← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 116

Sashe 10

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rukaya da tuni ta fara gargadar murya zata fashe da kukan itama ta ce" Auntynmu wani abu ya same ki? Ke da waye kike kuka?"

KAUSAR ta yi iya yinta dan ta yi kukanta ita kadai ama abin ya faskara, a dole ta dora kanta a gefen kafadar A'isha tana kukan ta ce" Aisha, na shiga uku, wayo Allahna, A'isha shin menene cutar da maza basa so a jikina? Na zama katuwar budurwa a cikin gida na kasa matsawa da tuntuni kuma kun samu kun matsa?, Aisha ku bar gannin na mayar da hankalina kan karatu ba dare ba rana ni dai karatu nima fa mutun ce kuma abinda kowa ke so ina so, Aisha samuwa ne bai yi ba a dole na hakura na rungumi karatun dan shi baya min tawaye, Rukaya kunna gani in dai aka ce ana sona dan tsokana ne ko dan a batan lokaci, dududu yan matancina bai fi a irga da na hadu da su ba suka nuna na masu, To ni yaya zan yi da raina ne?, Ni babu ruwana da sana'arka in dai na halal kake nema, nagartace mai halin datako nake nema wanda zai rikeni da mutunci nima, Aisha kunna gani habaice habaicen dangi har bana so a yi taron da dole sai mun je dan ta yannayin kallon da ake bina da shi kadai sai in ji du na tsani kaina, domin wasu basu zageni ba ama kallon da ake bina da shi yana fasara abinda aka kule a zuciya a kaina, shin ba za'a fahimci y'ar sunna nake du rashin hankalina ina son raya sunna ba?, Kun ga dai yanzu Abanmu shima hankalinsa ya karkato kanmu, kuma yana fa gaskiya shekaruna nawa bale ku?, Ina matukar jin tsoron na kasa farantawa Abanmu bayan shi rayuwarsa kulun a cikin faranta mana yake , bawan Allahn nan a duniya bashi da damuwar da ta wuce tamu, Rukaya nima ina so na amsa shi idan ya sake mana tambayar nan dan bana so hankalinsa ya tashi a kaina, wayo Allahna ni duka kaf kowama ya tsaneni, na gaza samun tsayaye ? Ku duba ku gani yadda na gandame na gaza samun tsayaye?, Ni komai tsufan mutun ni dai a min auren hankalin su Mama ya kwonta summa, a anguwar nan fa da gangan ake yadawa mamanmu magana kunna kallo, yi take yi kamar bata gane yaren da aka haifeta cikinsa dan a zauna lafia, wai mutane dan rashin jin tsoron Allah basa gane cewa auren nan lokaci ne sai su ringa maka muguwar fasara?, Aisha Rukaya kun san Allah idan har na taba saka iskanci a raina ya hanna min kula namiji da nufin aure Allah ya hanna min dukan farin cikon duniya da kiyama, kun dai ga TAUFEEK ne kadai namiji kwal a duniya da muke kawance zumunci wanda ya gama gari yanzun ba wani abin mamaki bane hakan ko? To ku shaida ne TAUFEEK shine mai min fadan in gyara ba dai ya yarda ya batan ba, kuma a kan mutuncina TAUFEEK sai ya bata da du wani saurayin da ya so zagina dan ni ganau ce ba jiyau ba , ko baban abokinsa da ya taba ce min wai me yasa ni hijab hijab ina boye jiki kamar mai gyambo har gobe basa shiri dan a gabana a gabansa yace bai taba tunanin zai wulakantani ba, ya daukeni kanwarsa kawarsa aminiyarsa ba zai bari a wulakantani ba, kin ga shi dinma jiya na masa rashin kunya ya kyaleni irin jeki katuwar banza ki yi haukanki ko? Shikenan A'isha ni kam duniyar tai min zafi Allah ma kuwa....."

A hankali mahaifinsu ya yi baya, ya jima da dawowa anguwar daga wajen jana'izar y'ar abokin nasa, gannin bata dawo ba ya saka shi zama cen wajen mai shayi sunna taba hira yana kuma kallon hanyar da zata bilo,
Yana gannin shigowarta da yannayin fuskarta ya taho shine ya iske koke kokensu da magangannunta

Ajiyar zuciya ya sauke a soron gidansa ya daga kansa sama a hankali ya furta" Allah kaine Allah, kai kadai ka san abinda ka boye a jinkirin auren y'ata, Allah kai ka halicemu kuma ka bamu jarabawar rayuwa dan ka auna imaninmu wanda zai karra mana kusanci da kai, ya ubangijin al'arshi idanma KAUSAR bata da rabon yin aure a duniya har ta koma gareka ne ni bani da ja kuma nani da matsala a abinda ka kadartawa bawanka, Allah ina rokonka a tafiyarta da dawowarta a mu'amalarta ta yau da kulun ka karra tsareta ka kareta ka hanna dukan wani mugun abin dake iya samunta wanda zai saka mu zubar fa hawayenmu a kanta, ya ubanji ga baiwarka nan idan har tana da rabon yin auren kuwa ka fitar mata da miji mai jin tsoronka, mai ibada, wanda zai riketa dominka ya zamto malami, yaya, amini, masoyi a gareta, da yardarka ba zan kuma daga mata hankali ba, ama zan ringa tuni da maganar auren dan ta ringa kokari irin nata, Allah na gode maka da yau har ta je ta yi kitso mamanta kuma tace harda kwaliya ta yi, ka karra kare min ita a duk inda take....."

