← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 116

Sashe 35

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A lokacin da Aba ya shiga daki sosai ya nunawa Mama damuwarsa da damuwar yarsa, Mama ta bashi baki cewar idan aka jure yanzu abin zai wuce, dama aikin asibiti aiki ne mai girman gaske, dole za'a sha wahala idan ba'a saba ba, ama a hankali komai zai daidaita

Numfashi ya fitar zuciyarsa na masa wani kaikayi,, abin ke sukarsa har kamar zai amayar ya sanarwa mahaifiyarsu ama kuma ya rike a ransa
A maganar Khausar maganar Mujaheed ta matukar daga masa hankali
Anya akoy zaren mutunci a yarensa kuwa
Shi zai fitar da su daga gidan nan ya kaisu wani, da ta bashi dama da tana hawa motar kanta?
Me kennan?

Gaba daya sai zuciyarsa ke son gannin haka a matsayin cin fuska ko sharar fage dan ya kangarar da zuciyar yarinyarsa, idan har mai kwadayi ce maganarsa na iya sakata yiwa abin wata fahimta daban, shi bama maganar rabuwarta da TAUFEEK ya tsaye masa a rai ba, dan ya san dama idan har ta yi aure ba kowanu namiji bane zai iya hakurin mu'amalar nan, kuma summa ai yana gannin hakan ba zai iya zama matsala a tsakaninsu ba, abinda yake iya yiwa hasashen na iya zama matsala a lamarin nan wani taku da ya hango wanda da wahala ya iya jurewa, watau wulakanci
Eh lalle shi talaka ne
Kuma yana zaune a anguwar talakawa, yana cin cimar talakawa
Ama hakan ba zai ba kowa damar wulakantashi ko wulakanta masa ya'ya ba
Bai je ya roka a wajen kowa ba
Bai je ya yiwa kowa maula ba dan ya san ba mutun ne zai bashi ba sai Allah
Bai wulakantar da kansa ba ko a anguwa bale a kasuwa uwa uba a gaban sirikai
Ba zai lamunci komai mai kama da cin mutunci ba
Shi yasa ko maganar auren su Aisha da aka saka ranar amsar sadaki da kaya nan da kwanaki goma sha biyu bai zurma ya yarda aka ringa ba ya'yansa abinda ya shafi kudi ko abinda ya fi karfinsa ba, ko sun amsa a rashin sanninsa ne, baya yarda baya bada kofar nan, dan ya san babu wanda ya iya rikita zuciya irin dan Adam, saima ya nuna maka duniya kaine ya yi tsaye ya watsaka

Ajiyar zuciya ya sauke bayan ya kai hakarkarinsa ya kwontar, a ransa ya gana yanke hukuncin sai dai Allah ya ba Mujaheed hakuri, domin ba zai dawo kan maganarsa ba gaskiya, ba zai gaba yarjewa Khausar amsar abin hannunsa ba, ba kuma zai masa maganar ba shiruma magana ce zai gani ne a aiyukansa cewa bashi da abinda zai basu ya ciresu a talaucin da yake gannin sunna ciki!

___________________________________

Du irin yadda ya so ta sasauta yannayin tsoron da take ciki nasa abin ya faskara
Dan murmushi ya yi yana kallonta, ta yi jajajir kamar an konata da ruwan zafi, sai hadiyar zuciya take yi tana sisine kai dan kawai yace sai ta ci abinci ya dubata kafin ta kwonta, haka ta wuni a kwonce waje guda danma ya wuni wajenta ya mata dukkan taimakon da ya dace domin har karin ruwa ya jona mata ya san jikinta ba maganar ciwo a yanzu sai dai ko ta saka tsoro a ranta ne bayan shi ya san a haka din ya yi iya yinsa dan kiyaye sakata a halin tsoron, ta so ta fi karfin tunaninsa ne har ta saka shi aikata haka domin bai yi niya da wuri haka su saje ba, sai gashi abu ya faru tsakaninsu a lokacin da bai shirya din bA

A hankali ya mike daga zaunen da yake ya mika mata hannu ya ce" Taso mana, wai ko ban duba da kyai bane kar aje kin karu, mu gani?"

Gabanta ya sake faduwa, curewa ta sake yi waje guda a saman gadon tana rintse ido tana jin tsoron kar fatarsu ta sake haduwa ta ji azabar da ta ji a yau
Bafa kokari ne bata yu ba, ta yi kokari fiye da tunanin bawa, abin ne ya girmami rashin hankalinta, ta yi dana sani da ta matse masa waje, ashe sanyin halinsa na macijin kumba ne sari ka noke? Ashe shi din wuta ne mai zafin gaske? Ashe hasashe ne take yi da akace da ya gama ta mike ta murje kamar ba'a yi ba? Gashi dai an yin an gama ama ta kasa mikewarma bale har ta murje kamar ba'a yi ba in ba dan an turo mata wace ta sake tayata kimtsa kanta ba da bata san yaya zata iya koda cin abinci bane

Da rarashi da komai ya bata kula daidai gwargwadon iyawarsa har ta samu barci

Murmushi ya yi yana dauke dubansa a kanta , tunani yake na lamarin rayuwa
Shi dama ya san a yanzu da take bakuwar lamarin ya fi karfin halitarta, sai dai mace rijiya ce ya san du wahala zata jure kuma du irrin abinda zata nuna a sannu zata saba
Shi likita ne baba ya san dalilin da ya sa ake so a bi mace a hankali har hankalintaa ya dauka

Murmushi ya sake yi ya karrasa saman salaya, ya shiga gabatar da ibadaraa cikin nutsuwa,
Sai kusan biyun dare ya kwonta, dan zai yi fitar wuri ne zuwa wajen aiki ga kuma kasuwa Aba ya fara maganar yana son sakar masa aiki shi kadai

