← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 116

Sashe 12

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

KAUSAR ta zarro ido sai kuma ta dauke kanta tana murmushi ta nuna masa atampar dake hannun hajia ta ce" Ankon muka ciro ka manta ne na fada maka jiya cewa yau zamu je kasuwar? Biyu na raba na hannun nan na wajen Hajiya naka ne ka gwadawa abokananka ni kuwa jibi in sha Allah zan fara gwadawa sauran freinds"

Ankon ya dan kalla sai kuma ya yi diffg bai ce masu komai ba, Hajia kuwa har yi take kamar zata bude masu baki ta kalli wannan ta kalli wancen, cen dai ajinta ya tsimkota ta ce" Ni ko a kauye, zamanin da nake ta balarabe, kafin kawata ta kwacen shi karya ne ace a kawancenmu ni in ringa yiwa kawa surutu ta kyale ni, wannan ƙawance naku lalle akoy alamar tambaya, ace kina surutu ya wani kyale ki? In nice in na kumaa kulaka in zama tsintsiyar sharar kurma!"

Aisha ta mike tsagal tana tatara komatsansu tana fan murmushi ta ce" To bara na tare mana taxi Aunty ""

KAUSAR kam dariyarta take ci, ita fa walahi lamarin hajia baya wani damunta, baya taba bata mata rai, kuma tsufan HAJIA tsufa ne mai kyau, domin koda yaushe tana rike da carbinta tana ja, wannan zamanin da ya zama abin tashin hankali wani tsufan dake zuwa a gigice? Rikicinta kuwa tafe yake da rashin munafurci da bata iya ba, wasu bama tsofin bane a gaban idannuwanka zasu nuna maka so a bayan idannuwanka kuwa tamkar su soka maka wuka su daina ganninka a cikin duniyar kwata kwata

Fitowar da ya sake yi da ky a hannunsa ya ce" Tashi mu je" ya saka HAJIA sakin murmushi tana kallonsa ta ce" Ba dai rai na bata maka ba ko? Ai ka ga ciwon kai kake yau kuma kace tare zamu sha ruwan ko? KAUSAR tayani gani kamar ya kumbura fuska?"

KAUSAR ta girgiza kai tana murmushi ta ce" Hajia yama yarda ya maki fushi haba dai, bai yi fushi ba ko besty?"

Gannin ba dai zata tashin ba ya saka shi yin gaba , hakan ya sa ta mike da sauri, hajiarma ta mike tana fadin" Bara in dubo maki yar tsaraba Y'ar nan, yadda kika san me bana iya na ganki ban dan miko maki wani abin na tsaya tsaya ai na zai tafi ya barki ba"

KAUSAR na faman Hajia dan Allah ki barshi na gode Allah ya saka da alkhairi ama sai da ta fito da bak'ar leda tana murmushi ta ce" ke kuwa, sakon Babanki ne duda yau bai aikon da goron ba, ki ce ina gaishe su kin ji? Allah ya maki albarka"

Amsa ta yi bayan ta rage tsayinta sannan ta ringa godiyar itama ta fice ta fito tana ta waige dan gannin inda zata ganshi

Da sauri ta karasa wajen motar yar sumulmula fara dake parker ta bude gabam ta shiga ta rufo tana fadin" Ka ga fa da bari ka yi muka shiga taxi kai dake ciwon kai?, Wai ciwon kan menene haka?"

Hanci ya dan ja kadan yana tashin motar ya fara tafia da su a hankali ya ce" inaga rashin isashen barci ne, shi yasa yau ban fita ba na huta"

Kai ta gyada ta ce" Banama kana jan tafsir ne?"

Kai ya gyada kawai bai bata dogon amsa a wannan tambayar ba, sai kuma ya ce" A wani shago kika fitar da ankon nan?"

Dan murmushi ta yi ta ce" a shagon Elhaji Habu ne, ana mutumen nan bashi da kirki kawai sharin mutane ne, mu dai ya mana mutunci sosai"

Baki kawai ya tabe har suka karasa gidan bai kuma cewa komai ba sai tatausan karatun dake tashi a hankali a cikin motar

A kofar gidan suka tsaya Aisha ta ringa sauke kayansu murna fal zuciyarta tana kaiwa ciki sannan ta dawo ta dan rage tsayi tana yi masa godiya ina ya zabga mata harara ya ce" Malama mike ki bace min da gani ni"

Da daria ta mike din ta yi ciki

KAUSAR da kula ta kalle shi ta ce" Kamar ranka a bace ko ciwon kan ne?"

"Na gaji ne" ya bata amsa , sai kuma ya kalli agogo ya kalleta zai yi magana ta sake fadin" Ko na fadawa Mama ta maka kunun ayar nan? Na ga kamar kana sonshi?"

