← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 116

Sashe 16

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da kyar ta sauke shi tana fadin" Menene a ciki?"

TAUFEEK ya miko mata katuwar ambulop din katinta ya ce" KAUSAR daga wannan aikar kar ki kuma sakani wata kin fahimta?"

Murmushi ta yi ta ce" An gama Yalabai, ama maganar dinkunnanka na wajen abashe ya yi kirana jiya baka leka ba ashe, sai kuma maganar wunin da muka yi da kai da kuma wankan ango da Mama tace a gidan su Uncle Abdallah za'a yi?"

Yana yiwa motar ky ya kunna ya ce" Zamu yi waya idan na koma gida ki gaishe min da Mamanaa please "

Hannu ta daga tana masu byby ta ce" YUMNAH na san sai ranar ko na kuma ganninki, sai mun je daukoki"

YUMNAH dake hadiye wani makuku mai taurin tsiya da daci a wuyanta cike da takaici ta dan saki murmushin yake tana sake bin kofar gidan su Kausar din da kallo wanda a ranta take ayana ita ko kasheta za'a yi ba zata iya zaman minti daya a gidan nan ba , ama a cikinsa aka haifi rundumemiyar yarinyar nan da take neman hanna mata sukuni da kwonciyar hankali? Subahanalah wannan wace irin masifa ce?

Sun koro da tafia cikin yannayi da dabara irin tamu ta mata ta ce" Sir, masha Allah gidan su Aunty Kausar ana samun baki, wanda ya fito ta yiwu uncle dinsu ne ko?"

Yana tukinsa normal, a fuskarsa ba wani yannayi haka a yannayin motsin gabansa bayan ya tsayawa danja ya ce" Aa ba uncle dinta bane, Saurayinta ne Baki gane shi ba?"

Cike da mamakin furucinsa da yannayinsa ta ce" Saurayi? Dama tanada saurayi?"

Da dan mamakin yannayin tambayarta ya dubeta, sai kuma ya tayyar da motar ya bi ayarin motocin da suka yi gaba bayan danjar ta saki suka dauki hanyar gidansu dake kusa da wajen danjar

Bai jima ba ya karasa kofar ya tsayar da motar a nutse ya kasheta sannan ya dan juyo ya zuba mata ido ƙadan

Da kula sosai ya ce" YUMNAH na gode da ziyara"

Murmushi ta yi tana dan sake kallon tsararen sajen fuskarsa da yannayin askin kansa mai fitar da fasalin fuska da tsarinta, sai kalar shadar jikinsa mai ruwan Ash color mai haske da ta dauki zare ashe mai duhu dinkin dan kadan ba wani da yawa ba

A hankali ya dora da fadin" But daga yau, bana so kina fita, ko ina ne kin fahimta?"

YUMNAH ta dan tsatsare fuskarsa da kallo, a hankali ta ce" Dama ba inda zan je Sir, sai wajen gyaran jiki kawai"

Dan kureta ya yi da duban da ya sakata jin ta dan tsargu, sai kuma ya dauke kansa yana kallon gefe a hankali ya ce" ita mai gyaran ta zo gidan ta maki YUMNAH"

YUMNAH ta dan zarro ido ta ce" idan gida ne fa akoy mugun tsada ne "

Da mamaki ya dan mata kallon kai? Tsada? Shi zata kawowa maganar tsada? Tsada ta kai maganar mutuncinta da yake son fara karewa daga yau har karshen rayuwarsa? Tsadar me da zata kamo shi nashi kwonciyar hankalin? Baya tunanin in har zai iya hakuri shi TAUFEEK iyalinsa a waje da shigar da ba ita ba kowani shara na kallo da sunna ta tafi gyaran jiki

A hankali ya ce" Kina iya fita"

Fuskarsa ta tsatsare da ido, da dan sauri ta ce" Zan fa yi a gidan, ba zan tafi wajen gyaran ba"

Motar ya kunna yana dan dage kafadunsa kadan , hakan ya sa ta kama marfin motar ta ce" Zamu yi waya da dare ne?"

A hankali ya dan duba agogon hannunsa, ya tabata idan ya fito dare ya yi sosai, sai kawai ya dubeta da kula ya ce" Aa, ki yi kwonciyarki, zan kirayeki da safe in sha Allah"

A hankali ta sake kureshi da duba, a zuciyarta kuwa tana ayyana ' Kennan ni ba zaka kirayeni ba dan zaka kirayeta?, Me sunnata ne wannan mata a duniyata ko nace a rayuwata?'

