← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 116

Sashe 81

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ya sauke ajiyar zuciya ya ringa takowa har inda take tsayen nan tana ta kiciniyar kunce agogon da aka daura mata ta gaza ya tsaya daf da bayanta bayan ya zubawa bayan nata ido a hankali ya sauke dubansa a wajen kugunta daidai inda ya lotsa saboda tudun mazaunanta da fadinsu sai ya zamto nan daidai tsatsonta kamar tana masa da gangan ko dan ta nuna kirarta bayan haka Allah ya haliceta kwatuwar wajen ne ya sa nan din karyewa da fitar da shap dinta sosai

A hankali ya sako hannayensa ta bayan nata ya dora hannayen nasa saman nata ya rike agogon yana kunce mata a nutse hakan ya sa ta dago a tsorace ta zarro idannuwa tana kallonsa ta madubin

Shima dagowar ya yi ya saka nasa idannuwan a cikin nata
Wa'inda a yau ya kasa boye dukkan nau'in abinda ke zuciyarsa a cikinsu, suka bayyanar da shi suka tona shi
A cikin makoshi ya budi bakinsa kadan ya ce" Barka da zuwa gidanki *MY WIFE*"
A rikice ta sake zuba masa ido, sai kuma ta buda hannayensa ta juyo da sauri dan son fita daga wannan mugun tashin hankalin da yake son sakata gabanta na dokawa, sai dai tana juyowar ya zamto yanzu ido cikin idon ba ta madubi bane suke yi, ta gar da gar ce

Da sauri ta sada kanta, lebenta sai son kiran sunnansa yake yi ama ta gaza fitar da amon

Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya dan matsa baya kadan sannan ya kamo hannunta kasa kasan ya ce" Zo mu je"

Kasa hanna kanta binsa ta yi, du kuwa da irin yadda jikinta ya mata nauyi har suka karasa kofar dakin Yumnah ya dakata ita a gefensa kadan yana kallonta ya dan buga kofar ta sake zuba mata ido

Basu wani dauki lokaci ba suka ringa jin nishinta da kyar

Da sauri Khausar ta dago kanta daidai lokacin da Yumnar ta bude kofar da kyar , sai luuuuuu ta fado jikinsa tana sakin hannayenta gaba daya tamkar wace ta tafi duniyar summa

Ba wai shi ba da bai shiryawa haka ba, ita kanta Khausar sai da ta kwala ihu a tsorace tamkar ba likita ba tana ja baya kadan sannan ta yiwo gaba tana kama masa da taya shi ambaton sunnan Yumnar

A rikice ta mike tsaye tana fadin" Ina valise dinka? (Wato ta likitocin nan ta duba marar lafiya)"

Rudewarsa bata kai Tata ba sam, shi dai ya talabi Yumnah ne yana kiran sunnanta da dan buga gefen kuncinta

A nutse ya mike da ita tsaye ya juya yana sauka Khausar na biye da shi ya ce" Tana part din Hajia"

Bata tsaya jiransa ba ta wuce da gudu, abinka da likita kamar masu wani boyeyen tsumi idan suka hadu da marar lafiya a waje, ta je bangaren Hajia wace ke sauraron wa'azin karfe goma ta fada da gudu gudu bayan ta yi salama ta ce" Hajia, ina akwatin TAUFEEK ta asibiti?"

Hajia kiris ya rage bata fado ta kai ba ta mike jiki na bari ta ce" Me ya samu magidancin? Innalilahi na shiga uku, gatacen a kasan gadona "

Kafin Khausar ta fito ta sanar mata Yumnah ce ba lafiya tuni ta nufi bangaren TAUFEEK din sai salalami take yi hawaye kuwa tuni ya bale mata

Khausar ta dauko da saurinta tana jin abin nan kiris ya rage ya tadeta dan sai da ta rike abu da ya dabaibayeta ta rasa yaya zata yi sai kawai ta karasa kofar falon da kyar ta tsaya ta warware nadin kaf dinsa ta yarfa a gefen kafada ba tare da tunanin komai ba ta shigo da akwatin da dan sauri ta kawo daf da shi sannan ta zauna ta bude tana kallonsa ta ce" Me zan miko?"

Sai a lokacin Hajia da ta turo baki ta juyo ta kalleta da niyar kai nata rankwashi ta kuma sileta tasss dan ta kusa hadasa mata hawan jini ashe wannan ce take marmarmartu kamar ta summa bayan ita sai ta rantse da huwan rahamanu karya ne dan ta hanna magidanci rawar gaban hantsi ne, ita kuma ta wani je a guje kamar mai kwanoni ne ba lafiya mai malan muntari tsabar rashin Sannin ciwon kai sai kuma ta yi arba da Khausar din a Khausar dinta

Ido ta fara fitarwa, sai kuma ta tafa hannunta ta ce" lah lah jama'a astagfrullah ke y'ar nan ke ce?"

