Sashe 113
Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sunna karasowa suka samu tuni su Yumnar sun iso, Yumnah na zaune a kasa kafafuwanta a hade waje daya, ciwo bai barta ba na haihuwa , ama yannayin mijinta shi ya fi komai daga mata hankali, yayarta na zaune daf da ita, mahaifiyarsu na saman kujera zaunen itama, ga dare dai ya yi ama tashin hankali ya saka su idannuwansu ya kekyashe tamkar rana, ga baby ta yi shiru abinta tana barci a hannun Akilah, Hajia na zaune itama , TAUFEEK na zaunen shima ama babu mai cewa komai tun gaishe da Hajia da suka yi da TAUFEEK din wajen ya dauki shiru
Kamar yadda suke zaune a kasa itama kasan ta je ta zauna daf da aunty Akilah, so take yi ta amshi babyn nan ta rungume a jikinta, tana so kwarai a bata babyn TAUFEEK dinta ta gani , ama ta san da wahala a bata shi yasa tunda ta ciro yar ta mikawa Akilah bata kuma nuna a bata ba ama tana matukar son kallon babyn ta kuma rungumeta a jikinta, ji take yi kamar itace ta kawo masa farin cikin nan, tabas ta san yana jiran wannan ranar, sai ga ranar ta zo masa wata iri, shi yasa ta so ta saka ya yi hakuri ama ya kiya, ta tabata ko menene to fa ya kai shi makura ne
Baba ne ya fara magana ta hanyar yin nasiha a tausashe ya ringa bada hakuri bale Hajia da ta kasance a wajen a dole ya bi yadda take so , sosai ya bada hakuri yana fadin" Idan rai ya baci, hakuri shine abinda ya fi dacewa bawa ya yi, bai dace ace an yi irin haka ba, a zauna a sasanta shi ya fi komai, ko menene ana iya sasanta shi a yafewa junna a ci gaba da rayuwa kafin mai rabawa ta raba, dan haka ko me yake faruwa a yi hakuri shi ya fi alkhairi"
Bayan ya gama nasihar da bada hakurin ne ya dubi maman su Yumnah ta bata damar yin magana
Itama a tausashen da bata taba yi masu magana ba yau ta dubi Mama ta ce" Hajia, dan Allah ko me ya faru a yafi junna a yi hakuri, mu bamu yi haka dan a bata maki rai ba, kuma kin gani Yumna yarinya ce ko me zata yi sai ana mata uzuri, ki yi hakuri komai ya wuce"
Mama dake zaune ta yi murmushi ta ce" Na hakura"
Daga haka ta mike ta juya da nufin tafiya
Baba da ya gama Sannin abinsa ne ya ce" Maman magidanci dawo ki zauna"
Mama ta dakata, a dole ta juyo ta dubeshi, kafin ta dubi Hajia ta ga hararar da Hajia ke sakar mata kamar idannuwanta zasu fado , sai ta yi wani murmushin ta dawo din ta zauna daf da Hajia ta sada kanta
TAUFEEK ya sauke ajiyar zuciya ya dubi mahaifiyar Yumnah da Yumnah din baki daya sannan ya kalli Aba, a tausashe ya ce" Aba, ka yi hakuri dan Allah ,ama bana tunanin bayar da hakurin nan a dunkule zai gyara Ni, dan ban me da me aka yiwa mahaifiyata ba duk wannan zaman da aka yi , wanda idan na ji ne zan iya ganewa in har zan iya yafewa ko waye, domin kaf duniya babu wanda zai wulakanta min uwa na daga masa kafa!"
Hajia aka wani saki murmushi tana sake ture daurin dan kwalinta gaba ta wani ja hannun riga ya yi sama kamar zata yi dambe ta ce" Ahaf, abubuwa ai an yi su magidanci ba dan kadan ba, Ni dai abinda nake so a gane a nan a cire min wata maganar rashin kunya cewar wannan y'a yarinya ce, ke yumana dan yan gidanku baki san darajar taki uwar ba? Ni fa munafunci ne da shashanci bana so, na fada a tsaye na fada a zaune karshe nima sai na zama abokiyar gabanta, ama idan zaki tuna na fada maki ke ki kiyayi magidanci da uwarsa wa bilahilazi idan kika yarda ya gane wawa ce ke sai ya tatakaki ya kaiki gidanku a kan mamansa, ke bakima san ruwan dake wankanki ba, sarakuwa ko bata sonka neman fada kake a wajenta bale wannan da babu abinda ya dameta da lamarinku ita fatanta ku zauna lafiya? Yo Ni nan meye baba ta soro bata min ba Allah jikan rai na yafe mata iyi? Ama haka na rayu ina bin gindi kar a watsani waje , uwa ai tana gaba da komai, in ba dan iska Bama waye zai raina uwar wani? Ki dauka a kan taki uwar gatanan mana iyi? In menene kece kika fara yiwa kanki, mu muna da sha uku aka mikamu daki muka iya girmama iyayen miji bale ya'yan yanzu ya'yan salula yar latse kunna dirowa duniya kuke matse anini, kuma kun iya neman maganin mata rai a shige daka da miji, har ku ne za'a koyawa kula da uwar miji? Da abinda ke ranki dai yar nan wanda ba zai samu ba dan gaskiya ina tsoron shima ba zaki samu ba, ki sauke kanki in zaki sauke a yi rayuwa in kuma tashina tashina za'a yi in fede biri da abawa a wajen nan na irin laifukan da kika yiwa uwar magidanci kau?"