_________________________________

Tunda sasafe ta shirya, Yau Aba ne tsaye kanta da zazafe tana turawa yana karra fadin ta karra ko kadan ne, abin har tausayi yake ba Mama idan tana kallonsu, soyayar Khausar da mahaifinta daban take kuma a bayane take

Tana gamawa ta sake yin bruch ta kuma shan panadol dan ciwon kan ya ragu ama bai daina ba gaba daya

A cikin hijaban da suka sha mamakin yawansu ya dauki daya ta saka a jakar da Aisha ta bata

Sosai Mama da yan uwanta ke karfafa mata gwuiwa sukai masu rakiya har bakin kofa

A kafa suka taka da Aba, sunna tafe Aba na ta yakin cire mata du wani kyankyami ko tsoro a ranta, yana nuna mata romon abin da sauransu har suka isa bakin likitar sannan ya bata dari biyar dinta cewar ta cin abinci ce
Haka dai ta rabu da Aba kamar an kawo yaro karami makaranta ranar farko tana ji tamkar ta bi shi da gudu ta su komawarsu gida

Haka ta saje ta ringa aiki tamkar ba gobe har kusan sha biyu mai gadi ya miko mata abinci cewar inji Abanta a nan ta kula ba abinci bane basa ci cin ne a tsaitsaye ba a nutse ba saboda aiki,kuma gannin jinni ko wani abin baya hanna su ci , sukan ci ne su ci gaba da aiki
A ranarma sai dare aka salameta ta nufi gida ta kuma tarda wani rikicin sabo na Mujaheed domin sai ya nuna ta ajiye wannan aiki zai sama mata clinik tunda bata da lokacinsa, karshema ya nuna shi faa gidansa bama zai iya barinta aiki ba, ita daita bashi hakuri sosai ta lalabashi suka rabu lafiya

A hankali kwanaki ke ja, har lokacin taron amsar sadakin Kannenta ya zo,ranar da ta yi iya yinta dan hanna kanta kuka, ba dan komai ba sai dan magangannu da ta ringa tsinta kala kala masu firgita zuciya da rikita tunanin bawa da saka bawa saka kansa a mugun tunani marar anfani

Kasancewar yan matan anguwa da na makaranta sun taru , ga tsofafin anguwa da datawa, kowa albarkacin bakinsa yake fada har zaman ya nemi gagararta a cikin mutane sai samun hanya ta yi ta fice a gidan ta nufi asibiti bisa umarnin Mama da itama tata zuciyar ta cinkushe gannin yannayin na khausar, bayan idan an tambaya ana fadawa mutane cewa tanada manemi magana ne bai yi ba a gaba, ama sai an bita da magangannu gasunan dai mararsa dadi

Tana zuwa ta samu doctoe Rauda ta kama mata aiki, a yanzu an fara bata dama irin ta saka allura da cirewa, wanke kurji da sauransu, haka kuma ta fara samun dama irin ta sakewa a cikinsu

Da wuri ta fito yau dan kiran da TAUFEEK ya mata cewar sunna gidan

A lokacin da ta karaso ta tardo ya zo daukan Hajia ne tare da matarsa, nan suka gaisa da Yumnah sama sama dai , ama ita sam bata gane ba dan hankalinta ba a nan yake ba a tunani yake wanda ke neman hanna mata sukuni

Sunna fitowa suka shiga mota TAUFEEK ya dawo ya dan zuba mata ido, du ta zube , kana ganninta kaa san ba jikinta bane , gashi yau harta lebenta a bushe yake kamas tsabar tunani da takura rai

A sanyaye ya ce"

*ALLAH BAI SAUKAR DA CIWO BA SAI DA YA SAUKAR DA MAGANINSA*

Ni ce dai Fareeda Abdallah, na sake dawo muku da tallen magungunanmu da zuwa yanzu bazan iya ƙayyade yawan waɗanda suka dace da biyan buƙata sanadiyyar amfani da maganinmu ba. Alhamdulillah! Ƴar'uwa ki gwada, wataƙila warakarki na tattare da maganinmu.
Haihuwa ce baki taɓa yi ba ko kuwa jinkiri kike samu sanadiyyar planning ko kuma haka kawai? Muna da ingantaccen maganin rashin haihuwa ga mace da namiji, wanda za ki bada sadakar 2k ga matsalar ko wane ɓangare. In sha Allah za ki dawo da godiyarki bayan amfani da maganinmu.
Sanyi (infection) ne yayi miki yawa yake saka ki ciwon mara, zubar farin ruwa, ƙaiƙayi, ƙuraje, ɗauke ni'ima, har ma ya saka mijinki ya dinga miki gani-gani saboda bakya gamsar da shi? Da naira 3k zamu haɗa miki magungunan da za kisha ke da Oga in dai kika yi amfani da su ku da sanyi har abada in Allah ya yarda.
Muna sayar da ingantaccen haɗin sabaya, wanda zai sa nonuwanki su cicciko, hatta fatar jikinki sai ta murje sanadiyyar shan kunun sabayarmu. 2500 bokiti 1litter.
Muna da maganin wankin nono ga mai ciki da mai shayarwa, wanda indai kikai amfani da shi yaronki zaiyi tubarakallah, ba ruwanki da laulayi. Muna da ingantaccen maganin Daji (Cancer), typhoid, maleria, yaron da yayi nauyin ƙafa, da sauran cututtukan da ban ambata ba.
Muna aika maganinmu ko ina tsakanin Nijar da Nigeria, ga masu buƙatar magani da gaske su tuntuɓeni akan lambar wayata 07039080978, ko 09077591726
Chapter 35 · 0% Book details