← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 116

Sashe 40

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata💃💃💃💃💃

Da dan Mamaki Khausar ta juyo dan gannin ko dai bata jita bane?, Sai ta ga aikinta take yi bata kuma bi ta kanta ba

Da wani mamakin ta dan sake dubanta, sai ta dan koma baya ta sake yin salama wannan karron da dan karfi

Sai dai abin mamaki bata ajiye maganarta ba ta ga Yumnah ta yi wani ecpression da fuskarta sannan ta dan ja tsakin da sarai ta ji shi ta saki abin zuba abincin dake hannunta ta juyo tana cire safar hannun nata ta dangwarar a nan da wani yannayi irin na wulakancin nan dake bayane ba a boye ba ta ce" Na ji ki, ban san inda yake bane"

Daga haka ta juya da saurin tafiya ta koma kicin

Baki da hanci ke bude Khausar ta rakata da kallo har bata ji takun saukowarsa ba sai muryarsa da ta ji ya ambaci sunnanta yana idasa saukowa da mamakin ganninta dashe a nan baki bude

A dan tsorace ta juyo da madaukakakin mamakin da bai barta ba ta zuba masa ido, sai kuma ta dauke dubanta a kansa na tsarewa da kallo, domin farar riga ce a jikinsa ama botiranta a bale sai ash color din snglt a ciki mai siraran hannu , hakan ya dan bayana wasu sashe na sirrin jikinsa wanda bata taba ganni haka kai tsaye ba

Hannunta na dama ta saka tana dan murza goshinta cike da shiga rudu da kuma yar kunyar yannayinsa ta dan juya ta ce" Am, barka da yanzu, dama ina kiranka ne baka daga ba sai na zo , Mujaheed ne ke cen kofa nake so idan ba damuwa a shigo da shi ko a fada masu na leka ......???"

Ta idasa maganar tana dan ajiye zancen da dan sake duban hanyar kicin din nan

"Ok" kadai ta iya ji daga bakinsa, sai kuma ta ji yana magana da waya cewar a bar bako ya shigo a nan kofar gidan

A hankali ta dan juyo dan yi masa salama, sai ta ga ya bala boturan, hakan ya sa ta samu sakewa ta dan dube shi ta bi wayar dake hannunsa da kallo, wace ta tabata itace mai dauke da numbar da ta yi ta kira tun dazun bai daga ba, ta so kwari yi masa korafin hakan, sai dai wani abu da ya dan tsaye mata a kahin zuci na yannayin da matarsa ta yi yanzun ya dauke hankalinta, a hankali ta juya ta ce" Thank you" sannan ta yi waje

Kansa ya mayar a zaunen da yake jikin kujerar ya lumshe idnanuwansa

Shin ta ina zai bi ya raba wannan alaka? Barin wannan alaka dan ta ji dadi anya daidai ne?
Idan ya yi duba da tarin abinda ya sani shi a kan manemin auren aminiyarsa kuma kanwarsa in ya yi shiru ya yi mata adalci daga ita har iyayenta kuwa? Shi dai ba abikin yin Mujaheed bane, abinda ke iya sab hanyarsa da tasa daya ce tak idan shagonsu na son sari a kampani, bayan wannan babu ta inda wani abu zai iya hada su, da ya dan kwatanta ganninsa sun zanta a kan lamarin......, A gaskiya baya tunanin in har zai iya yin hakuri ya zuba ido KHAUSAR ta auri mutun irin wannan bayan du irin wahalar da ta sha ta rayuwa a kan wannan subjet na mijin aure ba
Kwata kwata shi din ba mijin mace irinta bane
Ba dan aljihunsa ba ko yannayinsa ba, sai dan Halayarsa da suke boye wajen yan mata ama suke bayane wajen wa'inda suke iya sani

"Honey, na kawo abincin nan ne?" Yumnah ta katse tunaninsa da sanyayar muryarta da yannayi irin na macen dake gabar son birge abin birgewarta

Idannuwansa ya lumshe a kanta , sai kuma ya mike yana dubanta ya ce" Ina zuwa Yumnah"
Daga haka ya nufi hanyar fita a falon

Da ido ta bi shi, kirjinta na dokawa da tunanin ta yiwu wancen abar zai bi?
A hankali ta silale saman kujera ta dafe gaban goshinta da hannayenta bibiyu tana tunani, tunani take yi anya kuwa tana cikin hanyyar da zata kubuta daga wannan mugun abin dake faruwa a aurenta? Duka duka yaushe aka yi auren ama ita ta hadu da kalubalan zaman auren fiye da tunanin mai karatu, babu lokaci idan wannan mata ta nemi layin mijinta yana iya amsawa, babu lokaci idan ka ganshi kana iya ganninsu tare, ba dangin iya ba na Aba an kwaso katuwar mace an kawo gidan da mijinta yake da ta dan nuna sai ya nuna tamkar yar uwarsa yake kallonta? Anya ba zata yi tashi irin na kirki dan gannin ta samarwa kanta mafita daga wannan abin ba? .....da wannan bacin ran ta yi zamanta a nan tana neman mafita da tunaninta

