Sashe 48
Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Tunda ya fadi sunnan nan, na mutumen da ta sani a matsayin TAUFEEK ZAKARI wanda sai daga baya bayan shekaru biyu da sanninsa ta san d'a ne a wajen Mai Kwanoni har ta san gidansu ta san ahalinsa sai kanta ya fara hade mata abubuwa sala sala ta yadda ta shiga tunani mai tsauri da nisan gaske har ta daina jin motsi da fahimtar abinda ake yi ta afka a tunanin me kennan? Me hakan yake nufi kennan? Menene wannan din kennan? TAUFEEK dinta? TAUFEEK din da iyayenta suka sani matsayin baban amini kuma abokinta?, Taufeek din da sai dai ta daki kirji ta fadi wanene shi wa duniya? TAUFEEK din dake kare mutuncinta su hau sama su fado su shirya? Taufeek din da yake tamkar wani babi na rayuwarta wanda take jin ba zata iya shaƙar numfashi ba tare da zumunci da shi ba?, Shi din nan da a cikin sirrin rayuwarta wanda Mamanta bata sani ba shi ya sani? Shine tsaye cen a matsayin bako sabon bako a duniyarta da rayuwarta baki daya?
Sai Khausar ta tsinci tunaninta na hade mata , domin tashi daya sai ta shiga tunanin to anya a tarenta da shi akoy abu daya da ta sani gaskiya? Kar aje ahalinsama da ta sani ba nasa bane, kar aje Mama ba mamansa nace, kar aje Hajia ba kakarsa bace, kar aje, kar aje kar aje.................... Harta shi din kansa lokaci daya tsoro ya shige cikin zuciyarta cewa kar aje aljani ne ya shiga jikinsu ita da iyayenta yake mu'amalar zumunci da su....., Kai hatta rashin samun mijinta sai da ya gifta a kwakwaluwarta cewar kar aje to aljanun a jikinta ne suke??......babu dai abinda bata saka a ranta ba, wa'inda burinta ta samu kanta gaban mahaifiya, mahaifiyarta kadai ce zata iya warware mata wannan rudani da tashin hankali
Ta matukar shagala a tunaninta ta ji an sauke hannu kan hannunta
Da sauri ta kalli wanda ya tabata, wannan suarayin dai ne, watau ta tabo shi dazu shine shima ya tabata yanzu tabawa irin wannan domin hannunta ya taba kai tsaye sannan da ido ya mata alamun ta mike mana
Mikewa ta yi, kaffafuwanta na son gaza daukarta ta zuba dubanta a kansu su biyu
Shi sir din, sai likitar mace wace ke sanye da farin glasss fara kal da ita da hakoran makarta biyu sai walwali suke ta dan zubawa yannayin Khausar din ido ta ce" Lafiya kike?"
Khausar ta hadiye wani irin yawu mai wuyar fasara kafin ta iya amsawa cewar kalau take
Kacokam ta maida hankalinta kan likitar nan, wace ta fara yi masu Barka da zuwa cikin mutuntasu ba da wulakanci ba, sannan ta shiga kwatanta masu yadda nasu gwajin zai kasance, yau rana ce ta farko zasu fara amsa tambayoyi ne a kan theori zuwa gobe wa'inda suka wuce sai su samu damar zuwa gabatar da pratical dinsu
Sosai suka bata hankalinsu, cikin nutsuwa a tsayen nan tamkar tashin hankali ta ringa jefo tambaya sai ta zabi wanda ta yi niya ya bata amsa, a kadan sai ta maka tambayoyi kusan goma kana bada amsa shi kuwa yana tsaye yana bi da kallo yana kuma rubutawa a wani litafi a hannunsa har aka zo kan khausar
Cikin ikon Allah a Tambayoyinta daya ce kawai bata amsa ba, itama ba sanninta bane bata yi ba, asalima shi likitan shine ya mata tambayar cikin Muryar nan tasa ta tsare gida da harare harare irin na manyan mutane a waje din nan , sai kawai ta samu kanta da zubawa fuskarsa ido har sai da ya cire nasa duban ya ba likitar damar yi mata tambaya sannan kiri kiri ya dora bata bada amsar wannan tambayar da ya yi ba
Ita dai likitar Tambayoyinta take yi har suka gama da su sannan aka umarcesu kan su je cafetariat su karya, zuwa karfe uku su dawo su duba sakamakonsu , du wanda ya samu gobe karfe bakwai ya samu isowa dan fara aiki
Da wannan suka fice, har ta kusan fita ta sake dakatawa ta juyo, yanzunma ita yake kallo, da kallon nan nasa wanda idan tana masa fada yake zuba mata ido ya yi ta binta da shi
A hankali ta lumshe idannuwanta wasu irin hawaye suka nemi saukowa daga gurbin idnanuwan nata
Da sauri ta cire kanta ta fice ta bi ayarin sababin mutanen da za'a daukan suka sauka
Sam Khausar sai ta kasa binsu wajen cin abincin
