← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 116

Sashe 38

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da ido yake kallon fuskarta gannin ikon Allah su jan baki, su kwali su pankeke in ji hajia, daidai itama ta dubo gannin an dage, dan haka ta ja numfashi da sauri ta karaso inda yake tsayen, hakan ya saka dadade, nutsatse, hautsinanen, fitinanen kanshin turaren fara isowa kafin ita, a dan rikice ta ce" Dan Allah dauko min hijabin baba freind idan na fita sai na saka, ni kam na bani da rikicin hajia wai a haka zan fita fa"

Idannuwansa ya dauke a kanta ya sauke kan uwar daban, ita dai matar nan baba a wajen mai kwanoni, da ta dawo fuska na mata gyatsine kamar tsantsamen kunnun safe, ta wani cakare irin ko wace wace tana sake kankance ido ko ganne shi ne bata yi ko me take nufi oho?

Fuska ya daure sosai yana kallonta ya ce"

Wannan tsohuwa bata son zaman lafiya🙄🙄🙄

*ALLAH BAI SAUKAR DA CIWO BA SAI DA YA SAUKAR DA MAGANINSA*

Ni ce dai Fareeda Abdallah, na sake dawo muku da tallen magungunanmu da zuwa yanzu bazan iya ƙayyade yawan waɗanda suka dace da biyan buƙata sanadiyyar amfani da maganinmu ba. Alhamdulillah! Ƴar'uwa ki gwada, wataƙila warakarki na tattare da maganinmu.
Haihuwa ce baki taɓa yi ba ko kuwa jinkiri kike samu sanadiyyar planning ko kuma haka kawai? Muna da ingantaccen maganin rashin haihuwa ga mace da namiji, wanda za ki bada sadakar 2k ga matsalar ko wane ɓangare. In sha Allah za ki dawo da godiyarki bayan amfani da maganinmu.
Sanyi (infection) ne yayi miki yawa yake saka ki ciwon mara, zubar farin ruwa, ƙaiƙayi, ƙuraje, ɗauke ni'ima, har ma ya saka mijinki ya dinga miki gani-gani saboda bakya gamsar da shi? Da naira 3k zamu haɗa miki magungunan da za kisha ke da Oga in dai kika yi amfani da su ku da sanyi har abada in Allah ya yarda.
Muna sayar da ingantaccen haɗin sabaya, wanda zai sa nonuwanki su cicciko, hatta fatar jikinki sai ta murje sanadiyyar shan kunun sabayarmu. 2500 bokiti 1litter.
Muna da maganin wankin nono ga mai ciki da mai shayarwa, wanda indai kikai amfani da shi yaronki zaiyi tubarakallah, ba ruwanki da laulayi. Muna da ingantaccen maganin Daji (Cancer), typhoid, maleria, yaron da yayi nauyin ƙafa, da sauran cututtukan da ban ambata ba.
Muna aika maganinmu ko ina tsakanin Nijar da Nigeria, ga masu buƙatar magani da gaske su tuntuɓeni akan lambar wayata 07039080978, ko 09077591726

Noted: *MAI SON MAGANINMU IDAN BA A KADUNA YAKE BA, SHI ZAI YI KUDIN MOTARSA HAR ZUWA INDA YAKE, BABU INDA BAMA TURAWA IN SHA ALLAH.....SAI KUN ZO*
💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

*DA CIWO A ZUCIYATA*

💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

_MALLAKIN_

*SAJIDA NIJAR*

*FREE BOOK NE* 2️⃣2️⃣

LITATAFAN MARUBUCIYAR

Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Neman na kaina
Bani da zabi
Bak'a ce
Kutkale
Makauniya ce
Mage
Duk nisan jifa
Idan ka raina inda kake
Dutse
Alkalamin kadarata
Bani da zabi
Dakika Biyar

Now

*Da CIWO A ZUCIYATA*

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata💃💃💃💃💃

Fuska a hade ya ce" Ke, je dauko hijab baba maza ki sameni a mota !"

Daga haka ya juya ya yi gaba ko gaisar da Hajiar bai yi ba

Khausar ta yi tsuru tsuru ta kalli Hajia ta kalli hanyar da ya bi ya fita ta gaza koda daga kafarta ne bale ta dauko din, haka kuma ta gaza bin bayansa

Hajia kuwa ta ja ta harde hannayenta ta ce" Yau sai na ga ni uwar mai kwanoni zaki ji magana ko wancen marar jin tsoron Allahn!"

