← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 116

Sashe 17

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana kallon yayarta ta ce" Aunty ba fa dan kasuwa kawai bane ba fa likita ne, kuma kin ga wata mata ce mai sunna KAUSAR wai take kawarsa ko me?, Aunty ya fi a irga zai amsa bukatun KAUSAR ni ya kawo nawa a matsayin na biyu, in karkare maki harta iyayensa sun santa kuma sunna zumunci da ita, bama kakarsa du masifar matar nan tana son KAUSAR din nan dan ni ganau ce ba jiyau ba , Aunty abin damuna yake yi fiye da tunaninki, ni da ace budurwarsa ce na rantse maki da na san yadda na yi da ita dan kuwa na fi karfin jagaliyancin ƴaƴan garin nan, damuwata kawai ita ba maganar soyayya tsakaninsu dan ai abin bama wani tsari in kin ganta ta yi hudunmu fa ni da ke, sa'arsa, kawai abinda yake damuna haushi take bani irin yadda mijin da zan aura yake bata lokaci fiyema da ni kaina, Aunty harfa kaya ake mana iri daya fa, ko kishiyata ce ai sai haka!"

Kwarai, auntynta ta ji wani iri a bayanin kanwar tata, sai dai ko menene zata fi so a bishi a hankali, dan haka da kula ta ce" YUMNAH, mijinki yana sonki?"

YUMNAH cike da bada tabaci ta ce" Kwarai kuwa yana so na"

Auntynta ta ce" Shin a dan tsanin nan akoy wani abu da ya tauyeki da shi irin wanda aka saba tsakanin budurwa da saurayin da aka saka masu rana saboda ita? Ko kuwa akoy lokacin da kika fahimci ya so maki wata kyauta ta hanna?, Ina son sani ne dan na gane wani abin"

YUMNAH ta yi gagawar girgiza kai ta ce" Aunty maganar kyauta ai ba za'a nunawa TAUFEEK ba, yana min harda ta mamaki dan kin ga allert din gyaran da ya sako min yanzu haka dan wai baya so na ringa zuwa wajen gyara, kuma gaskiya ban dai tsaya na gane ba a kanta dan ina iya cewa wani lokacin yakan kawon abu yace KAUSAR ce tace zai min kyau suka siyo min dai da sauransu...."

Auntynta ta yi tsai tana hangen mamansu dake tsaye tana kallonsu ta baya ta harde hannayenta

Dan murmushi ta yi ta ce" To shikenan, abinda nake so da ke Auta ki kula, kin ga a furucinki kan iyayensa kina sakin harshenki ya fadi abinda kika ga dama, ki kula Auta ki girmam masa dangi koda autar gidansu ne a haka shima zai girmama naki dangin, sai kuma maganar Kausar , ina so ki fadawa Allah, idan kin tashi fada ki barawa Allah zabi, ki sanarwa Allah in har damuwa ce a rayuwar aurenku ita din Allah ya maku tsari da ita, in kuwa alkhairi ce Allah ya haska zuciyarki a kanta ku yi mu'amala ta alkhairi, kin ga mijinki namiji ne tsayaye da yake da mutane a karkashinsa tun yanzu, baki fa isa ki hanna shi ire iren mu'amalar nan, bama kamar yanzu da zamani ya zo haka, wasun matan abokanan lalacewarsu nema, ba tsoron Allah ba tsoron ciwo ko kunyar ya'ya, kuma gasu ana zaune da su kalau har sun isa da gidansu, ki kula ki bi komai a hankali, yanzu ne zaki fara, kar ki yarda ki fara da garaje da shirme Auta, inama abin kukan da daga muryar da tayar da hankali a nan?, Kefa macece cikin salama sai ki yakicetaba ransa ta hanya mai kyau ba ta hanyar muzguna mata ba in har kin kula cewa alakarsu fa bayan zumuncin da wani abu a kasa, kin ga namiji kowa da halinsa, abinda suka yi taraya a kai daya ne lamarin mata, Auta in har kin yarda cewa ba ta wani waje kika gaza ba yannayi ne haka Allah ya halicesu sai ki ba kanki lafiya ki rayu lafiya a gidanki da walwalarki, in kuwa har baki yarda da haka ba ina tabatar maki wahala zaki sh........."

"Ke, Auta bani wayarki " mahaifiyarsu da takaicin y'arta baba ya gama kamata ta karaso tana katse maganar da take yiwa kallon shirme ta amshi wayar y'ar tata ta duba adadin kudin da aka saka din na gyaran sannan ta mika mata ta ce" Tashi maza ki je dakinki ki yi wanka ki sha magani ki kwonta dan na san wannan kukan sai ya hadasa maki ciwon kai"

Mikewa ta yi tana daukan hijabinta dake ajiye gefe ta juya ta shiga haurawa, dan har ga Allah itama maganar yayar tata ba wani birgeta take yi ba, maimakun ta tayata samo mafitar da za'a iya raba TAUFEEK da wannan karfen kafar sai ta wani shiga magangannu wasu iri, ai walahi bama zai yiwu ba, du yar shegiyar da zata duban mata miji sai inda karfinta ya kare, ba maganar boka ko malan magana ce ta kai da kai!

