← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 116

Sashe 87

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajia ta wani saki murmushi tana kallon Alhusain ta ce" ka ji na Allah mai fadin abu domin ALLAH, kai shima fa sunnan an masa auren ne dazu da na kaiwa Khausara tuwon kari ras ta zo ta ansa ta shaki tuwona , haushi yadda ka san in dagawa magidanci nono kowama ya huta, wannan mugun hali da me ya yi kama, a baka y'ar a wanke tasss a gyare tana kanshi tana MUSMUS komai a wadace yana aiki irin wanda basa jin tsoron Allah, ka masa nasiha in kuma bashi da lafiya ne a sanar min in tashi tsaye dan da ka ga magidanci gaba da baya makiya ne da shi, matan uban nan kamar su kashe shi suke ji, kar su harbi lafiyarshi in shiga uku!"
Fada take yi tamkar ta ari baki, Alhusain kunya da dariya kamar su kashe shi kansa a kasa ya dantse lebe, TAUFEEK kuwa ya zuba mata ido yana kallo kamar wata sabon gani sai da ta dasa Aya ta sakar masu ledar turaran jijin tana turo baki hadi da gyara hijabinta

TAUFEEK ya girgiza kai cike da haushi ya ce" idan na kuma gannin kafarki a bangarena tabas sai na san yada na yi da ke, ke kam Hajia sai addu'a kuma, kar na kuma ganninki a wajena dan tsaf kike iya zige min mata , ku ji hijab har kasa kamar wata Malama , kuma da yake cewa turaranki dadi yana nufin kaurinsa idan kika turarawa mutun har ya yi wanki basa fita Ni koma kar ki biyo mu meye kike saka takalmi?"

Alhusain ya zarro ido yana fadin" kai da Maman Baba kake? Lalle baka da kunya, kuma bestyn kake kira matarka a gaban Hajia? Sai ta bi mu ai nasiha zamu yiwa matanka nasiha kuma da manya ta fi , mutumen kawai Hajia ai babu malamin da ya kaita kake wani yi mata rashin kunya"

Hajia ta ce" Gaya masa, gaya masa dan nan, Ni banma san me na masa ba da magaribar nan yace ba zan bi shi ba, wai kar na je bangarensa ai dole na je yaron nan ko dan na ringa masu nasiha, wai Khausarar ce yace matarsa? Nan fa yace min na masa auren dole Ni na manta ban fada mata ba dazun na taho mu je in sanar mata yanzu"

Wani irin cin birki TAUFEEK ya yi ya dawo yana nuna mata falonta ya ce" Koma, koma kin ji? Je ki cikin dakin in je in dawo , koma hajiata kar a shiga tsakanina da ke yan uba su ci galaba a kanmu, Ni fadan nan da muke yi ma gwara ki mana turare ta yiwu ba kalau ba"

Hajia ta yi ram da hannunsa ta ce" Kaima ka fara tunanin ba kalau ba ko? Ku je zan zo da safe in mana turare dan gaskiya bana tunanin ko lafiya ku je, Husaini na gambo Allah ya sa a sauka a jirgi lafiya ka saka hular sanyi saboda mura ka kuma tabatar ka yi addu'a ka ji? A kuma ringa yin jijin nan dan yana maganin iska sosai"

Alhusain a dole ya ringa dariya harda zama yana tsokanar Taufeek

TAUFEEK ya yi murmushi ya yi gaba yana fadin" Maragaici in ka gama ka sameni "

Alhusain ya daga murya yana fadin" ko Hajia bata fada ba Ni zan fada mata auren dole aka maku!"

Murmushi ya yi ya karasa bangarensa, shi kuma Alhusain maimakun ya mike ya bi shi su shiga ƙafarsa ƙafarsa sai ya yi zamansa saman kujera fara wajen shukoki kasancewar akoy hasken fitila ya dannawa matarsa kira wace idan suka fara fira ya tabata ba zasu gama da wuri ba bale ta san zai taso in an jima ta kama tambayarsa me yake so me zata masa da sauransu dan ba zai shiga ƙafarsa kafar aminin nasa ba bai san me zasu tarda ba, ko ba komai gidan mutun mai aure ba'a shiga kai tsaye haka ba

A lokacin da TAUFEEK ya tura falon ya shigo sai da ya dan zubawa falon ido ya lalubo wajen kunna fitila ya kunna

Falon ya karewa kallo sai kuma ya dan gyada kai, lalle an taba matar gidan, watau yau fitilarma Hajia Yumna bata kunna ba bale a yi tunanin tardo kanshi ko wata tarba irin nata ( masha ALLAH, ya zamto ko yayane mace idan mijinki ya zo ya samu wani yannayin da bai saba gani ba ya gane, ama ba a hade masa tunani ba kulun gidansa a hargitse kamar juji baya gane fari bale baki, du iya shegen Yumnah mijinta ya gane yau matarsa a sama take dan takan saka kanshi ta kuma girka koda na cikinta kadai ne)

Haurawa ya yi ya fada dakinsa ya shige bayi direct bayan ya ajiye karamar wayarsa, gaba daya yau bai dauki babar ba, dan kuwa koda yace masu na zai fita aiki ko kasuwa ba ya san sunna iya nemansa, Alhusain kuwa ya san ba zai shigo ba sai ya tabo shi dan haka suke yiwa junna , dabi'arsu ne, hasalima du tsakaninsu bai fi a irga ba suka shiga falon junna, sukan hadewarsu su sha firarsu ne a waje idan sun zo inda iyalansu suke basa sakin kari a yi ta zuba shirme ba kamun kan nan na wasu abokan mijin

