← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 116

Sashe 43

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wannan sabon kadaici ya so ya dameta sosai, dan kuwa har sai da Mama ta yi da gaske sannan ta dan saku, ba dan ta warware ta cire komai a rai ba, sai dan irga yan kwanakin da take tunanin itana tana iya wayar gari da sunnan amarya dan kuwa a irgenta kwana duka duka hudu ya rage alkawarin Mujaheed da ya mata cewar za'a kawo sadakinta

Sai dai shiru, Aba bai yi mata zancen an tuntubeshi kan maganar ba, ko aiki da take zuwa kuzarinta ragage ne, duda an kusa yayeta dan a yanzu ta haura wata biyu cikin na ukunta take, aiki ta koye shi daidai gwargwado, ama kuzari ya ragu a jikinta saboda tunani da neman mafita a cen kasan zuciyarta

Ba sai an fada mata ba, damuwar iyayenta a duniya a yanzun itace
Ba sai sun tsangwameta ko sun hannata zaman lafiya ba, ta kalli fuskarsu su kalli tata du safiya ta Allah a matsayinta da shekarunta sun isa su dami kwakwaluwarta da kwonciyar hankalinta
Wannan dalilin ya sa koda yaushe wayarta a hannunta take, kunnenta kuwa na sauraro dan son jin sauti daga gare shi, sai dai kwana biyu na ragewa watan ya cika sai ta neme shi dif ta rasa, domin kiran da yake mata na sasafe da darenma idan ba zai zo ba sai ta nema ta rasa

Sannu a hankali kwanakin da take irgawa suka shige, nan fa abin ya fara bayana a jikinta domin nan da nan ta fara neman fita a hayacinta, bata fahimtar komai har sai da aka bata kwana biyu a wajen aiki a tunaninsu bata da lafiya ne

Wannan damuwa tata ta saka Mama a damuwa har ta tirketa ta ji dalilin rashin cin abincinta da yawan tunaninta

Jin abinda yake faruwa ya saka Mama ranta ya baci, a gaskiya abin nan ya fara kona mata rai, ita da kanta a irgenta sau uku kennan Mujaheed yana fadin yau gobe, dan haka ta samu Aba da maganar ta sanar masa

Su dukansu basu zaci cewa Fada Aba zai rufesu da shi ba sai da ta fada din, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, cewarsa in har ya yi niya ya shirya to ya fito din in kuwa bai fito ba ba lalle ba dole shi baya neman rabuwa karfi da yaji da yarsa, kuma ya amshi kadararsa ko wace iri ce!, Bacin ran wannan ya saka shi ficewa ya bar masu gidan tunda duku duku ya ki dawowa

Sun wuni cikin tashin hankalin nan wani ya sake samunsu, domin kusan karfe hudu na yama aka yi salama cewar ta yi bako ana mata magana a kofar gida.............

💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

*DA CIWO A ZUCIYATA*

💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

_MALLAKIN_

*SAJIDA NIJAR*

*FREE BOOK NE* 2️⃣5️⃣

LITATAFAN MARUBUCIYAR

Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Neman na kaina
Bani da zabi
Bak'a ce
Kutkale
Makauniya ce
Mage
Duk nisan jifa
Idan ka raina inda kake
Dutse
Alkalamin kadarata
Bani da zabi
Dakika Biyar

Now

*Da CIWO A ZUCIYATA*

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata💃💃💃💃💃

Sunna cikin tashin hankalin wannan su su kadai a gida wani ya same su, domin tana cikin dakinta tana jan carbi wani yaro ya shigo yace ana salama da ita , da ta tambayi waye sai cewa ya yi wani ne wannan dake zuwa koda yaushe wajenta ne

Har ga Allah har gagawa take yi wajen mikewa daga saman salayarta ta cenza hijab da dan sauri ta leka ta sanarwa Mama sannan ta fito duda hasken gari ta fito hankali kwonce ta shiga duduba shi

Ai kam shi din ne, da farar jalabiya a jikinsa yana tsaye hannu daya goye a bayansa daya a cikin aljihunsa yana ta faman kada kai kamar wanda ransa ke bace

Da sasarfa ta gaishe shi bayan ta dan duka, sannan ta mike tsayinta tana kokarin yi masa bismillah kamar yadda suka saba idan ya zo wata mahaukaciyar mota ta nufo ta parker daf da tas har kamar zata gogi tasa

Irin tashin hankalin da ta ga ya shiga sai da cikinta ya so murdawa, a hankali ta mayar da hannunta da ta fitar dan yi masa bismillah zuwa cikin gidansu