Fitar da ya yi shi kuwa bangaren iyayensa ya nufa , domin tunda ya zo bai shiga ba, ashe rabon ya tarda abinda yake faruwa ne, rikici tsakanin iyayen nasu , Hajia na zaune tana ta kashe wuta tana fada domin mahaifinsa baya nan

A hankali ya fice a falon, ba dan komai ba sai dan gannin halin da suke ciki, ya tabata in dai yace zai zauna to yana iya haduwa da bacin ran da zai saka ya kasa hakuri
Sometimes, yakan ji kamar ya dauki mahaifiyarsa ya kaita nesa da wannan rayuwa, ama idan sun kadaice sai ta ringa kwatanta masa cewa wannan din ba damuwarsa bane tsakaninta ne da matan mahaifinsa, ya barta zata iya kwatar kanta tunda ita ba yarinya bace, kuma zaman aure take yi dole zatana haduwa da kalubale na yau da gobe, shi dai ya ci gaba da addu'a ya kuma kiyaye huldarsa ta yai da gobe da kowama

A bangaren Khausar

Tunda ta shiga motar bayan ya nuna mata cewa in bata shigo ba a ina zasu zanta? Duba da bata kawo masa kujera ba kuma bai ga wajen zama ba, kanta ke kasa tana sauraron irin tarin mitar dake bakinsa da kuma rikicin dake cikin bakinsa

Gaba daya rigimarsa idan ya jema ya dawo a kan TAUFEEK take sauka, hakan sai yake bata mamaki, ama ta nutsar da tunanintaa tunawa da wasu kalaman da ta ringa haduwa da su cewa dole fa zata iya haduwa da haka, ba kowaki namiji bane zai yi hakuri da mu'amala irin wannan dan haka a sanyaye yau ta budi baki bayan ta dago ta masa duba kamar sau biyu ta ce" Na san ba zaka taba yarda cewa mu'amalata da TAUFEEK zumunci ne kawai ba Elhaji, ka sani zumuncina da shi ya hada zumunci da iyayenmu, ko yanzu da ka ganni a gidansu Hajia ce ta zo da ni, a bangarenta nake kwana ina tashi, bayan wannan Elhaji maganar mu'amalata da TAUFEEK a yanzu da nake budurwa take da karfi, idan na yi aure du abinda mijina ya shinfida min ai dole zan yi biyaya in dai hakan bai sabawa adinina ba, dan Allah ka yi hakuri ka cire wannan magana daga ranka kwata kwata"

Har ga Allah, bai taba jin salama a maganarsu kan TAUFEEK ba irin nna furucinta na yau, ko dan ya kasance mutun mai son a girmama shi? A yanzu yana jin zai iya tunakarar wannan masifafiyar matar da ya kakabowa kansa take neman hanna masa rawar gaban hantsi, mace sai fitina, mace sai neman fitina, yanzu abinda ya fi jin tsoro maganar nan, da ya kwatanta ashariyar da ta dura a kan yarsa sai da cikinsa ya juya, ama abu daya ya sani ita din mayar kudi ce, zai kwatanta lasa mata zuma ya san da wahala ta iya kin amincewa da maganar auren nan, shi fa har mafarkin Khausar yake gashi ga ita matsayin matar aure, kuma ya tabata da wahala matarsa ta fi karfin Khausar dan kuwa in me take takama a jikinta Khausar ta damata ta shanye

"Mun yi magana da Aba, Aba ya nunan bacin ransa dan na je jiya da jus, yace baya son haka kar na kuma, sannan ya min maganar na fito idan da gaske nake" Ya fada yana dubanta

Khausar ta dan dago ta dubeshi sau daya ta sake dauke dubanta a kansa, a ranta tana tunanin yauwa ga abinda ya hasala Aba, dan ya masa magana ba sau daya ba, ba sau biyu ba, ama shi kamar baya jin me ake nufi da kar ya yi

Ya dan sake muzgutawa irin rikakun mazan nan da suka isa da gidansu ya ce" in sha Allah karshen watan nan za'a kawo sadakina, shikenan zaki zama tawa ko Khausar?"

Khausar ta sake sada kanta, tana jin wani abu na dan ratsa zuciyarta mai shige da salama
Chapter 40 · 0% Book details