Sashe 6
Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata
Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata💃💃💃💃💃
A nutse ya nufi bangaren Matan gidan, watau matan Elhaji yana sauke idannuwansa a kan kannensa uku dake zaune a baban filin kofar dakin mai dauke da farin tiles da shukokin da duka zagaye wajen sunna bitar karatun islamiya, ya tabata malaminsu bai jima fa tafia ba ya kuma basu assignment na yi
Amsa gaisuwarsu ya yi da kula, sai kuma ya dakata dan a lokacin ne kanwarsa mai sunna ISHRAT ta taso da ladabi ta ce" Yayanmu, Aba yace idan ka shigo ko wani lokaci ne ka je baya samunka a wayarka"
Jim ya sake yi a dole yana dan kallonta kamar itace ta kar zomon, dan maganar sai ta so dauke masa a harshensa domin ya so ne yace da ita Aban na nan? Sai ya ji ya kasa ciro kalmar a dole ya juya kawai ya shige tankamemen falon gidan nasu mai dauke da bangare bangare na falo uku dauke da kujeru saiti uku kala daban daban da kwaliya irin ta manyan mata masu maiko a baki
Takalminsa ya cire , sai farar safar kafarsa ya idasa shiga
Matan mahaifinsa su biyu dake zaune a falon Hajia FATAHEEYA sunna hira ya karasa da kula sosai da kuma ladabi ya gaisar da su kafin ya mike ya shiga haurawa sama bayan sun gama gaisawar dan nufa bangaren mahaifiyarsa hankali kwonce ya bacewa ganninsu
Shiru ne ya ratsa wajen nasu bayan tafiyar tasa, shirun har na dan lokaci domin kowace shirun da ta yi a cikin zuciyarta tana tunanin abinda ya tsaye mata a rai ne wanda yake damuwarta ko jin dadinta, sai dai a irin yannayin fuskarsu ba sai an tambaya ba abin tsaye masu ne ya yi , ba damar amayarwa, dan ko a tsakaninsu babu wace ta yarda da y'ar uwarta, zama ne ake yi na bugun ciki da munafurci, kowace na boye kalar wasanta ne dan sun yi wayon da ba zasu hada kai da kishiya ba, komai dadin dan miji ai ba d'ana bane...in ji Hajia NUWAIRAH
Wannan d'an daya cilo namiji ya zame masu wani baban gibi mai wuyar fasara
Shi din nan shine baban damuwar cikin kuryar zuciyarsu
Idan suka yi tsai suka duba irin girma da darajar da yake da ita aa cikin gari kadai sai su ji inama ace da wani gagarumin ciwo suke fama da wannan faduwar gaban
Irin daukakar da yake da ita a aikinsa, wanda yake matsayin baban likita aka nuna masu kuma ua dawo karatu,karatun wani munafurci? Kuma mahaifinsa ya ja maganar idan suka fitar da sirrin yaronsa daidai suke da fita a gidansa ya sake hadasa masu wutar kiyaya boyayiwa fiye da ta kishi
Juyowa Hajia NUWAIRAH ta yi bayan ta saisaita yannayin fuskarta sukai ido hudu da hajia FATAHIYA
Murmushin yake da ya fi kuka ciwo suka sakarwa junna , cike da isa irin ta isasun mata Hajia NUWAIRAH ta ce" Muna da shagali baba a gidan nan idan auren Elhaji karami ya tashi"
Da dan yanga da basarwa Hajia FATAHIYA ta dan yarfe hannu da cikinta a gaba wanda duka duka watansa biyu a jikinta ama idan tashi zata yi tana turo shi in zama haka dan abin nema ne ya samu ta ce" Ai kam, na san ranar ke uwar ango har kya yi kari da zinari dan farin ciki, Allah ya nuna mana"
Murmushin ta yi itama , ama bata bada amsar Adu'ar ba, karshema sai ta mike tana nufar sama bangarenta dan abinda ke ranta lalle lalle sai ta amayeshi zata ji dadi
Tana bude dakin nata ta ga yarinyar wajen yayanta da take riko wace tun tana karama aka bata zaune tana waya a saman kujera
Direct ta karasa inda take ta karbi wayar gana duba da wanda suke wayar, gannin sunnan kawarta ya sa ta mika mata wayar sannan ta nufi bayi tana ta dane abinda yake tukarta, dan kuwa ba kowa ne ya san me take ciki da asalin d'an mijin nata ba
Tana shiga ta rufe ta karasa ta kunna ruwa sannan ta cire dan kwalin kanta ta kama kanta da hannayenta bibiyu dake sara mata
Ta jima a haka sannan ta dago kanta idannuwanta na sake yin ja ta kalli madubin da idannuwanta da suka yi kamar sun rine na bacin rai sannan ta girgiza kanta tana sakin murmushi mai ciwo ta ce" Na tsaneka kamar yadda na tsani mutuwata!, Lalle zan rayu da burin gannin bayanka! Ba mutuwarka nake so ba, ka tagayara ka zamo dan daudu, ka zamo wanda ana takamar kaine namiji daya jal da aka haifa ama kuma ba anfani, yadfa uwarka ke rayuwa da farin cikin kai daya jal ta malaka tana ji tana gani zaka salwanta ka daura zani elhaji ya tsine maka ya kore ka! Yadda ubanka ya sakar maka ragamar dukiyarsa na rantse da wanda raina ke hannunsa sai ya kuleka saboda dukiya domin sai na yi sanadiyar da zaka zamo tamkar kare a bin mata, mai kuma shaye shaye dan kuwa du wanda ya auri bin mace ba zai taba ajiye dukiya mai albarka ba komai kudinsa, a haka zaka karar da dukiyar ta yadda sai ya yi shara'a da kai sannan ya tsine maka ya koreka!, Wannan alkawarina ne!".............
