← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 116

Sashe 9

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin hawaye ne mai dumi ya shiga kokarin saukowa daga cikin kurmin idannuwanta dan zubowa saman fuskarta a lokacin da ta shiga tambayar kanta shin menene laifinta ? Menene laifi dan ta zamto mai rufe jikinta?, Menene laifi dan Allah ya haliceta a yadda ya haliceta? Ita dai ba mai munin da za'a ce kai wance kuwa akoy muni ba, dan har fadi ake yi ta fi yan uwanta dorinar kyau kawai dan bata fitar da kyan ne......, Sha nawa ake cewa da ace zata yi kyale kyale irin na yan mata ta yada wannan hijabin da ta ga maza na biniyarta kamar kuda, mutun nawa suka ce idannuwanta, girarta, karan hancinta, bakinta abin kyau ne a idon mai kallo koda kuwa baya so.............., Fatar jikinta mai haske ce domin ta yi hasken mahaifiyarta ne, yannayin jikinta ba dati ba wari, shin wannan bai isa namiji nagartace ya nuna yana yinta ba?....., A yanzu dududu idan ta ajiye rayuwar nata a fili ta duba ba zata ce ga tsayaye nan da ya nuna mata aure yake so ba, ita fa kunyar yin zancema take ji, haka kuma kunyar yin saurayinma take ji, ita baban abinda ya fi bata kunya ace za'a mata aure itama, duda ta dade da yarda cewa auren nan ka so shi ko ka ki shi akoy lokacin da jiki ke amsawa hankali ya damu da bukatar abokin halita sai dai idan ka ki bada hankali ka yi watsi da lamarin a samu sasauci ba wai a daina jin bukata irin ta hannun bawa a jikin baiwa ba!
A yanzu shekara ashirin da shida kennan tana rayuwa, tunda ta yi ashirin da uku ta ga haila, a hankali ta shiga saka rigar mama duda ba wadatatun maman ne da ita ba ama mamansu bata yarda dan baiwa Maman kariya da zubewa ko lalacewa, ....sannu a hankali take fuskantar kaikayi irin na jiki mai zuwa ba dole sai an gayato shi ba, a hankali ta koyi korarshi harma ta dawo ta koyi rayuwa a haka,...............ita baban abinda ya fi tsaye mata a rai shine shin me ta yiwa maza da zafi haka ne? Me suke nufi to da ita ne? , Shin a matsayinta idan ta dauki dabi'a irin marar kyau yawo da dan gyale hakan zai zamto alkhairi a gareta da ahalinta da al'umar annabi kuwa?, Me yasa ita ta kasa samun wanda zai fito magana ta tsaya tsayin daka har ya kilaceta matsayin mata ba?, Sau biyu magana na yin kwari da ita har Aba ya sani sai dai shuuuuuu kamar an yi tsatsafa an dauke dan kuwa ko yarfin ruwan kafin a fito ya gushe a ido ne, dan mahaifiyar daya tsaf ta nuna ina hadinta da danta? Wannan jiki haka ai ba na zaman karamin yaro bane sai dai tsoho

Wani hawaye ne mai zafi ya ringa bin kumatunta, a hankali ta dora hannunta daidai kahon zuciyarta ta shiga ayana kalamai kamar haka' Shin laifin duka nawa ne? Nice ko? Nice na kasa maida hankali nima na yi kwaliya ko an aureni ko?, Nice na kasa tsayawa na yi dinki irin na yan mata ko a kulani ko? Du laifina ne nice nan bana sakewa mazan fuska ko?, Dan Allah Allah ka san nima na samu mai sona ko na samu ciwon dake zuciyata ya bace, domin *DA CIWO A ZUCIYATA* mai karfi ubangijina......'

Gannin tana neman kamuwa da cutar cuwon barin kai saboda tunani ya sakata mikewa a hankali ta je ta dauro alwallah sannan ta dawo ta kabarta sallah ta shiga yin nafila
Sosai takw hawaye a cikin sujadarta tana ambaton sunnan Allah kamar yadda ta saba, fatanta Allah ya bata miji na gari itama wanda zaya *YANTATA*, Burinta ta samu miji na gari wanda zai sota domin Allah ya riketa domin Allah, ta tabata Allah zai bata itama , a da damuwar bata gigitata har haka, a yanzu da mahaifinta ya yi maganar nan sai ta ji duka kaf hankalinta ya gama tashi

💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

*DA CIWO A ZUCIYATA*

💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

_MALLAKIN_

*SAJIDA NIJAR*

*FREE BOOK NE* 6️⃣

LITATAFAN MARUBUCIYAR

Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Neman na kaina
Bani da zabi
Bak'a ce
Kutkale
Makauniya ce
Mage
Duk nisan jifa
Idan ka raina inda kake
Dutse
Alkalamin kadarata
Bani da zabi
Dakika Biyar

