Sashe 27
Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kamar jira take yi ta daga kafarta da sauri ta karasa ta fada jikinsa tana sake rufe fuskarta a kirjinsa ta saki ajiyar zuciya bayananiya
A hankali ya mayar da dayan hannunsa ya rungumeta a jikinsa shima nasa idannuwan a lumshe
Kasa kasa sosai ya ce" Na fa yi dati zaki gogi dati a kwaliyarki mai kyau"
Idannuwanta ta sake lumshewa a hankali ta ja numfashi kadan tana jin kanshin turaran jikinsa mai sanyin kanshi na shiga hancinta kasa kasa ta ce" Bana jin wani dati, Ya Taufeek i'm so happy today "
Hannunsa ya saka ya dago fuskarta ya zuba mata ido
Ya yi murmushi a hankali ya kai lalausan lebensa saman goshinta ya mana mata kisss din da ya sakata sake lumshe ido
Kasa kasa ya ce" Ina maki barka da shigowa rayuwana Yumnah, Allah ya bamu zaman lafiya"
"Amen ya rab" ta amsa ita dinma, sannan ta sake zubawa sajensa ido kamar ta sake rukunkume shi haka take ji
A nutse ya ce" Bara na koma"
Ido ta bude da sauri tarr ta dora saman fuskarsa
Ya koma? Ina?
Kasa hakuri ta yi gannin da gaske yake ta ce" Ama ina zaka je ne da daren nan Yah Taufeek?"
Da kula sosai ya ce" Ba zan kwana a nan ba sai an gama bukukuwa irin na al'adun nan, you see da kunya na ringa tsalake mutane ina shigowa kuma ina fita"
Wani irin makoko da dana sannin barin wadincen rubda rubdan rubabun banzan kwanar mata a yau ya sake shake mata wuya, innalilahi tafia zai yi ? Du irin wankin kwakwaluwar da ta sha na irin kulawar da zata bashi daga yau har karshen rayuwarta dan kar ya dubi kowace irin mace haka zasu wani wargaza mata niya? Wace ta yi mata gyara ta yi mata wankin ido mai matukar girma domin mahaifiyarta ta nemi hakan, an sakarwa matar kudi na mamaki da ya saka ta zage dantse ta yi mata dala dala cewar sai ta ki jikinra ta sakar masa jiki ta yadda babu wata banza da zata shiga zuciyarsa sama da ita, har fada mata ta yi kar ta saki dan tana budurwa tace zata masa raki, komai wahalar da zata sha ta jure ta mike kamar ba ita ba, kuma ta yiwa kanta alkawarin jurewar sai kawai yace zai kwana ba a nan ba?
Tana ji tana gani, mijinta ya yi mata salama bayan ya dauko ledojin da ta ajiye ya damka mata cewar na baki ne sannan ya fice ya nufi bangarensa cikin nutsuwa
Nan ta zubar da ledojin ta karasa saman shinfidarta da aka yane da farin abin shinfida mai tsada aka baza turaran girma da kannanun flowers masu kanshi sai daukan ido suke ta hau ta kwonta tana rintse idannuwanta hawaye suka shiga bin gefen kuncinta cike da bacin rai ta kasa koda komawa inda suke bale har ta wani kai masu abin ledar cen, hasalima itama yinwar take ji, ama wannan abu da ta shaka ya sa ta ji ta hakura da jin yinwar, ama da bakin naci sai da Basira ta tardota har nan tana faman tsokanarta cewa angon ya fice ya masu sai da safe ita kuma ta makale ko zumar soyaya aka lasa mata? Ta fito mana,
Cike da rashin walwala ta nuna mata cewar ta gaji ne barci take son tabawa ga sakon nan ta je masu da shi inji shi, ita ta kwonta sai da safe
Da wannan ta yi kwonciyarta ta barsu da surutu tsakaninsu da baje bajajar suka auna a tumbinsu sannan suka kama wajen kwonciya dan hutawa
A nutse ya karasa bangarensa
Kamar yadda yake jin har wani mintsininsa datin jikinsa ke yi direct bayi ua wuce da babaan tawul dinsa a kafadarsa bayan ya cire rigar jikinsa
Ya dauki lokaci a ciki sosai kafin ya fito a nutse ya karasa wajen wrdrn dinsa ya ciro jalabiya ya saka sannan ya saka gajeran wando ya karasa wajen salaya dan gabatar da shaf'i da wuturi
Yana gamawa falo ya koma da laptop dinsa, da kuma wayarsa baba sai dan abin rufa da ya janyo domin niyarsa a cen zai yi barcinsa, dan dole sai ya duba laptop din ya yi yan aiyuka masu mahimmanci sannan ya kwonta
A lokacin da ya zo dan cin abinci kamar wayarsa ta fado cikin ransa
Tsam ya yi yana tunanin inda ya sakata, domin gaba daya ya manta da ita a cikin kwakwaluwarsa
Rigarsa da ya cire har ya ajiye saman mashine din wanki ya koma ya lalube, sai dai babu
A hankali hoton wayar a hannun KHausar ya shiga dawo masa idannuwansa
Idannuwansa ya lumshe ya koma falon sannan ya dauki wayarsa baba ya saka numbar sekatarinsa ya yi kiransa
A nutse ya sanar masa cewa kar a tura sakon komai a karamar wayarsa ta fice a hannunsa
Sakatarin ya sanar masa cewa ba'a rigai aka tura wani baban sako ba, wanda aka tura na marar lafiyar nan da aka dauko daga kauye ne kawai, ana iya nunin an bacewa lamba idan yana so?