TAUFEEK dake kallon yannayin Yumnah yana tunanin to mema zai yiwa Yumnar domin ba jinnin ne ya dawo ba, yana daf da cewa Khausar ta bashi abin auna hawan jinni maganar Hajia ta saka shi dagowa shima ya kalli Khausar din, daidai ta rikice tana son warware lafayar da bata san ta inda zata maidata ta daura ba, kawai sai ta mike da gudu ta nufi haurawa sama tana mai fashewa da kukan takaici har ta bacewa ganninsu dan kuwa TAUFEEK da Hajia da suka daga kai suka bi mata da kallo sai da ta bacewa ganninsu sai kuma suka juyo a tare suka yi ido hudu shi da Itan

TAUFEEK ya daka fuska yana hade girar sama da ta kasa ya ce" MEYE!?"

HAJIA ta tabe baki ta dauko akwatin ta turo masa daf da shi da gunguni tana gyara daurin kalabinta ta ce"

Hi PEOPLE 😍😍😍😍

Maganar adabi ce muke:

A tafiyar labarin *AZAL* ina dauke da *ADABI* ne kamar haka Zamantakewa
Yaki a soyaya
Kauranci
Bariki

Ya rab ka nuna min ranar fara shi lafiya idan har alkhairi ne

[7/21, 8:25 PM] +234 708 653 0343: 💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

*DA CIWO A ZUCIYATA*

💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

_MALLAKIN_

*SAJIDA NIJAR*

*FREE BOOK NE* 5️⃣0️⃣

*GARABASA, GARABASA, PROMOTION, PROMOTION DIN LITATAFAN MARUBUCIYAR A KAN FARASHI MAI SAUKI 1K, YAN NIJAR KUWA 1000 FRANCS CEFA*

1: Duk karyar kada

2: Yar mahaukaciya

3: Neman na kaina

4: Bani da zabi

5: Bak'a ce

6: Kutkale

7: Makauniya ce

8: Mage

9: Duk nisan jifa

10: Idan ka raina inda kake

11: Dutse

12: Alkalamin kadarata

13: Bani da zabi

14: Dakika Biyar

15:Wata kokowar

16: Aure yakin mata

17: Ni zan ladabi

18: Daga tafia daukar soja

*Dukansu a kan farashi mai sauki, zaka saka dubu guda ne domin promotion ne nake yi, ka tuntubeni kan layina kamar haka +227 93 81 16 18, Sajida Nijar*

Now

*Da CIWO A ZUCIYATA*

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata💃💃💃💃💃

Hajia ta tabe baki ta dauko akwatin aikin ta turo masa daf da shi tana guna guni ta ce" Miya ce, ai yau ka ga me nake nufi da ana gudu abu ba motsi, sai ka yarda a maka sakiyar da ba ruwa malan!"

Shi dai bai kuma bi ta kan Hajiar ba, Yumnah dake kwonce jikinsa tamkar wace ba rai a jikinta ya zubawa ido , kallonta yake yi zufa zufa na tsatsafowa a gaban goshinsa

A hankali ya sauke ajiyar zuciya a tausashe ya ce" Yumnah, ki buda idannuwanki"

Sosai gabanta ya fadi jin maganarsa, kar dai ya gane lafiyarta kalau? Sosai kirjinta ya ringa dokawa da tsoron kar aje ya gane cewa lafiyarta kalau ne

A nutse ya mike da ita ya haura saman dakinta da ita
Ruwa ya haɗa a dan karamin bokici da farin tawul ya zauna daf da ita, a nutse ya ringa dan matsewa yana dan goge mata goshinta sannan ya kunna mata kira'a
Bayan ya gama still yana zaune ne rike da hannunta dan ba zai iya tafia ya barta a wannan halin ba, duda babu abinda ya fito filin da a matsayinsa na likita ya gani na daga hankali, tana numfashinta normal, ama tunda ta yi haka sai ya bita a hankali ko dan abinda ke cikinta

Tun tana summan gangan har barci ya fara fizgarta a hankali barcin ya dauketa ama a kala ta kai karfe biyu da wani abu na dare

Mikewa ya yi bayan ya gyara mata kwonciyarta ya fice a dakin
Wani irin abu yake ji mai kama da bacin rai a kasan zuciyarsa, ama ya dane ya karasa kofar dakin Khausar a hankali ya dan murda kofar
Jin a rufe ya saka shi sauke ajiyar zuciya ya nufi nasa dakin

Da kyar ya samu barci ya dauke shi, cike da bege da tarin kuncin abinda yake tunanin na nema ya fara zama rainin hankali

A bangaren Khausar kuwa, tarin kunyarsa ya saka tana shigewarta ta saka sakata ta karaci kukanta sannan ta je bayi bayan ta gama karewa bayin kallo ta yi wanka ta fito ta bude bangaren tufafinta ta dauki riga marar nauyi ta saka ta fesa turare a jikinta sannan ta saka hula fara ta je ta yi addu'a ta kwonta tana ta shaƙar sansanyan kanshin sababin kaya da turaren dakin har barci ya dauketa cike da jin kewar iyayenta
Chapter 81 · 0% Book details