Kusan a tare su uku suka nema ba sai Hajia ta fada ba, kowane da yannayin da ya yi furucinsa ama matsayar su daya ce kar Hajia ta fere biri da abawan nan da tace zata fere, da baba mai kwanoni da Yumnah da kuma mahaifiyar Yumnar
Yumnah murya na rawa ta ce" Mama dan Allah ki yi hakuri, dukkan abinda na maki ki yafe min in sha Allah ba zan kuma ba, baba da Hajia dan Allah ku ba yayanmu hakuri ba zan kuma ba"
Baba sai ya karra jin tausayin yarinyar ya kama shi, ko dan bai san me da me ta yin bane? Ama ko menene yana ganin ana iya yafe mata, ko menene, dan haka a tausashe ya dubi maman TAUFEEK ya ce" Hajia karama, ki yafewa yarki kin ji? Kin san yayanmu sai da hakuri, ki dauka yarki ce ta maki laifi ta kuma yi nadama kin ji?"
Mama ta sauke ajiyar zuciya yanzunma a tausashe ta ce" Ni fa na jima da na yafe babansu, Allah ya shirye su ya musu albarka"
Da amen aka ringa amsawa, Maman Yumnah ta sauke ajiyar zuciya ta ce" an gode Allah ya saka da alkhairi an gode sosai, kin ga ta karu Yumnar idan da hali sai a kaita asibiti dan kar ta kwana abin ya zama wahalarwa"
Baba mai kwanoni kam sai ya mike gannin an samu sasantawa ya karasa ya dauki yar ya je ya duka daf da Hajia ya bude mata yar fuskar jaririyar yana murmushi ya ce" Hajia ga fa amaryar tawa, Ni sai nake gannin kamar ta fi magidancinma kyau masha ALLAH"
Hajia da kwallah ta tarun mata a ido a hankali ta amshi yar tana kallo , sai ta saki murmushi ta dago tana kallon Mama da Khausar dake matsowa tana so a bata, Hajia ta sake sakin murmushi ta ce" Matso ki tayani gani Khausara, kin ga yar y'ar magidanci , kin kuwa san irin adu'ar da nake yi Allah ya nuna min, kai shedan ko dan hegiya Allah dai ya rabamu da sharinsa! Mai kwanoni ka mata huduba mana ka ji? Wani sunna za'a saka mata?"
Baba na murmushi ya kalli TAUFEEK da har yanzu ba wani sakin fuska ya yi ba ya ce" Wani sunna kuka zaba ne Elhaji karami? Ka kuwa dauketa? Kamarku daya, kennan kama take da Mamanka, matso ka yi mata addu'a sannan ka duba lafiyarta idan kuwa asibitin zasu tafi sai a kai su a basu dukan kular da ta dace, Allah ya yi albarka"
A tausashe TAUFEEK ya amsa da amen Aba, sannan ya sake sada kansa a tausashen ya ce" ka yi mata da sunnan Nana Khadija Aba, Allah ya raya ya yi mata albarka"
Aba ya amsa da amen ya Allah, hakama dukkan wani dake wajen
TAUFEEK ya dora da fadin" sai dai ina neman alfarmar a yi hakuri da maganar fitan, zan dubata da kaina, ko wanka ba zata je gida ta yi ba zata yi a nan gidan, idan akoy Wada zai zo ya zauna mata Tom, in babu Hajia zata samo duk wace ta ga ta yi ta zauna mata, sai abu na karshe, Yumnah ki ji tsoron Allah ki kuma guji fushina, ba zan lamunce ki wulakanta koda auta bane a gidan nan dan Ni ban wulakanta kowa ba a gidanku, ki sani raina mahaifiyata shine mafi munin kuskuren da zaki kuma tafkawa, domin wannan zama da aka yi yau ina mai tabbatar maki ba za'a kuma maimaitashi da Ni ba, ba zai yiwu ace kulun ina tara iyayena a kaina ba, inaga na yi girman da zan kare masu wannan tashin hankali na iyalina!, Idan har da hali zan so ki gane mu zauna lafiya, idan kin kiya Yumnah ba zan iya zuba maki ido ki wulakanta min wace ta haifa maki Ni ba, du dadin zaman da zan ji da ke lami ne idan har baki girmama min uwa ba"
Yumnah da sai yanzu ta ji sanyi na ratsa zuciyarta ta girgiza kai da sauri ta ce" In sha Allah ba zan kuma ba yayanmu" a zuciyarta kuwa tana ayana' bi izinillah ba zan kuma ba, koda mama bata so na zan yi mata biyaya bale su Hajia ne ke cewa ba zata taba so na ba, sai yau na ankara da aunty tace na san basa son mijina Ni me zan masu a duniya da zasu so Ni? Kowa ta kansa yake yi, nima kuwa zan yi ta kaina, Khausar ta zama zanen kadarar rayuwata Allah ya yi sai ta auri mijina , in sha Allah zan koyi zama da ita, ina ji ina gani na haihu maimakun na zamto ina cen lulube ana jiji da Ni gani a filin Allah ko ciwon baya damuna kamar bacin ranka? Soyaya ba karya bace Ni na san ina sonka kuma zan yi maka biyaya koda kana cutar da Ni ne bale idan har na nuna ka cutar da Ni na zalunceka!'