← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 116

Sashe 20

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

TAUFEEK dake kallon titi direba na tuka su shi da Alhhusain ya yi murmurshi ya sake zubawa hanyar ido har suka karaso yana jin rikicin amininsa da aminiyarsa ya amshe wayar a tausashe ya ce" Ki tabata na ganki in ba haka ba ina iya yin fushi KAUSAR"

Zata bashi amsa ya katse kiran yana kallon kiran YUMNAH dake shigowa

Murmushi ya yi ya ki dagawa saboda sun karaso gida ne ana ta busa ana hayaniya kala kala idan yace zai daga ba zata ji shi ba sai ya soke wayar a aljihun rigarsa ta ciki a nutse ya ringa shiga jama'a murmushi kwonce a saman fuskarsa yana cikin shiga irin ta danyan yadi mai laushin gaske, wanda laushinsa ne zai nuna maka karkonsa da kudinsa a ido, mai dan duhun haske ama ya dauki zubi madaidaici a babar rigar, sai hula nutsatsiya mai yannayi da suturar jikinsa

Daria take yi bayan ta kashe ta yi ido hudu da Aisha

Haba ta dafe ta ce" Wannan abin na idannuwanki bakya ji ya maki rumf A'isha? Innalilahi wannan ni a titi ai ba zan shedaki ba, uw awara jarumar indian film dai wannan hanci an sake janshi haka?"

Aisha ta saki murmushi itama ta ce" Aunty saura ke taso ki ga a maki mu tafi kar a cinye miyar kari fa"

Kausar ta mike tana cire katon hijabinta ta karasa tana sake kallon kitson yadda aka boye shi a bayan daurin dan kwalin kamar ba kari ba, sai dai yadda ya malalu ai mai hankali dai ya san ba gashin bahaushe bane

Tana kallon Usaina dake hada kalolin hoda dan ta fitar da kalar fuskarta ta ce" Ama Usaina ni ba zaki saka min abin karin ba ko? Ni dai gaskiya kin ga wannan katon ribom din nake so nawa yake shi? Ni karin gashin nan sam bana so"

Usaina ta yi murmushi ta ce" Aunty, tsaya mu gama sai mu ga in ribom din zaki fi jin dadi a jikinki sai a saka shi, shima ai yanada girma sosai kuma kasa kasaa muke saka shi sai dauri ya hau kansa ya zauna, ama shi daurin da ake masa simple ne irin na zahrah buhari dai haka"

Ita dai sarautar Allah ta zubawa ido aka ringa juya fuskarta nan a juyo nan, ama ta ki a saka mata abin saman ido mai kalolin nan, sai dai sun ci karfimta gashin ido sai da suka saka mata madaidaici daidai da yannayin fuskarta, haka kuma jan bakin Nude ne aka saka mata ba mai karfi bane kuma ba'a yi mata barbada kumatu ba, kwaliyarta dai simple ce, kwalin nema ya so tsayar da su domin da kyar idon ya daina hawaye aka diga mata abin wanke cikin ido idon ya yi haske sosai sannan ta mike ta dauki nata lesh din itama ta zagaya baya dan sakawa domin sai ta saka za'a daura mata dan kwali

Hankali tashe ta yaye labulen dake karewa ta ce"
💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

*DA CIWO A ZUCIYATA*

💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

_MALLAKIN_

*SAJIDA NIJAR*

*FREE BOOK NE* 1️⃣2️⃣

LITATAFAN MARUBUCIYAR

Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Neman na kaina
Bani da zabi
Bak'a ce
Kutkale
Makauniya ce
Mage
Duk nisan jifa
Idan ka raina inda kake
Dutse
Alkalamin kadarata
Bani da zabi
Dakika Biyar

Now

*Da CIWO A ZUCIYATA*

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata💃💃💃💃💃

Hankali tashe ta yaye labulen dake kare mai saka kaya ta fito tana fadin" A'isha wannan rigar fa? Ji fa yadda ta min daga nan?" Ta fadi nan din tana nuna wajen cinyoyinta irin yadda rigar ta dameta ta fitar da yannayin kirar jikinta

Ido da baki da hanci Usaina ta saki tana mamakin Kausar, kai subahanalah, da haka yannayin jikinta yake take fama da zumbulelen hijab kamar zata kifa? Haka yannayinta yake yanzunma ta zo da wata riga ne bubu zumbuleliya wace bata kama ko'ina na jikinta ba sai yawo take a ciki ashe ashe abinda ke kasa kennan? Su sunna yiwa Aisha kallon masha Allah mai manyan mazauna ashe ga wace tace kau bani waje, eh lalle Kausar tanada tumbi wanda da ace bayanta ba pankameme bane haka da tsaf zai iya zamewa matsala a kwaliyarta, sai dai yanzun haka kadan ne ake ganninsa sakamakon yannayin halitar da Allah ya yi mata, sosai suka taimaka suka rufe mata yannayin tumbinta saima su da suke bugon idannuwa

