Sashe 95
Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kasa kasa Khausar ta ce" Wa'alaika Salam, yauwa please rike min in Bala boturan rigana".....a hankali, cikin rada rada ta yi maganar, sai dai idannuwanta na sauka kan Yumnah ta ja ta tsaya daga niyar karasawa inda yake tsaye yana kallonta da wani irin kallo mai wuyar fasara
Dan murmushi ta saki bayan ta dauke dubanta a kan Yumnah a juya ta nufi sam da plate din abincinta bata tsaya ta kara cewa komai ba, domin ba zata taba cin fuskar Yumnah ba, bata da wannan niyar, koda Yumnah na neman rainata ba zata bari su kona kawunansu a banza da wofi ba, idan har kishin ne zata fi so su yi mai tsafta ba irin wannan ba
Sai kuma ta lumshe idannuwanta tana jin banbarakwai wai namiji da sunnan Hajara, yau itace ke batun kishin Besty?
Murmushi ta saki ta gyara zamanta ta hanyar kwatanta daura kafa daya kan daya
Ya fi a irga da take ɗorawa tana saukewa dan bata saba ba, sai dai ta tirsasa kanta ta dora din ta kuma zaunar da kafar a haka cikin nutsuwa ta shiga cin abincinta tana jin kewar iyayenta da kannenta har kasan zuciyarta
A falon kasa kuwa da kyar Yumnah ta iya gaishe shi , domin tunda jinninta ya hau ta tsayar da dubanta a jikin Khausar ita da kanta ta ji ta sare hankalinta na neman idasa tashi
Silalewa ta yi ta haye sama, cike da tsoron juya bayanta dan haka kawai ta saka a ranta cewar mai wancen zai kalli nata kuwa?
A hankali TAUFEEK ya zauna yana ajiye wayarsa gefen kujera ya kai hannunsa daf da habarsa ya dan shafa yana murza sajen wajen tamkar wanda wajen ke masa kaikayi ko ciwo
Idannuwansa ya daga ya sauke saman wayarsa ya dauki wayar ya amsa kiran da ke masa
Dangane da aikinsa ne na makaranta da ya kwana biyu bai leka ba, nan ya gabatar da uzurinsa sannan ya ajiye wayar yana lumshe idannuwansa
Yana ji a ransa cewar har yanzu bai idasa zama cikakken magidanci ba tunda har zai tashi ya sauko du su watse su barshi a nan
Wata zuciya na rikirkirtashi idan ya yi tunanin rike mace biyun nan, anya kuwa wasan da zai iya ci gaba da bugawa ne?
Ajiyar zuciya ya sauke ya mike direct ya karasa dakin Khausar wace ke zaune bayan ta gama ci ta rufe idannuwanta a kan kofar shigowar ta kasa fita dan bata an ko Yumnah na tare da shi ba ita kuma niyarta daban da ta da, dan ko ba komai ai shekarunta sun isa su bata damar damawa rashin samun wajen yin ne dole ta noke
Da salama ya shigo yana sauke kaifafun idannuwansa a saman fuskarta
A hankali ta sauke kafar nata dake daya saman daya ta yi iya yinta ta zuba nata dubanta itama a cikin nasa tana amsa salamar a saman lebenta sannan ta zuba masa ido har ya karaso ya zauna daf da ita kafin yake kai bayansa gaba daya ya kwonta saman bed din
"Dan wajen kuwa ya kasance a bakina har garin Allah ya waye" amon muryarsa a jiya ya dawo dodon kunnenta a lokacin da take tunanin abinda ya dace ta fara gabatar masa
Da sauri ta mike tsigar jikinta na tashi ta shiga sauke numfashi tamkar ta yi gudun tsira sannan ta juya da dan sauri ta nufi hanyar frij dinta ta bude ta dauko tataciyar madarar wajen hajia dan ita kam tana jin dadinta sosai ta dauki kofin dake zice ta riko ta karaso daidai lokacin da ya dan mirgino ya zuba mata ido yana kallonta
Dakatawa ta yi dan daf da shi ta zuba hannunta na son kwasar rawa
Murmushi ya saki hadi da ajiyar zuciya a hankali ya mika hannunsa ya riko kofin sannan ya mike tsayen da take ya zamto ya kere tsayinta ainun ya taho da hannun nata da kofin daf da bakinsa a hankali ya shiga sha yana lumshe ido
Cikin rashin karfin jiki ta janye dubanta daga yadda yake lumshe idon cike da jin kunya ta dora duban nata a damtsen hannunsa dake mike daf da kugunta
Hannunta ta so janyewa da nufin juyawa, a hankali ya saka hannun nasa ya janyota jikinsa ta hanyar janyo kugunta har sai da jikinsu ya hadu da dan karfi sannan ya dan sasauta mata ya tsareta da duban dake daf da kasarata
Kasa kasa cen ta furta" Barka da saukowa , yaya gajiya?"
A hankali ya dago habarta da ta yi furucin cen cikin makoshinta tamkar ba Khausar dinsa dake ihu in yana waje ba abinda ya dameta ba
A hankali ya fitar da harshensa ya kawo daf da lebenta ya dan lasa yana kallon yannayinta
Cike da jin kunya ta rufe idannuwanta da hannayenta biyu da suke dauke da jan lalle sannan ta nemi shigewa cikin jikinsa cikin dabara ta sake boye fuskarta a kirjinsa
Ido ya zarro cike da mamaki yana kallonta lokaci daya zuciyarsa ta shiga dokawa
Cen kasa kasa ta furta" maimakun ka huta zaka fara neman magana ko?"