Asalima du gaba suka sakata sunna mata tambayar yaya za'a yi ta tsare sir da ido yana magana ta ki bada amsa?, Ta kuwa san wanene shi? Bafa ya son haka, idanma birgeta ya yi ta yi gagawar cire wannan tunanin a ranta dan kuwa tsaf zata iya hadiye zuciya ta mutu tana ji tana gani, domin dubunta sun rasa aikinsu saboda nacin sunna sonsa, wasun na nan cikin wahalar nuna masa soyaya, abubuwa dai gasunnan ba dadin ji a wajenta ita, saima kunya da ta ringa cike dukkan wani gaba na jikinta, a dole ta nuna masu cewar zata zauna a filin asibitin bata jin yunwa, da wannan suka shige suka barta sunna tayata aduar Allah ya sa kar ta jawa kanta saboda ta tsaya wasa a lokacin da ba'a masa wasa
Tana nan zaune sallah kawai take mikewa ta je ta yi a masallacin mata sannan ta dawo ta zauna har suka haura suka dubo result din, cikin ikon Allah a cikinsu babu wanda ba'a dauka ba, domin tana nan zaune suka kawo mata result din ta bi da kallo sunnanta ne na karshe a kafe a result din, ta yi dan murmushin yake suka zauna tare sunna dan zantawa da musayar numbo har yama ta yi sosai du suka mike kowa ya kama gabansa
A hankali take tafia, bayan tarin tunani mai kasara zuciya da kwakwaluwa tana tare ne da tarin yinwa da gajiya, dan abincin da ta ci tunda duku duku babu shi a cikinta,
Tsabar a rude take sai da ta karasa wajen ajiyar motoci zata ratsa ta wuce ta tuna tana da dan sahu, dan haka ta rakube jikin wata mota mai numfashi ta ciro sabuwar wayarta yar karama ta shiga kiran mai adaiditar
A kira na biyu ya daga yana bata hakurin bai daga da wuri ba
Murya a matukar sanyaye ta ce" Mun tashi"
Mai adaidaitar ya shaida mata cewa gayanan zuwa
Wayar ta kashe ta dan sake jinginar da bayanta jikin motar tana sauke ajiyar zuciya hadi da sada kanta kasa
A hankali kunnayenta ke jiyo mata takun mutane, da budewar mota da tashinta da tafia, har ta ji kamar ba kowa zuwa yanzun
A hankali hancinta ke son shaƙar mata kanshin turaran da itace ta bashi shi da kanta matsayin gift din aurensa tun daga lokacin idan ya kare sai ya saka ta kawo masa wani bata san dadinsa yake ji ko me ba
Bayan jin kanshin a daf da ita, sai ta fara jin alamun innuwar mutun, sai kuma idannuwanta suka sauka a bakake sidik din takalman ƙafarsa sau ciki masu masifar kyau da daukan ido
Da rashin kwarin gwuiwa ta dago dubanta ta sauke a saman fuskarsa, lokaci daya shi ya lumshe nasa idannuwan a hankali ya budi bakinsa ya ce" KHAUSAR......."
Da sauri ta sake bin bakin nasa da kallo..
.., eh Khausar ya fada , ita dai Khausar
A hankali TAUFEEK ya dan sake dubanta ya ce " Khausar Please, ki daina alamun nan na ranki a bace, tun dazu nake kallonki, ki daina min kallon kamar wani bakinki ko wanda ya maki karya, ki tsaya na fahimtar da ke abinda kike tunanin na boye maki kin ji?????"...... Ya fada, da sanyayar Muryar da ta san shi, Muryar da ta san TAUFEEK dinta da shi, Taufeek din mafarkin ta, ko tace aljannin tunaninta
Da sauri ta kuma cire dubanta a kansa ta juya da nufin tafia...............
Taku biyu ya yi ya riko mayafinta, hakan ya sa mayafin nata faduwa gaba daya daga jikinta daga yafen da ta masa
Ransa ne ya ji ya fara ɓaci, ya bi mayafin da kallo a hannunsa a lokacin da ta juyo da nufin amshe mayafinta ta yi tafiyarta ba tare da ta ce da wannan aljanin ci kanka ba, dan kuwa yanzun zata tafiyarta a kafarta ne ta sanarwa mama a yi gagawar kiran Aba a fada masa ya dawo du inda yake a mata rukiya, dan ta gama yarda ta jima a duniyar aljannu har ta janyo iyayenta ciki bata sani ba!
"Wannan din wace irin banzar dabi'a ce kike son dauka bayan kin san na hanna? Meye ya sa kika yafa wannan abin kika zo har nan da shi? Bayan wannan kika zo kina kallo saurayin nan na taba maki hannu ba zaki iya hannawa ba? Menene wannan sabuwar dabi'ar da ba taki ba? Bafa na son haka kin sani sarai?" Ya fada yana huci daf da ita irin yadda suka saba idan ta bata masa
Gaba daya Khausar sai ta karra tsorata, hawayenta suka bale, sai ta ringa hasko abin ta wata fuska daban.....ta yiwuma bakin aljani ne ya aureta tunda har yana mata kashedin wani ya taba ta