Nan fa aka shiga rikici, domin firr ta ja ta tsaya kan ba zata saka rigar nan ba, sai dai bata sani ba tsiya ce kannen nata suka shirya mata domin kaf kayan lesh din shine dama dama wanda ya dan rufe mata sutura

Tamkar zata yi kuka haka take sake maimaicin ba inda zata iya fita a haka, ba zata iya ba

Gannin rikicin na gaske ne Usaina ta je ta dauko wata alkyabarta baka mai shara shara, shara shara ne da ita sosai alkyabar dan yan mata ke yawan sakata sai yan gayun matan aure , itama irin shigarta kennan , Alkhyabar ba wani abu da take boyewa sai dai ta dan kare dai , sunna ne domin gwarama mayafi da ita , nan ta dawo tana budewa ta ce" Aunty, kin ga wannan alkyabar sabuwa ce sau daya tak na sakata in har zaki iya sakawa mu gama daurin ki saka ki ga zata rufe fa"

Kausar dake zaune ta harde hannu ta gama kutuntumawa Aisha da rukaya ashar sai huci take kan bafa zasu fitar da ita tsirara ba jiki a sanyaye ta ce" Usaina ni da a je a daukon sabon hijabina na sallah da muka yi sai na rufa, yaya zna rabaki da kayanki kumaa bayan wannan nauyi da muka dora maki?"

Usainar ta ce" Lah, aunty walahi ba wani maganar nauyi, kuma ba maganar aro tsakaninmu, kin ganta in dai zaki saka din ni zan ji dadi, yanzu yaushe aka koma aka dauko maki hijab aka dawo inace yanzu Mama ta gama fadan baku karaso ba?"

Shiru ta yi, du nauyi ya damu zuciyarta, haka aka daura mata daurin da ya idasa fitar da sirrin kwaliyar sannan ta saka alkyabar wace ita da kanta sai ta tsaya gaban madubin a hankali tana shafa yan kannanun walwalin gaban alkyabar farare karkar ba masu yawa ba tana gannin yadda alkyabar ta hau yannayin dinkin har kasa da irin yadda kwaliyar ta hau kalar fatarta tamkar ba ita ba

A hankali ta daga idannuwanta ta kalli kannenta da suka sakata a tsakiya sunna kallon madubin su dukansu

Wani ni'imtacen murmushi ne ya kwace mata a fuskarta a hankali ta ce" tabarikalah masha Allah"

Aisha ta saki murmushin itama a hankali ta ce" Tsarki ya tabaka ga ubangijin da ya halici samai da kasai da dukan halitun ciki, Aunty kwaliya tana maki kyau sosai haka dama?"

Rukaya ta yi murmushi itama a hankali ta ce" Tamkar ba aunty ba, kalli yadda ta yi? Inama Elhaji ya ga kwaliyar nan na tabata yau zai ce a daura aurenku"

Da yar dariya ta mintsini hannun Rukaya sannan suka juyo Usaina ta ringa kashe masu hotunna sunna faman fadin ta ajiye masu zasu zo su amsa a wanke a fitar masu tunda babu mai babar waya a cikinsu

Sai bayan sha biyu na rana suka fito daga gidan kwaliyar suka shiga adaidaita wace Rukaya da kyar ta samu waje dan wajen matse masu yake sai sun jijirga suk dauki hanyar gidan su TAUFEEK da akwatinsu

Sunna karasawa suka tarar gidan dinke da al'uma, babu kalar da babu tun daga tsofafi har zuwa yara kannana, kai yan matan dake gidan tamkar gida mai yan mata bayan yan matan gidan basu wani girma ba, yan matan cikin gidan ne dangi ne da ango dinsu na safe, sai dai ba irin lesh din su KAUSAR ba domin wannan su Mama ne suka yi shi iri guda sai makusantanta da ta ba ita da kanta, lesh ne mai daraja da tsadar gaske hakan ya sa har suka karasa bangaren Maman akan bisu da kallo ne ga tsararen kwaliyarsu ga lesh din jikinsu sai a yi tunanin wasu makusanta ne wa Hajia watau mahaifiyar TAUFEEK din

yinin biki kawai ake yi ba ji ba gani, biki irin na manya masu hannu da shunni

Kokarin dukawa take yi dan gaisar da Mama da ta nufota tana murmushi hakoran makarta biyu na walwali ta saka hannayenta ta tareta tana fadin" Oyoyo yarinyata, koda yake fada ya dace na rufe ki da shi, ama ba yanzu ba sai mun salami baki zan maki tass a gidan nan, zo maza ga abincin TAUFEEK dauki yana bangaren Hajia dan Allah kai masa ki dawo ku je da yan uwanki bangaren cen na amarya ku kai na baki ance zasu iso su yi gyaran dakinta dan yau za'a kawota"
Chapter 20 · 0% Book details