Khausr ta hadiye yawu da kyar

A hankali ta ce" Hajia na tafi sai na sauko"

Hajia ta washe baki tana gyada kai ta ce" Ni na san nice zaki fi kauna yar nan, a dawo lafiya ina nan ina jiranki"

Tamkar an zare mata laka ta samu ta fito tana ta rungume hannu a kirji ta nufi motar dake parker dan alamun tsayuwar motar suka nuna mata yana ciki

Da sauri ta samu ta fada motar ta rufo tana sauke ajiyar zuciya
Juyowar da zata yi sai da gabanta ya fadi sakamakon kaifin da idannuwansa sukai mata a fuska yana binta da kallon me nace maki?

Fuska ta marairaice ta ce" Yaya kake so na yi ne? Hajia fa na tsaye ka san ai ba zai taba yiwuwa na take maganarta ba ko?"

Motar ya kunna , cike da jin haushi ya ce" Hakane, sai nine ai maraininki, nace nine tawa maganar ba a bakin komai ba, tunda na kula baki dauki damuwata a komai ba, jiyan nan kin rainan hankali abinda na hannaki kin sake yi, kuma yau kin kuma yi, sai ki ci gaba, ki ci gaba Khausar!"

Daga haka ya ci gaba da tukin
Sunna shigowa harabar asibitin ya lalubo face masque ya saka a fuskarsa cikin dabara sannan ya parker dan nesa ƙadan yana jiran ta gama saka farar rigar da baby hijab din, domin ba abinda ya dameta a nan ta cire dayan hijab din ta ajiye ta saka karamin fari kal mai kyan gaske ta kuma saka farar rigar

Da yannayin tsokana ta dube shi ta ce" Ka kuwa san yanzu tsaf bake iya maka allura na maka karin ruwa da komai da komai?"

Ido ya zuba mata, yadda take saki murmushi irin an fa fara kwarewar nan ya saka shi yin murmushin shima aman bai ce mata komai ba

Ta dora da fadin" Na tabata idan ka samu kaima shekarar badi in sha Allah nice nan zan koya maka, dan bani kwondona na tafi "

Kwondon ya juya baya ya dauko ya bata, sannan ya dakattar da ita ya dan daga farin kyalen da aka rufe kwondon ya saka kudi a ciki a hankali ya ce" A dawo lafiya likita"

Kudin ta kalla tana zarro ido ta ce" Wannan fa?"

Shima ya zarro mata idon ya ce" Kudin kifi da dambu ne "

Idon a zarre ta ce" kuma duka wannan? Wannan ai sai na ciyar da likitocin emrgncy da shi "

Ya yi murmushi ya ce" Ki tafi mana ana jirana fa"

Murmushin ta yi itama tana kudurta zata dawo masa da kudinsa in ta sauka, dan babu abinda zata siya ga abincin nan Hajia ta zubo mata zai isheta ne, sai kawai t dan ja baya tana masa alamun sai an jima sannan ta juya ta nufi ciki

A wannan ranarma sun sha aiki, aikin da a yanzu take iya cewa idan bata fita ba sai ta ji wani bari na zuciyarta na cen, du irin abinda idannuwanta ke iya ganni na tashin hankali abin ya zame mata wani jigo na barin zuciyarta domin a ranta take gama yarda cewar fitarta aiki taimako ne wa al'uma da ita kanta, idan tana taimakon marar lafiya a yanzu tana jin wata irin nutsuwa a cen kasan zuciyarta, in ta ga an samu an fitar da mutun lafiya daga emrgncy sai ta ji wata salama tamkar mutumen nan danginta ne

Yau da wuri aka salameta, hakan har ya bata mamaki, domin tun bayan sallar la'asar aka ce ta shirya ta tafi gida, dama fitowar tasu suka sani basu san komawarsu ba, domin emrgncy ko manyan ma'aikata kan fita su je wani sa'in saukarsu ta zamto ba yadda suka sn zasu sauka ba, dan idan wani aikin ya samu dole su zauna, domin wani lokacin hargitsewa gidan ke yi sosai sai gyaran Allah

Da murmushi ta fito saboda tsokanarta da abokin aikinta ya yi cewar yau za'a je a sha barci an tashi da wuri su Hajia Khausar

Bata taba tunanin iya gannin TAUFEEK a wajen masu parking din motoci ba, sai ganninsa ta yi, hakan ya bata mamaki ainun, harma ta kasa boyewa ta ce" Aa, yaya aka yi ka san lokacin tashina bayan ba lokaci ne a kayade ba?"

Dan murmushi ya yi yana basarwa ya bi kwondonta da kallo, ya ce" Baki ci komai ba hala tun safe?"

Murmushi ta yi bayan ta shiga motar tana jan abu ta rufe ta ce" Na zatama zan iya ci tunda na zo da shi, sai kawai na manta da shi kwata kwata, sai yanzu da na shiga cenza kayana na ganshi kuma ka ga har ya fara bacewa ba damar na kyautar tunda nima ba zan iya ci ba"

Kai ya gyada ya tayar da motar ya dauki hanyar gidansu da ita
Chapter 38 · 0% Book details