Budewar ta yi ta fice ta shige cikin gidansu

Tana nufar falonsu mesage na shigowa wayarta, sai ta ki dagawa tana sake kasa kunne dan gaskata idan har muryar yayarta ne
💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

*DA CIWO A ZUCIYATA*

💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

_MALLAKIN_

*SAJIDA NIJAR*

*FREE BOOK NE* 🔟

LITATAFAN MARUBUCIYAR

Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Neman na kaina
Bani da zabi
Bak'a ce
Kutkale
Makauniya ce
Mage
Duk nisan jifa
Idan ka raina inda kake
Dutse
Alkalamin kadarata
Bani da zabi
Dakika Biyar

Now

*Da CIWO A ZUCIYATA*

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata💃💃💃💃💃

Da sauri ta daga kafarta ta idasa shiga tana bude sakon bankinta dake sanar mata shigowar makudan kudi na mamaki da ta tabata daga angonta ne, kuma kudin ba na komai bane sai na gyara Wa'inda in har gyaran zata yi ko amare ashirin ne ya ishe su tsaf harda suturun wunin biki da komai komai tsadar abin kuwa bale ita daya, sai dai maimakun ya mata dadi sai ta ji sam bata jin wani dadi ko zumudin abin har ta karasa ta zauna gefen yayarta dake wake ga amarya yar dangi ga amarya YUMNAH tana tafi da murmushi na farin ciki

Yannayin YUMNAH ya sakata rage zumudinta tana kallonta sai kuma ta kalli mai aiki dake ajiye masu ruwa ta salameta ta ce" Ke lafiyarki kuwa ? Yannayinki ya nuna kina cikin wani bacin rai?"

YUMNAH ta zubawa fuskar yayarta ido, a hankali hawayen dake makale mata suka samu damar zubowa , sai kuma ta fashe da kuka ta mike ta karasa ta fada jikin yayar tata , tana kukan sosai ta ce" Aunty, kun zo?, Sannunki da zuwa....."

Hankalin yayarta a tashe ta dagota daga jikinta tana jan hijabin dake jikinta ta ce" Subahanalah ke kuka kuma? Menene? Subahanalah lafia? Me ya faru a gidan sirikan naki? Mama tace kin je masu barka da sallah har ina cewa me yasa kika fita yanzun fa kuma ba maganar fita in ba dole ba?"

Tana kukan tana kallon auntyn nata, duda ta san yawancin lokuta yayar tasu ta kasance daban a yannayin halaya, domin wani lokacin harta da mamansu kwasa suke yi, bama a kan maganar saka hijab da sauransu in dai ta zo gari to fa sai an kwasa da ita kamar ba wace ke rayuwar turai ba haka zata ringa fadan a suturce jiki da sauransu dai abubuwa dai irin na tsauri
Tana hawayen wani na korar wani ta ce" Aunty, TAUFEEK ne, Aunty lamarinsa ya fara damuna, abubuwan da nake gani sun fara tsoratar da ni, tun yanzu ina tsoron nan gaba ya zamo irin mazan nan masu kara aure, watau ya kasa hakuri da ni daya kwal a matsayin matar aurensa!"

Kallonta take yi, bata katseta ba, tana kuma jira ta ji baban abinda ya sa kanwar tata ke kuka haka, dan kuwa ta tabata ba wannan kawai bane....domin in har wannan ne bata san me zata kirayi YUMNAH da shi ba,
Sai dai ga mamakinta YUMNAH ta ja ta tsayar da maganarta tana ta shashekar kuka

Fauziya ta ce" Ki daina kukan haka mana ki fada min menene wai damuwar? Dan na san ai ba zaki kasance mace mai irin ra'ayin nan ba, ko nace mai son sakawa kanta ciwo a banza da wofi ba, ina nufin yau mace komai kankantar shekarunta in dai ta fara amsa bayanan soyaya daga namiji in tana da hankali ai Auta ta san cewa ba'a halitoshi dominta ita kadai ba, bale kasancewarta musulma kuma y'ar hausa? Koda a gidanku ba'a yi ba kin gani a makota, menene zai dameki da irin tunanin nan tun yanzu salon ki kasa kula da kanki da maganar aurenki tun da jan sawunki a kan shirme? Ko kuwa maganarki da shi dama shi baya sonki kece ke sonsa zaki kai kanki inda za'a gaza hakuri da yarintarki a ringa maki uzuri? Ke Auta Allah na tuba ke da kika dauko dan kasuwa ai kin san ba dai a kan maganar mace zaki kawowa kanki damuwa ba ko????"

Kukanta ba wani dainawa ta yi ba, saima ji da ta yi kamar damuwar ta karru a kan da
Chapter 16 · 0% Book details