Adu'ar da ya yi kennan kafin ya fice daga gidan dan zuwa samun liman ya karra amso aduo'i kamar yadda ya saba

A cikin dakin kuwa rarashinta suke yi har sai da ta daina kukan ta dawo sauke ajiyar zuciya

A tausashe tamkar sunne yayun suka ringa nuna mata cewar kowani bawa ai da irin kadararsa, jarabawa ce ta ubangiji kuma alhamdulilah Allah ya basu iyaye masu tausasawa a dukkan rikita rikitar dake iya samunsu yau da gobe a cikin gidansu
Cikin ikon Allah suka samu ta saki jikinta sosai sai ajiyar zuciyar da take ta saukewa kafin A'isha ta dauki wayarta ta buga numbar TAUFEEK bayan tace bara a mata kiran TAUFEEK din ta bashi hakuri tunda da kanta ta gane itace da laifi tace ta masa rashin kunya

Kira na farko bai daga ba, sai a na biyu ne ya daga kuma ya yi shiru ya ki ya yi magana hakan ya sa Aisha yin murmushi dan ta san TAUFEEK ba dai zuciya ba ta ce" Yayanmu barka da warhaka, dama bamu jika ba muka ce bara mu tabo mu gaisar da kai"

Amsata ya yi jin A'isha ce sai kuma ta ba Kausar wayar tana fadin" Amshi aunty ga yayanmu nan"

Wayar ta amsa tana kallonsu sunna dariya suka fice dan yadda ta zaro ido irin kuma sai ki bani?

Shiru ya mata kamarma ya ajiye wayar, sai dai ita ta san bai ajiye din ba dan baya mata haka du fadan da zasu yi kuwa

Hanci ta ja wani hawayen ya bale mata a sanyaye ta ce"Ka yi hakuri dan Allah"

Wani irin tsinkewa gabansa ya yi ya fadi har sai da ya dakatar da rubuta code din bankinsa da yake yin transfer ya saurara yana sake tabatar da kamar kuka take yi kamar kuma mura take, sai dai to me zai sakata kuka ita ? KAUSAR fa mutun ce mai mugun hakuri da kuma juriya, har ga Allah shi yana girmama hakurinta da kawar da kanta a kan abubuwa da dama, kuma ya san dai fadansu ba shine zai saka ta yi kuka ba, shi yasa ya ce" Mura kike yi ne?"

KAUSAR ta dan yi jim, Sa kawai ta fashe masa da kuka har tana shasheka ta ce" TAUFEEK...... TAUFEEK ka gani ko?????"

Idannuwansa ya rintse a hankali ya idasa saka code din ya tura ya rufe computer sannan ya mike ya kashe kiran ya fito daga office din nasa yana lalubar aljihunsa dan jin inda ky dinsa yake ya nufi wajen dankareriyar jeep dinsa dake ajiye ya bude ya shiga yana dan lalubar gashinsa ya kunna sannan ya harbata kan titi

Silalewarya ta yi tana hawayenta, bayan ta yi tunanin gaba yake mata shima ta rintse ido tana tunanin to mema ta masa ai du laifinsa ne ta yi zuru zuru ta jiyo muryar Abansu yana fadin" Shiga mana TAUFEEK, ke Rukaya shinfida masa tabarma , nima ba zama zan ba zan koma nan na dawo"

Firgigit ta mike daga kwonciyar ta bi Rukaya da ido da ta fitar da tabarmar ta shinfidawa TAUFEEK wanda ya cire takalminsa ya zauna yana kunce agogonsa ya ajiye gefe kafin ya dago kansa ya zuba mata ido

Abinda da mai manyan idannuwa masha Allah idon yai mata zuru zuru ya yi ja , haka abin kwalin du ya zubo sai wani wiki wikitu take da idon tana kikiftawa shi kuwa yana sake kallonta har ta karaso tana kallon A'isha ta janyo masa ruwa a rijiya a zuba a tsaftatacen kwanon silba an ajiye masa

Habarta ta ringa sosawa a hankali murya shake ta ce" Da kana anguwar?"

Hannunta ya bi da kallo dake dauke da kunshi ja ya dan tabe baki ya ce" Ke kukan me kike, ke da waye?"

Kasa kasa ta yarda harara ta ce"

💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

*DA CIWO A ZUCIYATA*

💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

_MALLAKIN_

*SAJIDA NIJAR*

*FREE BOOK NE* 7️⃣

LITATAFAN MARUBUCIYAR

Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Neman na kaina
Bani da zabi
Bak'a ce
Kutkale
Makauniya ce
Mage
Duk nisan jifa
Idan ka raina inda kake
Dutse
Alkalamin kadarata
Bani da zabi
Dakika Biyar

Now

*Da CIWO A ZUCIYATA*

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes
Chapter 10 · 0% Book details