← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 116

Sashe 15

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita dai du gannin abun take yi wani iri, bama da ta ga mahaifinta ya shigo da kankana da yan kayan hadin da ya saka Mama ta zana masa ya ba su Aisha kan su yiwa bakon ruwan tarba wanda hakan ya matukar sakata sake jin kunya da nauyin mahaifanta harma ta kashe wayar ta boye a daki ta wuni cikin tunanin ta inama zata fara ? Yaya zata dubi abin? Ta ina zata bi da abin? Haka dai ta har magariba ta kawo kai Mama ta shigo ta tasheta tana fadan me take haka bata kimtsa ba bayan ta san tanada bako?

Aisha ce ke dan murmushi tana kallonsu Maman na tsaye kofar bayi tana fadin maza ta yi wankan nan da kyau ta fito Rukaya kuwa ta idasa kimtsa kayan tarbar bakon ta saka a dakin Mama ta kilace bayan sun fitar da na gidan

Shirin ya zo mata wani iri, riga da sket dinta sai hijab wanda da kadan ya zarce gwuiwarta aka bata kan su zata saka domin tarban bakon

Ta saka sket da rigar ama ta kasa saka hijab din har Rukaya ta sanar da ita cewa bakonta fa na waje kusan minti ashirin kennan

Jiki ba karfi ta mike ta dauko wani hijab din sabo wanda suka saka ranar sallah ta zumbula abinta sannan ta dauki carbi kamar wace zata he bayar ta wa'azi ta fito tana rakubewa wayarta a kunnenta tana amsa kiran TAUFEEK dake sanar mata zai biyo ya bata katinta da zata bayar dan ta nace sai da ta buga mata kati na gayata ta samu ta wuce a gidan da kyar tana sauke ajiyar zuciya

Motar ta kurawa ido bayan ta ja ta tsaya a kofar gida, ance ta je ta shigo da shi ne, sai dai bata tunanin in har zata iya karasawa wajen motar cen dake tsaye ko ba zata iya karasawa ba, uwa uba yau anguwar dinke take tak da jama'a yan matan ne da samarinsu, tsofafin ne ana firar dare dai haka, kuma a hasken farin watan da ya haske anguwar tarin bolar dake zube ko'ina ta hasku tarrr haka itama ta hasku cikin farin hijabinta harma aka fara dan tsunguri tsoman ana raraba maganar cewa ta yiwu wanda ya saba zuwa ne ko kuwa menene wannan? Ciki harda yan matan da suka sha kwaliya suke kannan bayanta sosai sunna zaune a nasu gefen sun zubo ido sunna son gannin ya fito ya shiga cikin shigarsa ta kamala da tarin kwarjininsa kamar yadda ya saba, sai dai yau har yanzu babu fito daga motar ba

Tana kokarin neman layinsa ta ga ya bude motar ya fito, hakan ya sa ta dan sake matsawa kadan jikin garun ta sada kanta

"Barka da warhaka Hajia Kausar" ya fada da muryarsa mai sanyi kamar yadda ya saba yi mata magana

Cike da kunya ta dan dube shi, sai ta ji inama zata iya rage tsayinta koda basu zo daya ba ta dan gota shi kadan? Sai dai har ga Allah bashida tsayi ko kadan Mujaheed, dan dai yanada dan fadinsa ga tumbinsa kuwa a cikin manyan dinkinma ana gannin yadda ya yi gefe abinsa

Dan rage tsayi ta yi ta gaishe shi sannan ta sanar masa ance ya shiga ciki

Kwarai ya ji dadin haka, dan hakan ya nuna masa yana iya samun karbuwa wajen iyayenta, domin in har aka baka dama ka shiga cikin gida to fa ana da niyar dubanka ne

Har kasa ya duka ya gaisar da Mama dake labe daga daki sannan ya zauna saman tabarmar da aka shinfida masa, ita kuma ta labe daga fan lungun dakin su Mama tana ta aukin murza hannayenta

Su aisha sun gaishe shi sun kuma kawo masa ruwa sannan suka basu waje

Shiru wajen ya dauka, tamkar bata taba magana da shi a waya ba, kanta a kasa sai zufa take yi, haka yannayin da take ta motsa jikinta na alamun rashin sabo da zama irin haka da namiji ya bashi mamaki

Murmushi ya yi ya ce" KAUSAR, alhamdulilah, na godewa Allah da ya nuna min wannan rana, ina ta fata na ganta da raina da lafiyata, sai gashi na ganta, KAUSAR ni di ba yaro bane, inada mata biyu da Y'ayana bakwai, kamar yadda kika ganni a shagon gidanmu shagon mahaifina wannan itace sana'ata, watau ni dan kasuwa ne, a gaskiya ban cika jan neman aure ba dan in har na nuna ina so din nakan fito a mutun a bani na kilace, ni dai na ga kin min kuma ina sonki da aure, dan haka me kika ce ne ke KAUSAR?"

