance cikin salama ba da wulakanci cin zarafi ba, domin ka ga mace , makarantar da ka sakata a zamanta da kai karatun zatai maka bita har ku koma ga ubangijinku, ina nufin idan ka gyara kanka ka gyarawa, idan kuwa ka bata kanka ka batawa ka ji Taufeek?"

Kai ya gyada, a hankali yana sauke ajiyar zuciya, sosai yake daukan karatun mahaifiyarsa a ko yaushe, ya kasance mai matukar ba hudubarta mahimmanci, bata taba budar bakinta idan sun yi zama irin wannan ta koyar da shi mugun abu ba, shi yasa yake girmama dukkan furuci nata koda kuwa cikin wasa da dariya zata yi masa

"Shin yaushe ne aikin nan da kake yi zai kare?, Shekara nawa kennan bana?"
Ta fada a nutse tana dubansa da kula
Chapter 25 · 0% Book details