← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 116

Sashe 70

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A nutse Baba ya ce" Assalamu alaikum wa rahamatulah, kamar yadda Hajia tace, haka ne, ina son sanar maku ku dukanku abinda ya faru jiya, alhamdulilah daurin auren da muka je da Magidanci aka daura shi , wannan din hukunci ne na Ubangiji, haka Allah ya so, da wannan nake dubanki Yumnah kan maganar, na san me mata ke daukan abokiyar zama, haka kuma ana iya fasarar cewa baki jima a gidanki ba hakan ta faru, ki Kadara cewa Allah ne ya hukunta haka a rayuwarki, dan kin ga Hajia gatanan da mahaifiyar mijinki rana daya na aure su, kowani bawa da irin kadararsa mijinki kansa bai san cewa san daura aurensa da KHAUSAR ba, ita dinma cikin firgicin abin take harda kukan bata so, to gaba daya dai hakuri za'a ba kowa da kuma fatan Allah ya sa KHAUSAR alkhairi ce a garemu baki daya, ban nemawa mijinki auren Khausar dan na ga gazawarki ta kowani fani ba, ban kuma yi haka dan wata mummunar manufa ba, Allah ne ya Kadara ita din matar mijinki ce , ina fatan zaku mana biyayya gaba dayanku ku zauna lafiya"

Hajia ta saki wani murmushin gannin irin zazaro idannuwan su Hajia nawarah da ita din kanta Yumnar, Mama kuwa kanta a kasa dama bata dago ba, dan bata da ta cewa a taron da bayanin

TAUFEEK kallon fuskar mahaifinsa yake yi tamkar ya ga bako a duniyarsa, Hajia ta gyara zamanta ta ce" To hakurinma da kake badawa Ni ban ga laifin da aka yi ba, aure fa aka ce, in ba'a yi ita aka aurota? Kawai dai batun kishiya ne ba dadi ama in ta yi duba da khausara ai dama kishiyarta ce ba yau ba sai ta ba kanta lafiya a zauna lafiya, magidanci kuwa Ni dama ina hango shi a mace hudu ne, dan in ka yi duba da auren nan sunna ce ta ma'aiki, jikana kuwa baya tsoron uban kowa bale ya ki jera hudu ana masa cenji cenjin tukunya yana rayuwa tamkar da Sarki wannan shine more rayuwa, itama Khausarar da take kukan bata son shi zan koma ne, na sameta , babu mai hannani wanka mata mari a kan magidanci!"

TAUFEEK a hankali ya maida idannuwansa ya lumshe , daga zaunen da yake ya gama gane Yaren mahaifinsa da kuma kakarsa, ana nufin cewa auren da aka daurawa Khausar aminiyarsa a jiya da shi ne aka daura shi?

Idannuwan nasa ya so budewa a hankali, sai dai da sauri ya bude su sakamakon faduwar Yumnah saman kansa rana jan numfashinta da dukkan karfinta hannunta a damke da rigarsa tana kallonsa a hankali idannuwanta suke rufewa har ta rufe su ruf still tana jan numfashin nan da kyar tamkar wace zata bar duniya

A rikice du suka mike, Bama kamar su Hajia Nawarah ba sunna Salalami , dama tunda Baba mai kwanoni ya fara bayanin nan suka kasance a kololuwar mamaki sunna binsa da kallo sai zubewar Yumnah ta saka su mikewa sunna neman daukaka abin fiye da misali

Hajia ta rafka salatin itama tana gannin yadda su Hajia suka talafo Yumnah ama ta ki sakin rigar TAUFEEK, haka kuma numfashinta da gaske sama sama yake yi tamkar wace zata summe
Da tarin al'ajabi Hajia ta ce" Wai summa ta yi? La ila ha ilalahu Muhammadu rasululahi sallalahu alaihi Wasallam, summa ta yi daga mata abokiyar zama ko me ?"

A tausashe TAUFEEK ya kalli Hajiar kasa kasa ya ce" Ki daina ihun nan mana ki yi a hankali bakya gannin halin da take ciki?"

Hajia ta yi tsuru tana kallon yada yake magana da wani yannayi na lisilama, sak kamar munafuki, in ba mantawa ta yi ba dazunma da tana bashi abinci ai magana ne ya kasa kuma ya kasa ci da kansa ko? Yaushe ya samu lafiyar talafar wannan tabaryar har yake son mata iya shege?

Baba ne ya budi baki shima hankalin nasa a tashe ya ce"

Alhamdulilah, mun fa dawo, sai fatan Allah ya bamu ikon yin typing lafiya, ya kuma bamu ikon farantawa junna