Dan shiru ya yi, kafin ua girgiza kai yana fadin kar a ce komai, sannan ya kashe wayar ya karasa wajen cin abincinsa ua zauna dan cika kulunsa
______________________________________
Washe gari da wuri wuri Khausar ta shirya ta fice a gidansu bayan babanta ya bata dari biyuntata nufi cen wajen da ake kafa sunnayen wa'inda zasu iya zuwa su amshi takardunsu da wajen da zasu amsar
Sai dai tunda ta je din hankalinta ya nemi rikicewa sakamakon rashin gannin sunnan TAUFEEK a layin wa'inda aka tabatar cewa sun samu din bayan ga sunnan du wani wanda ta ji ance ya samu ciki harfa ita
Takardar nan ta mata karantawa ta fi a irga har sai da ta fara shanye sunnayen dake laye ta hakura ta juyo gida ido sai zubar da ruwa yake tana tafe tamkar zata tashi sama, uwa uba yau din hijab din Mama nema ta saka du irin kwaliyar da aka sha jiya kamar ba a fuskarta ba fuska tana neman sinkime mata dan shiga rudani da tunanin me kennan?
Tana shigowa a lokacin har karfe goma na safe ta gota ta nemi waje ta shiga rusawa Mama kuka kan ai Besty fa da alama bai samu ba, dan bata ga sunnansa ba
Itama Maman hankalinta ya tashi gaskiya, dan harma ta rasa to me kennan?
Aisha ce ta ringa kwatanta masu to ko dai an mance ne, ana samun irin haka fa kar su yi hahawar rikicewa, ama ina Khausar kaffafuwa baje a tsakar gida kukanta take kashirban da kyarma ta iya cin maka yar murden da Aisha ta silala tana faman bin Aishar kan ta zo ga dari biyunta nan ta siyo kati a kireshi
Mama ne ta hanna hakan, cewarta jiya fa yake ango, kar su kireshi bata so
A dole Khausar ta hakura da maganar kiran, sai dai nata sunna da ta gani gaba daya zumudinta da farin cikinta suke neman bacewa bat, abinda ya fi damunta in har bai samu ba fa yaya zai ji? Yaya zasu yi? Sam ta manta fushin da take yi da shi, burinta ta ganshi su je su sake dubawa su ga ta inda zasu bilowa al'amarin
Kusan karfe biyar na yama sunna zaune su uki a tsakar gidan ya shigo bakinsa dauke da salama
Mama ce ta fara amsawa fiskarta wadace da fara'a tana sake rufe jikinta da hijab dinta sosai tana masa maraba da zuwa
Dukawa yayi kamar yadda ya saba ya gaishe da Mama sannan ya yi zamansa saman tabarmar da Aisha ta sake kabewa ba wani kyankyami ko wani dari dari yana duban kwanon dake gaban Kausar tana dibar awara ta kudinta na safe ya mika hannu ya ja gabansa shima ya shiga ci hankali kwonce a lokacin da Mama kuwa ta mike ta yi ciki dan bata cika zama idan sunna nan ba, ba dan komai ba sai dan akoy yan matan, a tare da su baki daya
Khausar ta nemi sake dauko rikicewar fuskarta tana kallonsa ta ce" Wai freind daga ina kake? Ka kuwa san tunda safe nake nan ina sheka kuka ina nemanka?"
Kumatunta da suka dauki abin man awara ya bi da kallo, sai kuma ya tabe baki kasa kasa ya ce" Haka fa, gashi kina dirkar awarama "
Awarar ta kalla, ta kalli hannunta, sai kuma ta kalli Aisha ta ce" Aisha, dan Allah ban yi kuka ba?, Awarar nanma da ka gani ji na yi juwa zata makani da kas ne na yi hakuri nake ci, ama ni dake cikin tashin hankali, zuwa fa na yi ban ga sunnanka ba , ka san me hakan ke nufi ai ko?"
Cikin halin ko in kula ya ce" Eh"
Hakan ya sa ta zuba masa ido, wani abu na dan mintsininta a zuciya, EH? EH fa yace ko?
A dan yannayin fusata ta ce" Eh?, Wani irin eh? Hakan fa na nufin baka samu ba ko kuwa an cinye maka ne, dan ai da aka fada an fada ka samu ko?"
Banza ya mata, maimakunma ya bata amsa sai ky din mota da ya mikawa aisha ya umarceta kan ta dauko ambulop a motar
Jim kadan ta dawo Lhausar ta cika yadda ka san an saka mata balan balan a kumatun an hura sai hararensa take yi, shi kuwa har awarar tata ya kama sai cinyewa yake yi ko damuwar abinda ta fada bai nuna ba
Ambulop din ya yiwa Aisha nuni da ta bata
Tana budewa ta ga takardarta, watau diplomanta ta kwalin bama ta takardar ba, wace in kana son amsarta bayan ka yi takarda ka ajiye sai ka yi jira har Allah ya fitar maka da ita, dan kuwa kai tsaye ba zaka je ka amsa ba, Bama wannan na, a yau aka kafa masu cewar suna iya amsa, hakan na nufin daga gobe masu hanya zasu iya zuwa su samu ta takardar, ya su ya su kuwa sai sun bi layi har layinsu ya iso, sai takardar dake nunin an nata damar zuwa koyon aiki a babar hospitall din garin har na tsayin wata uku da albashi du karshen wata na kudin abin hawa da abinci