← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 116

Sashe 58

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ki je da Madam, ki aunata, bata da lafia " muryarsa ya sake katse mata hanzari

Sai da ta rintse idannuwanta, da kyar ta iya hadiyewa ta dakata har Yumnah ta gama shan kanshinta ta fito sai bubudewa take yi suka nufi labo

A lokacin da Khausar ke kokarin fitar da abubuwan bukata Yumnah na murmushi ta ce" Ai da kin barshi, ciwon nawa ba wani sai an auna na, furen soyayya na fara tsinka, wanda ya fi komai daraja da kowa a duniyar Mijina, wanda ya bani tun ranar da na zama halaliyarsa, ba kariya dan kar na samu baya kuma jin kunyar hakan!"

Har ga Allah, bata taba jin bacin rai irin na wannan lokacin dangane da rashin da'ar yarinyar nan ba

Hatta allurar dake hannunta sai da ta subuce ta fadi
Ba tare da ta bi ta kan allurar ba ta zubawa Yumnah ido, sai kuma ta zagayo a hankali tana sake Binta da kallo daga sama har kasa

Da kula sosai ta ce" Yumna, AKOY wata matsala tsakanina da ke ne wace ban san da zamanta ba?"

Yumnah ta wani gyatsine fuska ta ki bata amsa

Wani irin makuku da ya tsaye mata a wuya a lokacin sai ta ji koda korarta za'a yi yau saboda Yumnah a shirye take ta amshi korar

Rai bace ta damki hannun Yumnah ta juya da ita tana janta ta nufi office din nasa da ita, idannuwanta sun riga sun rufe ta manta waye shi a nan, kuma WACE Yumnah a duniyarsa

Tana buɗe office din su docter zasu fito
Bata tsaya bi ta kansu ba ta idasa shiga idannuwanta har ruwa ruwa suke da yaji yaji da karfi ta karra janyo Yumnah wace ke tirjewa gabanta na faduwa ta tsayar da ita a gabansa

Da mamaki su docter ke neman dawowa, sai dai tunda ya ga abinda yake faruwa dama ya zubawa camerar ido lokaci daya kuma ya masu alamar su tafi da hannunsa sannan ya danna abin rufe office din ya rufe da kansa ya sake zuba mata ido tasa zuciyar shima tana wani iri kamar wanda yake cike da tsoron abinda zai fito daga bakinta dan irin yadda kirjinta ke sama yana kasa sai da ya ji nasa kirjin shima yana hakan

A rikice ta dube shi sannan ta kalli Yumnah ta ce" Bama zan tsaya jin abinda ke tsakanina da ke da ya sa kike min abubuwa na rashin da'a ba, da shi din zan yi kuma daga bakinsa nake son ji! , TAUFEEK me matarka ke nufi da magangannu wasu iri da take aika min tamkar Ni din abokiyar gabarta ce ko wani abin ya shiga tsakanina da ita? Haka ranar da na je nemanka yarinyar nan ta min tsaki da wasu abubuwa mararsa dadi, yau kuma kace na aunata tana fada min furen soyayya ta tsinka na halar wanda ba'a saka abinda za'a hanna daukansa? Ni fa yar Hausa ce ba bagwariya ba, kuma abinda take nufi da Ni ina daf da ganewa harma ina jin kamar zan mutu da haushinta in kuwa haka ne!"

Fada take hawaye na gama cika idannuwanta ta kalli Yumnah wace ta gama sarewa duniya daga idannuwan mijinta ta ce" Ke kuwa, wace irin shashasha ce da zaki yi tunanin abokina zai iya zamtowa abokin aikata masha'ata? Ko ba haka kike nufi ba kar na maki karya na kulaceki?"

A rikice Yumnah ta Dube shi, ta kuma dube ta ta ce" Aunty Khausar Ni kuma?"

Khausar ta dantse lebenta sai ga wani hawaye wani na bin wani sunna bin kuncinta, a raunane ainun ta ce" Ni ba mazinaciya bace, Allah ne shaidata, ba komai tsakanina da mijinki sai zumunci gayanan ki tambaye shi, shikennan dan na zama sharar shanye sai a ringa wulakanta ni? Ba za'a barni na ji da ciwon dake ZUCIYATA ba sai an rikita min lisafi? .... TAUFEEK me yasa ne? Me na yi da zafi ne?, Me yasa TAUFEEK kowa idan ya mike yake kokarin ganin ya wulakanta ni bayan na kasance mai kare mutuncina?......" Ta idasa a matukar raunane, a hankali ta dafe kanta jin irin juya matan da yake yi ta juya tana cire rigar jikinta dan kuwa ta sani ne wannan asibiti yau ko ta aba ce ai an koreta kennan dan ta san ta yiwa oga fitsara an gama

Kofar take kokowa da ita dan ta budu ama sam kofar ta ki ta budu
Ta ja ta ja ya fi a irga ama kofa ta nuna bata san tana yi ba