*DUBUN GAISUWA DA FATAN ALKHAIRI ZUWA GAREKU YAN UWA DA AMINAN ARZIKI, SPCLY SAJIDA PALACE, MEMA ZAN CE? TA INA ZAN FARA? A INA ZAN SAUKE? ADDU'A ITACE TSAKANINA DA KU DA FATAN ALKHAIRI, KUN YI RAWAR GANI NA MAMAKI, KAMAR YADDA KUKA SABA KUN YI MIN ALKHAIRI FIYE DA TUNANINA, ALLAH YA SAKA DA MAFIFICIN ALKHAIRI, ALHAMDULILAH Y'ARKU NA GODIYA, ALLAH YA BIYA, WA'INDA SUKE TAMBAYANA DALILIN SHIRUNA DA YAWA KU YI HAKURI HAIHUWA NA YI SHI YASA, WA'INDA BAN AMSAWA BA KU GAFARCENI , WALAHI MSG DIN DA YAWA SOSAI FA, INA FATAN ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MUKU A DUK INDA KUKE, KUN SHIRYA JIN ME ZAI FARU A RAYUWAR KHAUSARA YAR GIDAN ABA DA AMININTA DA KUMA ABOKIYAR ZAMANTA? ME ZAI FARU TSAKANIN MAMA DA ABOKANAN ZAMANTA? MU KAFTA PEOPLE😌😌😌*

💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

*DA CIWO A ZUCIYATA*

💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

_MALLAKIN_

*SAJIDA NIJAR*

*FREE BOOK NE* 4️⃣3️⃣

*GARABASA, GARABASA, PROMOTION, PROMOTION DIN LITATAFAN MARUBUCIYAR A KAN FARASHI MAI SAUKI 1K, YAN NIJAR KUWA 1000 FRANCS CEFA*

1: Duk karyar kada

2: Yar mahaukaciya

3: Neman na kaina

4: Bani da zabi

5: Bak'a ce

6: Kutkale

7: Makauniya ce

8: Mage

9: Duk nisan jifa

10: Idan ka raina inda kake

11: Dutse

12: Alkalamin kadarata

13: Bani da zabi

14: Dakika Biyar

15:Wata kokowar

16: Aure yakin mata

17: Ni zan ladabi

18: Daga tafia daukar soja

*Dukansu a kan farashi mai sauki, zaka saka dubu guda ne domin promotion ne nake yi, ka tuntubeni kan layina kamar haka +227 93 81 16 18, Sajida Nijar*

Now

*Da CIWO A ZUCIYATA*

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata💃💃💃💃💃

Baba ne ya budi baki shima hankalin nasa a tashe ya ce" Subahanallah, yaya kun ririketa kun gaza dagata, dagata TAUFEEK mu je asibiti dagata mu je"

Mama dake tsaye tana jiran gannin su Hajia in kamata zasu yi su kamatan ama sai wani daukaka abin suke ne, Hajia baba kuwa dama hannayenta biyu a kirjinta banda harara babu abinda take makawa magidanci dan bata taɓa tunanin zai samu karfin tare wannan matar ba shi da ba lafiyar kirki ne da shi ba?
A nutse mama ta dan matso ta ce" Hajia dan gyara in gani"

Hajiar ta dago ta dubi Mama, ta ga Maman sosai fuskarta a hade, abinda bata taɓa gwadawa ba, kai abinda ya shafi magidancin nema Maman tana matukar nuna kara da kauda kai, da dan mamaki ta matsa din ta bata waje

Da kula sosai Maman ta ce" Sai an kaita asibiti ne? Numfashin nata nake gani sama sama Elhaji?"

Shi da kansa ya yi mamakin wannan lamari na mama duda halin da yake ciki na rabuwar tunani da kuma matarsa mai dauke da dan tayin cikinsa dake kwonce saman jikinsa idannuwanta a rufe ruf tana kokowa da numfashinta, da kula ya ce" Yumnah, Yumnah hey......"

Mama ta duka daf da su sosai , da kula ita dinma ta dafa bayan Yumnar a hankali tana dan shafa kanta ta ce" Daughter, Please calm down, kin san halin da kike ciki kar ki janyowa kanki wani ciwo a kan abinda ya riga ya faru, Please calm down...."

Hajia Baba ta sake yin KISKIRIM tana bin kowa da kallo

Baba dake tsaye ya bi Hajia Fatahiya da ido wace ta fita tana dana waya cike da basar da uban kowa, wayar Tata kuwa ba kowa take nema ba sai uwar Yumnah, domin tsabar bin salsala irin na kuturta bin dan aboki har numbar junna ne da su sunna zumunci irin nasu

Baba ya ce" Ka dauketa mu je asibiti ba wata kama ce da ita ba?"

Sai yanzu TAUFEEK ya sauke ajiyar zuciya , shi kokarinsa na gannin ta daina jan numfashinta ne, ama firr abu ya gagara , dan haka ya mike tsaye tsaf da ita a jikinsa tamkar ya dauki yar jaririya ya juya ya nufi hanyar fita da ita dan bin umarnin iyayensa cewar a sadata da asibiti

Hajia ta rafka salati harda talabe haba, tana biye da su ta dan riko hannun baba ta ce" Ka san wa bilahilazi yaron cen dazu sai da na masa dan jagora na fitar da shi daga dakinsa na sauko shi kasa na bashi abinci, dan sak yace da Ni baya gani jinninsa ya hau, ka ga wannan abar ta suma ya dauketa, to ko dai Mayu suka rike shi kuma yanzu suka sake shi da na yi da gaske?"

Baba mai kwanoni ya yi murmushi ya ce" Hajia ai saukin dai ya samu ne kawai, Allah dai ya tsare gaba"

Har kusan babar motarsa suka karasa Mama ta bude bayan motar ta shiga ba tare da ta bada damar wata zata rakata ba ta masa alamar ya sako Yumnar
Chapter 70 · 0% Book details