Mata biyu ne suka fito, kamar yaya da kanwa haka

Wace ke taunar cingan din ce ta bude cikin motarsa daga gaba ta dauko wayarsa tana ci gaba da tauna cingan din ta danna wayar hannunta ta shiga amsawa kamar haka" Gamu gashi bobo, yanzu fada min yaya zan yi in kashe localisation din"

Daga dayan bangaren akai mata bayanin yadda zata kashe ainahin abinda ya basu damar gane inda ya zo daga fitowarsa daga gida bayan ta saka shi a kason kwana uku kennan

Tana kashewa ta juya wajen motar tasa ta maka wayar da jikin madubin motar, ji kake tartsatsa karar fashewar madubin motar kafin ta karaso inda yake tsaye mundil a gabanta jikinsa sai rawa yake sai wurna wurnatu yake kai kace in ya sha iska ya dauketa yana iya makata da kasa, domin ita dinma a ginne take koda bata kai Khausar din ba to fa ta kusa kaita ne dan ko a yannayinta ba siririyar mace bace

Kare masa kalo take yi tana taunar cingan din nan yana wani kas kas kas sannan ta juyo bangaren Khausar wace ke tsaye, ama kana ganninta ka ga wace ke shirye ta iya aukawa da gudu in ya kama dan kuwa abinda ya dakatar da ita ta yiwu maganar da yake yawan fada mata ne cewa shi din tsayayen namiji ne a gidansa da waje!

"Elhaji Mujaheed kennan, wai tsakaninka da Allah a tunaninka shikenan har ka sha bulus ? Kai yanzu a cikin kwakwaluwarka tunaninka nima irin sauran biyun cen ne da ka hade gida daya kake wulakantawa? Ai ina tunanin tun a lokacin da na ki ka hadeni gida daya da matanka ya dace ka san ni ba irinsu bace, ko nace tunda ka san me ka aura ya dace ka taka a hankali, kai yanzu har wani sankon dan daba ne a haka? Kai har dan jagaliya ne? Shine ka tarda babanmu kasuwa yana cinikin hatsinsa ka tayar masa da hankali a cikin jama'a kana masa ikirarin a min magana aure kace zaka yi ba ruwana a cikin maganar kuma gida daya zaka hadani da matar in ba haka ba daular da ake mora sanadinka tsaf tana iya tashi daga sunnanmu? To kai ai baka san da tsohuwar yar iska kake zaune ba sai yanzu, gidan nan da ka bada baka ga sai da aka baka nono ka sha ka kuka damuki abinda ka damuka ba kafin ka yi kyautarsa? Ai kyautar gida da ka yi tun kafin ka aure ni ne , a duniya muka watse ka bada kyauta dan ka yaba kuma sai da saurayina ya tabatar da sunnan gida sunnana ke sama kafin na yarda da kyauta ta zama tawa, kai yanzu kana tunanin dan kana da yan kudaden nan ka fini mutane ne ko wani haukan ke kada maka cewa kana iya kwace gida? Da nake ce maka daga ni ka rufe ka dauki maganar a tatsuniya kennan shine ka nufo wannan zaka kawo min mu jera??????" Ta fadi wannan din tana nuno Khausar wace idannuwanta suka yi waje tsabar tsoro da firgicin abinda yake faruwa, haka kuma kafin kace meye wannan an fara tsalakowa kallonsu, kuma an rasa mai cewa ufan domin fadan kamar mai digi ne da dadin kallo a lokacin har sai da matar nan ta nufota a tsayen da take bata ankara ba ta kama hijabinta ta aniya neman kwashe shi daga jikinta

Nan fa hankalinta ya idasa tashi, jikinta haka yake rawa tana rikewa matar na ja

Da karfi makociyarsu ta karaso ta aniya shiga tsakani haka yayar matar itama ta shiga
Karshe dai da kyar makota uku suka hanna wannan lamari da tuni ya rikita hankalin Khausar ya kuma so ya zauta tunaninta,
Tunda take, tunda ta malaki hankalin kanta a anguwar nan bata fito ba fan kwali ba, sai gashi a yai za'a cire mata hijabinta daya da ya fi sutura a jikinta domin a kasan ba wani abin a zo a gani bane dan kuwa zani ne kawai saman yar ficiciyar riga ta shan iska

"Au, fadan area zaku mayar da shi ko ku din danginta ne?" Matar ta fada da tarin rashin kunya tana harar makociyar Mama
Chapter 43 · 0% Book details