Zama mamansu ta yi tana dauke kai hadi da hade fuska a lokacin da Fauziya murya a tausashe ta ce" Haba Mama, haba Mama, yanzu haka zaki nunawa YUMNAH bayan kin san maganar da nake fada mata gaskiyar kennan?"

Rai bace mahaifiyarsu ta ce" Kim ga Fauziya dazu kika iso, bana son damuwa please, ba kuma na son mu fara raba hali, ke sai ki mance ni na haifeki ki ce zaki sakani a hanya , ki je kawai ki huta ki yiwa Mubaraka wanka na yiwa su Mahfuz, maganar nan kar ki saka kanki a ciki, ki barmin kawai na san yadda zan bilowa lamarin lokaci nake jira dan ba zai yiwu ba, mu da muke garin mu muka san wannan mu'amalar kuma muka hango ilarta, ko ciki daya suka fito gaskiya ba zamu iya yarda da kusancin nan ba tsar zamu raba bale wai kawa kawancen namiji da mace, irinsu ne ke hanna maka zaman auren kana ji kana gani , domin ko me mijinka zai kareka da shi sai sun amince"

Ajiyar zuciya ta sauke, ba dan komai ba sai dan gannin maganar da alamu baba ce, kuma ba za'a barta ta shiga ba dan ra'ayi na iya bambanta, sai dai ta so su bata dama ta yi hanni irin na addinin musulunci ta kuma yi tuni da abinda aka sani, dan a ganninta yau macen da ta san ciwon kanta take kuma neman lahirarta zata yi domin Allah da kuma gyaran kanta, bayan wannan yaushe zaka saka damuwa a kan wanda aka halartawa irin hakan? Yau koda su biyu zai aura rana daya tanada abin fada ne? Wannan din kamar wata hanya ce da ta dauko wace ba zata bileta ko'ina ba, domin in har ta saka damuwar nan a ranta tabas ba zata rayu yadda take so ba, hakan na iya zama wata tawaya koma dalilin da zai ringa hadasa mata fitina da mijinta, bayan cewa namiji a waje da kuke saurayi da budurwa ne kake da damar ya tsaya ka tsaya in ta yiwu fine in ta bace kowa ya kama gabansa, daga bakin da ka zama malakinsa matarsa zaman zai cenza salo ne daga ka isa da shi zuwa ya isa da kai, watau rayuwa yar shawara yar samun matsaya mai kyau tare da yi masa biyaya, kai inma abinda ya shafi mata ne bama duka maza suke baka fuskar ka kawo masu maganar ba, tsaf za'a nuna maka ba huruminka bane kuma ka hakura kuwa ka zauna, domin wannan din ba cikakiyar hujar da zaka zo gidanku bane a kasarmu ta hausa

Mikewa ta yi bayan ta yi fatan Allah ya sanyaya ta yi gaba kamar yadda Mamanta ta umarta

Mahaifiyarsu kuwa ta dan girgiza kai cike da takaicin Y'ar tata ta fari, ita har mamaki take idan Fauziya na wani abin, kamar ba nononta ta sha ba , salo salo irin na ubanta, to ta je cen ta yi kanta ake ji ita dake zumunci kamar a hada kai da kishiya ita ta gano, na zata sakawa autarta sakaran ra'ayi tana zaune kalau ba

A gidan su KAUSAR kuwa a lokacin da ta koma ta samu mahaifiyarta rike da kudin nan a zaune ta balbaleta da fadan a kan me zata bari ya bata makudan kudi har haka? To kuwa za'a mayar dan ba zata ja mata rigima da babansu ba, da kyar Maman nata ta yarda cewa bata san ya ajiye ba da bata yarda ba, haka suka yi jigum jigum har abansu ya dawo ya tarar da abinda ya faru, nan ya sake yin nasa fadan shima yace aaba za'a karba ba dan haka ta sanar masa idan ya dawo a bashi, baya cikin amsar kyautar mazan zamani ba'a san me gobe zata yi ba in Allah bai yi su din ne mazan ya'yan ba a zo ana rikicin kudin da bashi da su bashi da inda zai hako su, dama shi haka ya hori ya'yansa, bai cika son irin kaye kayen kyautar samarin nan ba, in ba an san da maganarka har ta yi karfi ba a fara amsar irin abu dan jefi jefi kyauta irin ta sallah da sauransu ba, to kuwa koda sun amsa ba da sanninsa ko na mamansu bane, Mahaifin nata ne ya ajiye da kansa da nufin in ya dawo a mayar masa da abinsa

Washe gari kusan karfe goma da zai fita ya fitar da kudi masu yawa har kusan dubu talatin a cikin ajiyarsa ya ba mahaifiyarsu cewa ta ba KAUSAR ta samu wani abin da ta ga ya dace ta yiwa TAUFEEK kyauta na tayashi murnar aurensa, duda kadan ne ta kamanta , sannan suma zasu yiwa iyayensa daga bangarensu
Chapter 17 · 0% Book details