A rikice ya juyo dan neman agajin a bude mata , sai ta ga Yumnah ta nufi dakin da yake na cenza suturarsa ta shige da dan sauri shi kuwa yana tsayen nan yana kallon gefe fuskarsa ta yi wani irin kicin kicin kamar ba TAufik din HAJIA ba

A hankali ya kawo dubansa inda take tsaye kikam gabanta na dokawa tana ta nazari kala kala

Da hannunsa daya ya mata alamun ta zo nan, hakan ya sa ta dan wara dubanta tana kallonsa da son karrin bayani

Lebensa ya sake dantsewa ya mata nunin ta zo inda yake nufi, ama Khausar ta ki aikata hakan

A hankali ya cire tishu ya dan goge fuskarsa sannan ya jefa shi cikin abin shara ya mike tsayinsa da kyau ya nufo inda take tsaye

Tunda ya taho Khausar ta samu kanta da kallon gabas da yama, kudu da arewa cikin tunanin ina wajen buya ba tare da ta gane haka take tunani a ranta ba

A hankali take ja ba, TAUFEEK na matse mata waje har ta kai jikin kofar nan ta rintse idannuwanta da karfi bakinta na bari ta ce" TAUFEEK dukana zaka yi?"

Bakin dake bari ya zubawa ido, a hankali ya sake kure mata duba kafin ya bude bakinsa a hankali ya ce"

*Kai matsa Bama son haka fa🙄🙄🙄😒*

💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

*DA CIWO A ZUCIYATA*

💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

_MALLAKIN_

*SAJIDA NIJAR*

*FREE BOOK NE* 3️⃣5️⃣

*GARABASA, GARABASA, PROMOTION, PROMOTION DIN LITATAFAN MARUBUCIYAR A KAN FARASHI MAI SAUKI 1K, YAN NIJAR KUWA 1000 FRANCS CEFA*

1: Duk karyar kada

2: Yar mahaukaciya

3: Neman na kaina

4: Bani da zabi

5: Bak'a ce

6: Kutkale

7: Makauniya ce

8: Mage

9: Duk nisan jifa

10: Idan ka raina inda kake

11: Dutse

12: Alkalamin kadarata

13: Bani da zabi

14: Dakika Biyar

15:Wata kokowar

16: Aure yakin mata

17: Ni zan ladabi

18: Daga tafia daukar soja

*Dukansu a kan farashi mai sauki, zaka saka dubu guda ne domin promotion ne nake yi, ka tuntubeni kan layina kamar haka +227 93 81 16 18, Sajida Nijar*

Now

*Da CIWO A ZUCIYATA*

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata💃💃💃💃💃

Bakinta dake bari ya zubawa ido sosai, a hankali ya sake kurewa fuskarta duba kafin ya bude bakin kasa kasa sosai ya ce" Menene wanann?"

Khausar ta yi gagawar lumshe idannuwanta sakamakon iskar bakinsa da ta dan shafi saman fuskarta a hankali har ta ji kanshin abin amfanin gyaran bakinsa, maganar kanshin jikinsa kuwa ji take kamar itane ta yi wanka da turaren, irin matsewar wajen nan ita da shi tunda suka hadu basu taba samun irinta ba

Khausar ta yi ta yi ta gane mene din a cikin tarin fitsarar da take nadamar dama bata masa ba wane yake tambayar menene din ta kasa ganowa dan abinda ta fada da yawa ai kau? A sanyyaye ta dan dago idannuwanta tana marairaice murya dan alkur'an du sai take tunanin wai kar fa ya zaneta fa, a raunane ta ce" Dan Allah ka yi hakuri, dama Mama ce tace yau na tabatar na baka hakuri , to dama WANCEN yar ce ta raina Ni take min wasu abubuwan fa shine na ga ai ta rainani kau, kuma magangannunta dai ba dadi sosai dan kamar wace ke zarginmu bayan Ni da kyau haramun din junna ne, ka yi hakuri ba zan kara ba besty"

Irin yadda ya yi maganar muryarsa a kurya ainun, haka ta bashi amsa, irin maganar nan ta cen cikin nan kana yi tsigar jikin mutum na tashi wace har ga Allah makocin daki aka cika yiwa itama a maganar salihan bayi

Maganarta take yi harda yar kwalarta , fatan da take ya matsa koda da taku daya ne ai inma a dakun ne zata fi shiryawa ba a shamaceta a nadeta ba ko? Ko ba komai mutumen nan kato ne, kato irin kartin nan masu tsayi da cika, yana iya fin karfin mata ai

A hankali ya kai yatsarsa daf da lebenta, sam ba da niyar tabawa ba, sai dai yana kaiwa din yatsar tasa ta dan dangwali abinda ke bakinta yake walwalwal kasa kasa ya ce" Ni ba fitsarar ba, yau kika fara min rashin kunya ne? Wannan abun da kika saka a bakinki menene kuma?"
Chapter 58 · 0% Book details