Magangannunsa ba da tashin hankali yake fadarsu ba, hasalima a sanyaye harufansa suka fi fita sunna shiga cikin kunnayenta, sai dai mamaki mai karfin gaske da ya kamata shine dama yanada iyali? Fuskarsa kamar bata nuna ya kwana biyu ba, bama wannan ba irin lokutan da ya ware yake kiranta bata taba sannin cewa shi din mai iyali bane da bata ringa amsawa a lokuta irin wadannan ba, domin yana kiranta kafin a yi sahur fa, haka kuma bayan an fito daga sallar asham yana kiranta su dauki lokaci mai tsayi sunna magana, magidanci? A irin wannan lokacin ai ko yayane yana tare da iyalinsa, in ta yi duba da lokutan da Abanta yake gida kennan, sunna tare baki dayansu a gida fa? Ina laifin ya ware lokacin da yake kasuwa ? Sai ta ji wani iri, ama kuma maganar wai ko dan yanada iyali zata iya kasa amsa masa ko daya, to mem ake tunani ne? Ita dama abinda take tunani kennan da rayuwarta cewa lalle ba zata taba aurwn saurayi ba, to ita a haka din nan ta auri saurayi ta ce me ta yi kennan? Tap ai da kunyama wani abin , ita aurensa da ya'yansa saima tace adu'arta ALLAH ya amsa sai ta je su yi zamansu

MUJAHEED ya dan sake muzgutawa ya ce" Hajia KAUSAR kar dai a saka na sare an min shiru?"

KAUSAR ta sake sinne kanta ta boye fuskarta cike da nauyi da jin kunya ta ce" In sha Allah zan sanarwa su Mama, abinda suka yanke sai na sanar maka"

Murmushi ya yi yana gyada kansa ya ce" Masha Allah, haka ake so, ya zamto ana tambayar amanar iyaye , to ama ke yaya kika ganni na maki ko?"

Ta kofar hijab din take dan kallon nasa, yadda ya wani kanne ido sai ta ji kamar ta kwala kiran Mama dan ta zo ta tayata gannin wani makararan rashin da'a, ama kuma sai ta kwabi kanta ta sake sade kai har dai ya gaji da surutunsa shi kadai ya gaza samun yadda yake so ya hakura ya mike cike da mamakinta, kwarai ya yi mamakinta, domin halayarta sai suka so bambanta da wasu yanmatan da yake kulawa , yan matan da kamar jira suke a taya su? In ka je inda suke kuwa sai in Allah ne ya tsare maka amaninka, in ba haka ba tsaf za'a iya lalata da y'a a gidan iyayenta, ama ita tabarmar da ya zaunama bata hau ba kuma kanta da ta sada har ya mike ya ajiye alherin da ya ajiye wanda sam bata kula ba bata dago ba sai da ta ji yana yiwa su Mama salama ne sannan ta dan ciciba ta mike murya a fan sanyaye ta ce" A gaida gida da Y'ayana Elhaji, Allah ya hutar da gajiya"

Yar dariya ya yi yana amsawa sannan ya sa kai bayan ya tabatar mata zai kireta fa kar ta kashe waya, ita kuma ta gama yanke hukuncin in sha Allah ba dai zata kuma amsa wayarsa a lokatan da take kyautata zaton magidanci na tare da iyalinsa, dan a yadda ta dafe din nan ta sha ruwan gidansu har ta batse ba zata so in ta zama matar aure a ringa yada mata mugwayen manufofi irin wadannan ba

Fitarsa da amsa kiran TAUFEEK ta tabata ko mota bai karasa ba, ya sanar mata ta turo Aisha ta amshi sakon zasu fice,

Da dan sauri ta ce" Aa, to bamu gaisa da ita ba zaka wuce ne? Bara na fito"

Tana fada ne ta katse sannan ta karasa ta sanarwa Mama da dan sauri ta fita ta tsalaka ta karasa kusan motar gefen da yake dan dayan gefen da take bakin hanya ne ta mika hannunta suka gaisa tana fadin" Amaryarmu, kin kusa zama tamu dai yar uwa nan da yan kwanaki"

Murmushi YUMNAH ta sakar mata tana fadin" Aunty Kausar har kin saka na ji kunya"

Dan murmushin ya yi shima ya juya a zaunen da yake ya ce" Kin ga sakonki baya ni fa ba zan shiga gida ba dan so nake na kaita na wuce akoy aikin dake gabana mai yawa"

KAUSAR ta je bayan ta bude motar tana fadin" Ba'a gama rikicin gidan bane TAUFEEK?, Ba zaka barwa HAJIA maganar ba"

Da dan haushi kadan ya ce" Haka fa, HAJIA HAJIA tsohuwar nan ni da ita ne, ai ta gama siye ƴaƴanta tsaf sun ce sai dai na yi hakuri har ta amince min zaman gidana daban, KAUSAR ki je ki mata nasiha ta ringa jin tsoron Allah "

KAUSAR ta kyakyace da dariya tana rike da marfin motar bata taba katon bokicin dake shake da tuyar da aka kawo masa ya sa Mamansa ta debar mata ba ta ce" Ni? Ai in na hadu da HAJIA ka tabata idasa ajiye maganar zamanka a gefenta zamu yi , TAUFEEK so kake dan shirin d amuke ya bare?"

YUMNAH da zuciyarta ta cika da tambayoyi game da mutumen da ya fito daga gidan wanda sarai ta sanshi , sai kuma maganar da ake kamar ana nufin a cikin gidan nan za'a zaunar da ita ko menene? Ko dai itace bata fahimta daidai ba? Sai kawai ta ji wani abin TAUFEEK na fadin ta sauke bokicin mana ya sanar mata fa sauri yake yi? Hakan ya sa da sauri ta kalle shi ta kuma kalli baya tana zubawa bokicin ido cike da mamaki da wani tsoro tsoro dan bokicin ta tabata na gidansu ne daya daga cikin bokitan da aka yiwa TAUFEEK din ne na kwarya kwaryar sallah aka kai gidansu ai ?
Chapter 15 · 0% Book details