← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 116

Sashe 2

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fuska ya dan gimshe ya kalli inda take zuwan sannan ya maida dubansa kansa fuskarsa a dan gimshe ya ce" Ka fa san bana son haka ko? Na sha fada maka ka mutuntata ko ka shafa mata lafiya, kowa ya yi ta kansa ko?"

Zai bashi amsa ta karaso inda suke tsaye fuskarta dauke da madaukakin murmushin gannin ya ji maganarta har ya zo din kamar yadda ta masa maganar jiya da yama da suka rabu daga wajen exercice cewar ya tabata ya zo aji a kan lokaci ya kuma yi exam din nan a cike kar ya saki ya ki zuwa fa?

Tsayawa ta yi dan daf da shi ta ce" Bani abin kunnen bawan Allah?"

Murmushi ya yi yana fan shafa bayan kansa ya cire abinda ke cikin kunnensa ya mika mata da wayarsa kirar iPhone 11 pr ita kuwa ta kashe ta bude jakarta inda ta san ba zata fashe ba ta saka masa a ciki sannan ta rufe ta sake dubansa ta ce" Ka dauki shafukan fa na fada maka jiyan kuwa?"

Shnayayun idannuwansa ya dan bude kamar wani mai shan abin maye bayan babu abinda yake sha haka yannayin idannuwansa suke ya dan kalleta kadan ya kuma gyada kai, shi fa du ba wannam bane a gabansa, abinda yake gabansa aikin da Mahaifinsa ya saka shi yace kuma karfe takwas da rabi ya zamto yana bakin shagonsu na wajen sabon gari dan a sauke kaya a gabansa ya kuma daidaita komai , yau dai wunnin yau sam bashi da wani lokaci gaskiya, shi yasa ya yi safiya ya zo dan baya so su raba hali saboda jarabawar nan, idan dai ta ga ya zo ai ba zata ji haushi ba ko ta yi fadan bai zo ba yana wasa da karatu

Da jin dadi ta yi gaba dan duba sunnanta ta barsu ko ci kanka bata cewa Kamal ba, haka shima da ido ya rakata kafin ya dauke kai yana girgiza kansa yana tunanin ta yiwu tun fadan da aka yi ne bata masa magana take masa gaba, bai sani ba cewar ita ba maganar gaba a cikin tsarin rayuwarta ,idan har ta kula cewar zamanta da kai akoy wani abu mai kama da wulakanci ko cin zarafi ne zata janye jikinta cikin salama ba tare da ta yi naci ko ta dorawa kanta abinda zai dameta ba,
Hasalima abokin nasu da suke takama da shi shine ya yi mata nacin son kasancewa aboki a wajenta itama, daga wannan bata tunanin akoy wani abu da zai sa ta zamto abokiyar gabarsu, ko fadan da aka yi budurwarsa ce take tunanin meye tsakaninsu haka? Kamal din wajen fada mata bafa soyaya sai ya yi aiki da munanan kalamai da suka sa ta daina gannin kimarsa....., Lalle ita talaka ce, ama a cikinsu ai talakawan da yawa,haka kuma yannayin jikinta ita baya damunta dan ta san Allah ya haliceta haka , haka kuma yake son ganninta, bata tunanin wani bawa zai iya tsayawa ya zageta a duniya dan kawai ita din tana da jiki da ake kiranta da yar lukuta saboda shi, ba kuma ta tunanin bata je neman alfarmar wani wani ba zai wulakantata ba, idan sun kula zumunci ne da zamani yazo da shi tsakanin namiji da mace na abotaka, nata kawancen bai kaucewa tsarin adininta ba domin akida gareta shi kuma yana da addini, layin rayuwarsu ba daya bane dan shi yana zuwa makaranta ne dan yaki da jahilci , dauke kewa, jin dadin mu'amala da jama'a, inda ita kuma take karatu dan samun abin sakawa a baka gobe idan Allah ya nufa!, Ita karatu ne take yi da dukkan karfinta dan bata da madafar da ta wuce bin abinda ya dace dan ta samu rabauta itama da nutsuwar zuciya, shi kuwa wadinnann ya dade a cikinsu domin ya
💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