TAUFEEK ya lumshe ido yana jin kusoshin kansa na daf da kuncewa, gaba daya fushin da ya kunso da tunanin anya kuwa a bashi kula yadda ya dace suka gudu suka barshi da wani irin shauki mai wuyar fasara
"Kunyana kike ji?" Ya samu harshensa da furta kalaman da ba ainahin su yake son fada daga bakinsa ba
Bata bashi amsa da fatar baki ba, sai da kanta ta dan daga a hankali still tana jikinsa kanshin turarenta ya hade da nasa
Ajiyar zuciya yake saukewa a jejere a hankali ya karasa wajen bed din nata da ita ya zauna ya dorata saman cinyarsa abaya ko jin nauyinta kasa kasa yake shafa hannayenta yana son dago fuskarta ya ce" Dama za'a ji kunyana?"
Yanzunma bata ce masa komai ba, cikin dabara ya kai hannunsa saman cinyarta yana ji a ransa dole ya bita a hankali, sannu sannu ya ce" why kika rufe min kofa, bayan na san na yi barna? Ko nuna min za'a yi da likita fa na kwonta?"
Har ga Allah yanzun kam ji ta yi kamar ta zura da gudu, dan har sai da ta so kwace kanta daga jikinsa ya kiya ya sake maidata ya rungumeta sosai a jikin nasa
Cen kasan makogwaronta ta ce" Abinci fa?"
Yanzun dagowa ya yi dan dole ya zubawa fuskarta ido, kai? Ya bani ya lalace, kamar ba ita ba
A hankali ta samu ta mike daga jikin nasa tana jin yadda itama nata kirjin ke dokawa
Da dabara ta samu ta rike kanta, cikin sabon salon yi masa magana ta ce" Abincin fa? Tashi mu tafi ka ci abinci urs bosss"
'Ya Salam ya ayana a kasan zuciyarsa
A fili kuwa ji ya yi wani irin girma da isa na shigarsa
'dama na san tsarina ce, shi yasa ta zama zabina' ya sake ayanawa a zuciyarsa
A bayane ya riko hannunta yana bin dima diman abinnan da kallo ya ce" Wai da in dan kashe arna kafin in ci abinci kin san lada ne da abin sosai anMatana"
Murmushi ta yi ta janye hannunta ta karasa wajen tufafinta ta bude ta ciro hijab dogo ta zumbula sannan ta juyo inda yake zaune jiki a mace ta wani sakar masa fari da madaidaiciyar fuskarta da dara daram idannuwanta da suka dauki kwali a hankali ta ce" wa'inda ka kashema ai sun isa sir, taso mu je"
Ido ya zarro yana binta da kallo har ta bacewa ganninsa
Ajiyar zuciya ya sauke a ransa ya ayana' Ni da ban mutu ba, ai dole na raya sunna matata'
Sai da ya je dakinsa a gagauce ya yi wanka ya cenza tufafinsa sannan ya je ya tiso keyar Yumnah suka sauko dan har yanzu basu yi wani zaman a zo a gani ba
A wajen cin abincin Khuausar ta zubawa kowa bayan ta ji ra'ayinsa ita kuma ta zuba jus kadan tana dan sha tana tunanin abinda take son tambayarsa dan ta ci nata abincin har suka gama ya masu umarnin zama a falo
Bayan ya zauna din shima ya fuskance su, da yannayin cikakken magidanci ya yi masu salama sannan ya ce" Ina son yin magana da ku, bana son kowa ya katse Ni da abin bacin rai ko na raini wa junnanmu, ina fatan kun fahimta?"
Su dukansu sun bashi hankalinsu ne kuma sun amsa shi, dan bai bada fuskar raini ba ko kadan
Da kula ya ce" ina so ku fahimceni ku kuma dauko maganana da mahimmanci kamar yadda na dauke ku da mahimmanci, ina so kowace ta sani gidan aure take, zaman aure muka taru mu yi wanda nake fatan ya zame mana sanadiyar shiga aljanna, dole ne ku koyi hakuri da junna, dole ne ku iya kaudawa junna kai a wasu abubuwan dan a zauna lafiya, hakan na nufin ya shafi kowa ba maganar karantar shekaru ko girman shekaru a gidan aure, dan du wace ta iya daukan namiji tana cikin layin wace Allah zai kama idan ta cutawa yar uwarta dan son rai"
Dakatawa ya yi yana kai dubansa wajen tv ya kashe ya sake maido dubansa kansu, yanzunma da yannayin serius ya ci gaba da fadin" kowace nan ra'ayina ne, babu wace aka min dole ko aka cusa min, ina so ku san ina iya zaman aure da ku ne dan ina son ku!"
Su dukansu sai da suka kalle shi wannan karron sannan suka kalli junna, shi kuwa ya yi kamar bai ga abinda suka yin ba ya ce" Dan haka ina so kokowarku ta zamto dan ku gyara zaman mu ba dan daga min hankali ba "
Khausar ta turo baki sosai tana dane kanta, dan har ga Allah bata taba jin wani guguwar balaki irin na yanzu ba, kuma abin haushin a kan gaskiyarsa da yake magana ba karya ba, da kyar ta dauke kanta ta sada kasa tana jin lokacin da yake tambayar shin me suka tsaida maganar kwana?
Yumnah kanta kasa furta a ta yi, zuciyarta tafarfasa kawai take yi tunda ya fara magana yana nuna darajar su daya a zuciyarsa abin ya nemi zautar da tunaninta
"Magana nake yi" TAUFEEK ya fada a nutse yana sauke masu duba