Now

*Da CIWO A ZUCIYATA*

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata💃💃💃💃💃

A yanzu da mahaifinta ya yi maganar nan sai ta ji duka kaf hankalinta ya gama tashi, bata da wani sukuni, da kyar ta ji sasauci a zuciyarta har barci ya yi awon gaba da ita

Dukkan abinda suka saba yi da sanyin safiya yauma suka gabatar, sai dai babu wanda bai kula da yannayin sanyin jikinta ba har suka zauna dan karyawa

Sunna tsaka da karyawar ne aka yi kiran mahaifinsu cewa yar abokinsa ta rasu magidanciya, wannan dalili ya saka shi mikewa ya shirya da gagawa ya fice ba tare da sun samu sun yi zaman na safia ba

A sanyaye ta sanar da mahaifiyarta yau ake kafa masu result na exam dinsu da an jima zata je, maman nata ta amince ko dan ta samu ta je ta dan sake, domin itama karfin hali ne take yi bata da karfin jure yannayin KAUSAR

Du a nan tsakar gidan suke zaune KAUSAR ta yi wanka ta shige

Da kiciniya dai su suke ji, ama babu wanda ya kawowa ransa abinda yake faruwa, haka kuma ta dan dauki lokaci a cikin dakin bayan ba sabonta bane jimawa ana shiryawa har ta fito tana ta sisine kai dan har ga Allah kunya take ji kwalin da ta saka da girarta da ta caje da dan jan bakin nan kar mahaifiyarta da yan uwanta su gane, sai dai ta makaro domin ko kanshin turaran da take bazawa ya fi wanda ta saba dan gigawa hamatarta, na yau mai girma ne, haka da ta duka dan amsar kudin da mamanta ke bata dole suka yi ido hudu har maman nata ta ga kwalin dake saka idon nata hawaye dan bata saba ba, hakan ya sale karyar mata da zuciya ta dauke kai da sauri ta laluba yar karamar jakarta ta ciro dari biyu ta karra mata sannan ta suri bokici ta ce" Idan kin fito daga leka sakamakon ki tsaya gidan Laria ta maki kitso "

Kudin ta cure a hannunta ta yi wufff ta fice a gidan cike da tarin kunyar hijab din dake jikinta bai kai mata har idon kafa ba kamar yadda ta saba sakawa, tsayinsa daya da tufafinta

Tun tana tunanin zata iya jurewa ta dago kanta har ta sadakas gaba daya ta ja hijabin ta rufe jan bakin tana jin nauyi a ranta kamar ta aikata wani abin kunya

Haka ta je ta duba result dinta sannan ta fito ta karasa gidan Laria ta shige suka shiga hirar yaushe gamo aka kwonce kan aka shiga wankeshi bayan ya bushe aka dasa mata kitso wanda zai hau da yannayin gashinta

Ita da kanta sai ta ringa jin wani dadi dadi a kan nata, bama da ta je ta yi alwalar sallar azahar haka ta jita sakai ruwa na ratsa dukan kofofin kanta

Sai kusan la'asar ta fito daga gidan, haka kawai ta dasa tafiyar kafa, tafia a hankali ba kamar yadda ta saba ba, tana tafe tana tunanin dacewa a cen kasan zuciyarta, a ganninta yanzun kam ga kunshi a hannunta, ga kitso, idonta da kwali daidai gwargwado dai ai kwaliya ta kare ya dace ta samu mashinshinin da zata yiwa Abansu maganar itama ta samo fa, sai dai abin mamaki har ta cinye dogon layin kasuwa ta shiga na gidansu shiru kake ji wai maye ya ci shirwa, a lokacin da ta kawo kan kwana nema ta kusan hadewa da wani dan garuwa kana ganninsa ka san ba yaro bane ya wani ce da ita yi hakuri Mama ban kula ba
Ita da abin ya wani daketa ko ci kanka bata ce da shi ba ta ci gaba da tafia zuciyarta na zafi har ta shige gida

Ko da ta shiga gidan kasa cin abinci ta yi,mahaifiyarta dama sunna cen kai gara, sai kannenta Rukaya na kicin Aisha na wanke wanke ya wuce dakinsu ta tsuguna cen wata loko ta hade kanta da gwuiwa ta fashe da kukan da take ta rikewa tun a hanya

Da sauri Aisha ta dago daga wanke wankenta ta kallo kofar dakinsu, hakama Rukaya dake kada miya da sauri ta kallo wajen

Rige rigen shiga dakin suka yi dan kukan na KAUSAR har tsakar gida

Gaba na Faduwa Aisha ta duka tana kokarin kama KAUSAR ta ce" Auntynmu lafia? Waye ya saka ki kuka?"
Chapter 9 · 0% Book details