*DA CIWO A ZUCIYATA*

💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

_MALLAKIN_

*SAJIDA NIJAR*

*FREE BOOK NE* 2️⃣

LITATAFAN MARUBUCIYAR

Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Neman na kaina
Bani da zabi
Bak'a ce
Kutkale
Makauniya ce
Mage
Duk nisan jifa
Idan ka raina inda kake
Dutse
Alkalamin kadarata
Bani da zabi
Dakika Biyar

Now

*Da CIWO A ZUCIYATA*

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata💃💃💃💃💃

A lokacin da ta shigo gidan kowa yana nan

Bata tsaya tsaye tsaye ba alwallah ta daura kawai ta shige dakinsu ta zauna ta bude litafinta tana yi tana kallon yan uwanta dake hira da makociyarsu wace ta shigo su kuwa sunna tsakar gida da mamansu sunna tataunawa kan shirye shiryen auren y'arta budurwa

Aisha ce ta kula da yannayinta domin sosai yannayin nata ke nuni da ranta a bace yake, dan haka da kula ta ce" Hajia sister wai waye ya tabo ki haka?"

Kallonta *KAUSAR* ta yi a hankali , sai kuma ta kalli inda mamansu ke fadin maza Rukaya ta fito ta zuba masu abinci su ci

Dan sa'ida ta ji a ranta, domin har ga Allah tafiyar da ta yi dambun nan gaba daya kamar bata ci komai ba take ji, du ya yi kasa, dan haka ta kasa ba Aisha amsa har Rukaya ta zubo abincin ta shigo da shi dakin lokaci daya kuma suka mike sunna fita dan Maman ce ta shiga fadan kar su kumkume daki su ci abinci

Du a tsakar gidan suka zauna saman tabarma da kwanon da Aisha ta janyo masu ruwan rijiyar ta ajiye sula shiga cin abincin a cikin kwano daya gaba dayansu cikin nutsuwa

Ajiyar zuciya makociyar Mama watau maman Naïma ta sauke a ranta tana jin tausayin Maman da ƴaƴanta......., Har ga Allah abin a tausaya ne idan aka yi dubi da yan matan sun fa kai sun kawo ama shiru ko daya ba'a aurar ba, su jira suke yi KAUSAR ta samu miji, wace idan har rayuwarta za'a zauna a duba babu wannan tsarin a cikin tsarin rayuwarta......., Babu wanda zai ce yau ya taba gannin saurayi a matsayin na KAUSAR, yarinyar kamar wata mai bakin aljani ita din da kantama bata da alamun ta damu da wata magana ta d'a namiji a rayuwarta, wani fannin kuwa har ga Allah ana yi mata duba ne na wace bata bada wani dan motsin da zai nuna cewa ta dan itama mace ce tana cikin layin mata a rayuwa ba, ko me yasa ta zabi gabatar da rayuwarta haka? Allah masani

Sunna nan zaune har yan matan suka gama cin abincin, cikin gagawa ta shirya ta daura alwallah ta dauki salaya ta saka a jakarta ta kuma daukan hanya domin safe da yama ne jarabawar kwana uku

Ta yamar ma bai zo ba haka ta sake shako wani takaicin harda yiwa kanta fadan in sha Allah ba ita babu shi, tunda a zamantakewarsu ba zata iya fada masa magana ya dauka ba, tunda bata isa ta nuna masa mahinmancin karatunsa ya gane me take nufi ba, ita har yanzu ta kasa gane ina ya dosa , in karatun ne baya so ai ba dole ya yi zamansa mana a gidansu? Ama sai ya wani dauko kafa ya zo makaranta ya koma har gashi yanzu ana cikin lokaci mai mahimmanci wanda idan baka samu abin kirki ba to fa ka san me ka shekare kana yi shi bama zai zauna ya yi ba? Tana matukar jin takaicin rashin maida hankalinsa a kan karatu kamar yadda zata iya ji a kan yan kannenta A'isha da Rukaya, bale dai shi da yake biyan makarantar nan mai masifar tsada, ita kanta da ta samu shiga saboda kyan sakamakon jarabawar shigar da takardunta suka yi bata wasa sai shine zai yi wasa?
Haka ta yi karatunta bayan sun ci abinci ta shige da wuri ta yi sallah ta yi kwonciyarta domin yau ko abanta ba zai sameta ido biyu ba, haka take idan ana jarabawa bata da lokacin kowa sai an gama
Chapter 2 · 0% Book details