Ido ya zarro da sauri ya girgiza kansa, wanda hakan har ya so dan bata mamaki, sai kuma ya cire mata mamakin ta hanyar fadin yau ba zai fito ba zai je makaranta ne, a zuciyarsa kuwa yana ambaton ina shi ina kunnun nan? Abu dadi a baki yana sha kamar kar ya kare ashe ashe yana shirya masa tashin hankali ne? Saboda kunnun ayar nan da ya sha jiya a gida ya gaza barci har kusan biyu na dare yana fama da ciwon ciki, ga tarin gajiyar kasuwa da ta huldodinsa na gida da waje, a haka a dadafe ya kai kiran sallar fari , an yi kira kuwa ai ba barci dole ya sake fitowa ya sha madara mai dumin gaske har yana zufa, shi dai ya rainawa kunnun aya wayo kuma ya yi tirrr da shi dan bai kyauta masa ba

Gannin yau kamar yan shiru shirun sun fi komai yawa ya sakata yi masa salama ta yi shigewarta gida tana cire hijab dinta tana shafa cikinta da yake ta sabewa saboda abin azumi a jikin nata shi kadai ke raguwa sosai sanadiyar azumi ama ba wai shafewar dindindin ba, dama da azumi haka yake mata yakan ragu sosai, har bayan azuminma yana iya daukan kusan wata biyu bai koma yadda yake ba, sai fatar jikinta dake dan karra gyaruwa daga yannayin haskenta kadan ta karra yin luwaiwai, ko dan zaman gida ne da hutu ba hanyar school?, Itafa ba fa fara bace aa, fatar mahaifiyarta ce mai haske haka, irin bakin nan mai haske mai kyau, to haka yannayin fatar jikinta take

"KAUSAR, wannan kaya haka jama'a mutanen nan su basa gajiya da dawainiya ne Fisabililahi?, Shin auren yaron nan ni me zan yi na kyautatawa ga ahalin nan?"

RUKAYA dake ta farin cikin itama domin sun zagaye kayan sunna ta dadagawa ne ta ce" Mamanmu, sai dai a je tunda safe idanma da hali a kwana a cen ko kwana biyuma , in ba wannan ba ina muka ga abin basu?"

Mama ta yi murmushi ta ce" Gaskiya ne daurin aure har amsar amarya da mu za'a yi shi, ama kuma du yawan arzikin mai arziki yana jin dadi idan ya ga an masa kara an kula, in sha Allah komai kankantar bajintarmu zaki ga mahaifiyarsa da shi kansa sun ji dadinta, duba fa ki gani, idan ta tashi ware mana abu harta ni sai an ware nawa , lalle zumuncin mace da namiji akoy jin wani iri, ama idan har da kare dokokin Allah sai nace na Kausar da TAUFEEK alkhairinsa muke gani, idan an yi aure kowane ya kama gabansa kuma shikenan sai zumuncin mu iyaye in mun rike"

KAUSAR ta yi murmushi tana kaiwa zaune hadi da neman wajen kwonciya ta ce" Mama, yinwa nake ji"

Mama ta dungure mata kai ta ce" Zaki fara ko?, Ke kam ki yi kokari ki daina yiwa ciki bauta, wannan lamari naki da cikinki abin haushi, ace mace kadan ta ji yinwa ta kama raki kennan?, Azumi dai baya son haka, tashi maza yau ke zami tuka tuwon sahur kin ga na shinkafa za'a tuka kuma kin fimu iyashi"

Baki ta zumburo ta ringa kyakyafta ido tana jin gaba daya kasala da juwa sai yanzu suke lulubeta, ama a haka dole ta mike ta kama aikinta dan kuwa kowa da aikinsa basa barin Maman ta yi komai har a sha ruwa sai iya aikin Baba wanda har yau suke mamakin irin yadda Mamansu bata sakar masu aikin mahaifin nasu, lokuta da dama idan sun yi nacin hakan sai tace to ita kuma a ina zata samu ladan ? Kowa ya yi inda yake da lada kawai su barta da aikin mijinta (wannan din wata hikima ce da hanyar da zaka iya ba yayanka tarbiyyar sanni da kuma sake rike girman miji a bayyane da kuma badini, domin a rayuwa yaya babu abinda ya kai iyayensu girma da daraja, sukan dauki dukkan abinda iyayensu suka dauka da daraja suma da daraja ne, idan har uba na so ya'yansa su raina shi ko su ringa yi masa biyayar dole to ya ringa wulakanta mahaifiyarsu a gabansu , a cikin iyayen kuwa wace ta fi gagawar saka zuciyar ƴaƴanta biyaya da daukan launin abinda take so itace uwa, uwa idan ta so za'a gyaru, in ta ki za'a lalace kuma a kan turbar da ta dora ne, Muna karbe du wani motsi na iyayenmu muna hanna su yi dan ba zamu iya muna zaune su motsa su yi wani abin ba bayan gamu a zaune, hanyar da suke bi ta nuna mana na mahaifinmu bamu da hurumi a ciki na matukar shiga zuciyarmu har muma muna gina tamu rayuwar a haka, idan har a gidan aure irin haka ta samu kuwa inaga da izinin mai sama jin dadin zaman auren zai samu domin akoy gannin kima da biyayar wanda ya ajiyeka...., Allah ya dafa mana)

A lokacin da Baba ya zo aka sha ruwa aka wuce masalaci sai kusan goma suka dawo suka zauna fan cin abinci, a kuma lokacin ne Aisha da zumudinta ta kawowa Baba kayan
💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

*DA CIWO A ZUCIYATA*

💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

_MALLAKIN_

*SAJIDA NIJAR*

*FREE BOOK NE* 8️⃣

LITATAFAN MARUBUCIYAR

Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Neman na kaina
Bani da zabi
Bak'a ce
Kutkale
Makauniya ce
Mage
Duk nisan jifa
Idan ka raina inda kake
Dutse
Alkalamin kadarata
Bani da zabi
Dakika Biyar

Now

*Da CIWO A ZUCIYATA*

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Chapter 12 · 0% Book details