A nutse ya yi wanka sosai da sabulun wankansa na ruwa mai sanyin kanshi sannan ya fito da tawul yana jin dakin nasa wani iri dan yau bai samu turaren wuta ba,

Wani yadi ya fitar mai tsari marar hayaniya ya saka a saman kannanun kayansa tamkar wanda zai fita anguwa sannan ya samu turare ya fesa sosai yadda ya saba kafin ya fito a nutse ya fara shiga dakin Yumnah da salama

Bakin gadonta ya sameta rike da kofin kwalba cike da madara da nido sai dan karamin cokali tana sha

Tunda ta amsa salamarsa ta kalle shi sau daya bata kuma kallonsa ba ta maida kanta cikin abinda take sha gabanta na dokawa hankalinta na neman tashi

Dan murmushi ya saki ya karasa bakin gadon ya zauna ya sake dubanta a tausashe ya ce" Ina yini Yumnahna"

Yumnah ta lumshe idannuwanta hawaye ya bale mata, a hankali ta fashe da kuka

Ajiyar zuciya ya sauke a nutse ya janyota jikinsa ya rungumeta yana taping din bayanta kadan kadan, a hankali ya furta" Its ok Yumnah, ya isa haka kin ji?"

Yumnah ta ringa sauke ajiyar zuciya tana jin yadda kirjinta ke dokawa
Ya rab shin yaya zata yi da ranta? Ta yiwu a ga laifinta, tana yiwuwa a ki yi mata uzuri, sai dai ba zata iya ba kowa hakuri a kan abinda take ji ba, ita ta san ba laifi take aikatawa ba, kuma mijinta ya isa ta yi kishinsa

A sanyaye sosai ta furta" yayanmu....., Na kasa hakura, yaya zan yi in iya hakura?"

Sosai ya ji tausayinta ya kama shi, a tausashe ya cirota a jikinsa ya kama hannayenta yana kallonta ya ce " babu abinda zai kusanta ki da samun nutsuwar zuciya irin addu'a, sannan idan har bakya so ku zauna a waje daya kina da ikon zaba domin Musulunci ya zo mana cewa sai idan mace na so a hadata da abokiyar ZAMANTA ake haɗawa ......"

Da dan sauri ta kure lebensa da kallo, lokaci daya take ta tunanin maganarsa, hakan na nufin a fida Khausar daga wannan gidan da wannan banzar kakar rasa take ita a barta daga ita sai Hajia tana hannata rawar gaban hantsi? Ba zai yiwu ba, idanma Khausar ta yi nesa kennan ba ranar rabuwa tsakaninta da mijinta? Ba zai yiwu ba!

A hankali ta girgiza kanta ta ce" Ka barta a nan, kar a kaita ko'ina ta zauna a nan din"

TAUFEEK ya dan zubawa yannayinta ido, sai kuma ya dan lumshe idannuwansa yana rike da hannun nata ya ce" Shikenan, ama ina so ki kwontar da hankalinki ko dan abinda yake tare da ake, idan kin ji hankalinki zai tashi kuwa ki yi ta yin addu'a in sha Allah zaki ji sauki a ranki, Yumnah ban karra aure dan bana son ki ba believe me"

"Yayanmu, ka karra aure ko aka aura maka ita? Ka daina cewa ka karra, ka daina ɗorawa kanka abin nan Please" Yumnah ta fada tana sake duban fuskarsa

TAUFEEK ya zuba mata ido, yannayin na so ya fara damunsa fa, gaba daya kamar wace bata gane yarensa

A nutse ya saki hannunta ya mike ya karasa wajen tufafinta ya dauko mata hijab baba ya karaso ya mika mata
Amsa ta yi ta saka tana jiran karin bayani dan ta san ta yiwu fita zasu yi sai ta ji ya ce" *NI NE NA KARRA AURENA, BA AUREN DOLE KO NA HADI AKA YI MIN BA, MU JE HUSAIN ZAI MAKU SALAMA*"

Tamkar ya caka mata mashi ta ji a kirjinta

A raunane ta bi bayansa da kallo har ya karasa ya bude zai fita ta ji karrar bude kofar dakin da take kyautata zaton na Khausar din ne, dan haka da sauri ta taho ta riko hannunsa cikin nata harda rabun masa a Jikinsa a lokacin da suke bayyana a gaban Khausar wace ta fito hannunta rike da kaskon turaran wutar da ta sakawa dakinta bayan ya kama sosai ta ji tana ra'ayin sakawa a falon sai ta zuba wadatace ta dora hijab saman doguwar rigar yadi mai santsi dake jikinta ta fito dan kaiwa falon idannuwanta suka sauka a kansu

Wani irin abu ta ji ya caki makogwaronta, a hankali ta bi talabar da TAUFEEK ya yiwa Yumnah da kallo kafin ta dauke kanta tana tabe baki wanda tabe bakin tsaf a cikin idannuwansa ta juya bata ce masu ufan ba ta fara yin gaba a nutse ya sauka kasa turaran wutar nan na tashi ta karasa falon ta ajiye ta juya da nufin komawa sama TAUFEEK da ya hanna kansa Binta da kallo ta karfi da yaji cike da basarwa ya ce" Kar ki koma ki tsaya ku gaisa da Husain"
Chapter 87 · 0% Book details