Da kyar ta iya saisaita kanta sannan ta fito muryarta bata fita da kyau ta ce" Ke Hamdiya Ajiye wayar nan maza ki sauka ki ce da auntynku na shiga nafila ba zan sauko ba dan kar ta ga shiru"
Ajiye wayar Hamdiya ta yi ta dauki hijab dinta ta saka sannan ta fice, dan kuwa dokar gidan ce, ko mace dokar yayansu ne ya masu hani yawo ba hijab ko shigar da zata rufe suturarsu sosai koda a falo ne, idan dai so kake yi ka yi yawonka tsirara ko da shiga ta rashin da'a cen ka kule dakinka ka yi, in kuwa ka yarda ka fito da shigar da ba ita ba aka yi rashin dace ka hade da shi a ranar tsag zai darwaye maka fata kuma babu abinda za'a yi
Da takaici ta kule ganninta a kan Hamdiya ta karasa saman kujerar cikin dakinta na farko ta zauna tana kada kafa........., Watau du iskancin FATAHIYA baya gabanta, wani jiji da kai a kan ciki ko? Ba shine a gabanta ba, abinda yake gabanta wannan ne, ta tabata ko yan biyar maza Fatahiya zata haifa ta riga ta makaro tunda kafin su zama abin alfahari ta gama jigatuwa, ama wannan basamuden mai balagagiyar iskanci da tsiron rashin kunya ko? Ya gama yi mata kaka gida da ya'yan gidan baki daya, ita saima ISHRAT ta shigo ta ci ubanta yau, yarinya sai kunnen kashi, irin yadda take yiwa ƴaƴansu biyaya na ci mata tuwo a kwarya, zata daidaitata ne , dan ba zai tana yiwuwa ta zama aminiya a wajen makiyinta ba!
Murmurshi ne kwonce a saman fuskarta tunda ta buda ledar kilishin nan ta gani
Kanta ta dago dan yi masa godiyar dawainiyarsa a kanta, domin koda ta zamto mahaifiya a gareshi baya hannata yi masa godiya a duk lokacin da ya kyautata mata, sai ta ga a tsaye yake a wajen da ya mike tun bayan gaisheta da ya yi ya ajiye ya mike
Sake tsura masa ido ta yi kafin ta dauke kanta ta ce" Kai zauna mana "
Inda ta nuna masa ya kalla, sai kuma ya zauna yana sada kansa
Baki ta tabe ta ce" Ka leka Hajia ne?"
Kai ya girgiza dan rabonsa da kakar tasa tunda sasafe da ta kai masa maganin baki da na basir ta saka ya sha ta kuma tofe shi da yawu ciki da bai
Baki ta kuma tabewa ta rufe ledarta da kyau ta ajiye a gefe ta ce" Baka da lafia ne?"
Kai ya dago wannan karron ya dan kalli mahaifiyar tasa, sai ya kuma gimtsewa yana ayana yanzu zaka amshi sakamakonka a hannu TAUFEEK tunfa baka tausayin kanka
Mamansa ta tabe baki tana harararsa sama da kasa kafin ta dauke kai ta ce" Kai dilla tashi ka bani waje, bana son shashanci kuma ni ba sa'arka bace da zaka zo har dakina ka min rashin kunya!, Kai in banda iya shege ni zan ringa magana kana yarfawa? Ka kula ni ba Hajia bace kuma ni ba elhaji bace tsaf zan wanke fuskar yaro da mari, tunda dai lafiyarka kalau sarautar da baka gada bace ta motsa sai ka yi, daga nan ka je wajen ubanka yana nemanka kuma ka je wajen HAJIA ka san in bata ganka ba yanzu zata hauro nan ta bi daki daki ta barmu da Allah, ni ka rabani da rikicin da ya fi karfina ka ji na fada maka! Jeka kawai jeka walahi tun muna mu biyu!"
Murmushi ne ya subuce masa a hankali ya sake dago dubbansa yana kallon mamansa, watau ba zai tana yin tsufa da a dura masa ba dadi ba a gaban mahaifiyarsa.........har ga Allah sai ya ji wani sanyi sanyi da farin ciki, hakan ya sa ya dan sake kureta fa kallo ta fitar da kilishinta ta fara ci ya ce" Yanzu Mama dama sarauta ta fi kudi ne?, Ai asalim mulkin kudi ne Hajiar Babanmu"
Dan kwalinta ta turo gaba ta nemi ajiye ledarta,
Yana gannin hakan ya mike da dauri ya fice yana sakin murmushi harda rike hularsa dake son faduwa dan fitowar da ya yi ta dan makalu da kofa
Dakatawa ta yi itama tana yar dariya kafin ta girgiza kai ta karasa wajen wayarta ta daga ta amsa mijinta fa fadin eh ya shigo gayanan zuwa bangaren nasa