← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 116

Sashe 71

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajia ta zagaya gidan gaba ta bude ta shige tana fadin" Mika mata ita mu je, bayanin dan tayin nan ya fi komai tsaya min a rai mu je , sai mun dawo "

Baba mai kwanoni ya yi murmushi bayan motar ta fice a gidan, watau sosai ya yi mamakin mahaifiyar TAUFEEK yau gannin idonsa itace ta yi gaba da lamarin yaronta, ya kuma ji dadi mai girman gaske, sai kuma TAUFEEK din dake hade girar sama da ta kasa na rashin kunya

Sunna isawa asibitinsa kamar yadda dokar wajen take idan har aka kawo daya daga cikin dangin wani ma'aikacinsa, Wada suke da kusanci sosai kama daga mahaifiya, mahaifi, mata, ya'ya to ba za'a duba marar lafiyar da mutumen ba dan gudun rikicewa da sauransu , dokar kuma na kan kowa ne ba iya ma'aikatan ba, har shi mai wajen, dan haka sunna isawa aka dorata a kujerar tura marar lafiya aka shige da ita bangaren emrgency, shi kuwa ya zauna a office din doctern dake aiki a ranar a hankali ya jinginar da bayansa bayan doctern ya fitar masa da ruwan roba ya ajiye masa sannan ya fita da sauri ya tarda abokanan aikinsa dan bata taimakon gaggawa

Cikin ikon Allah a lokaci kankanin aka samu aka daidaita bugawar zuciyarta sannan aka tsayar da zubar da jinin da ta fara , sai dai kukan da take yi sun gaza hannata shi, sun yi iya yinsu dan gannin ta daina kukan ama ta kiya, uwa uba tunda suka daidaita harkar bugawar zuciyarta ya zamto ko me aka zo za'a saka mata sai ta karanta a zaune cir a saman gadon take hakan ya sa ta ki a saka mata alurar barci, abinka da wace take da damar dakatar da su din ne, domin da wani ne gaskiya Bama zai tarki haka ba

Docter Muktar ya dubi Nurse Halima da kula ya ce" Ina ga ki tabo docter, dan kar ya mana fadan cewa a kan me zamu saurari ra'ayinta kin san baya son wasa da irin haka"

Nurse Halima ta fitar da numfashi tana cire safar hannunta ta ce" Ok docter"

Fitowa ta yi da dan gaggawa dan karasawa office din docter Ahmad din dan ta isar da sakonsa, sai dai tana fitowar ta samu wajen dakatawar ya cika sosai, dan kuwa matan Elhaji mai kwanonin sun karaso su dukansu, haka kuma mahaifiyar Yumnar da yayarta wace ta zo gannin jikin mahaifinsu da ya yi yar jinya su dinma sun karaso din, sai dai yannayin mahaifiyar Yumnar sam ba alamun sassauci a fuskarta kamar yadda yannayinta yake

Tunkarar Nurse Halima ta yi , fuskarta a hade hakama yannayinta ta ce" Nurse yaya jikin yarinyata? Ina fatan tana iya mikewa mu je gida?"

Yayar Yumnah dake tsaye kusa da Hajia ta yi gagawar kallon mahaifiyar Tata, 'ya ALLAH' shine abinda ta ayana a cen kasan zuciyarta, shin yaya zata yi da wannan fitina ne? Ama a gaskiya wannan mata da ta kirayi mamansu ta ziga rikicin nan bata yi masu adalci ba, yanzu gashi tunda mahaifiyarsu ta zo ko gaisar da iyayen TAUFEEK din bata yi ba sai fizge fizge take yi har ta saka Hajia gaishe da ita cike da mamakinta, sai kuma ga wata Maganar?

Nurse Halima da kula sosai ta ce" Sorry Hajia, matar Sir ce a ciki, jikinta da sauki sosai sai dai ba maganar tafiya da ita yanzu, ki dan yi hakuri zan je wajen sir din ne"

Da sauri mahaifiyar Yumnah ta dan tareta ta ce" ki dan dakata, ina son shiga ganninta, du wani wanda zai ce wani abu a kanta bayana yake dan nice mahaifiyarta, ina bukatar a bani y'ata na cenza mata wata asibitin!"

Da sauri yayar Yumnah ta matso ta ce" Mama, dan Allah ki yi hakuri ki zo ki zauna"

Rai bace ta juyo tana daga hannunta kusa da ita ta ce" Ke Akilah walahi idan kika yarda kika kawon raini a wajen nan zan dauke fuskarki da mari, in ke baki san zafin Yumnah ba Ni na san ciwon abata idan ba zaki iya ganni ba kauce ki koma gida!"

Wani tsadadan murmushi Hajia Fatahiya ta saki tana sake talabe jaririyarta, hakama Hajia Nuwairah ta dauke kanta tamkar basa wajen

Hajia ta shiga rafka salati tana kallon mahaifiyar Yumnah, lokacin ne kuwa Nurse Halima ta wwucewarta dan ta kula abin na nema ya zama family isu
Hajia ta ce" Ikon Allah, wai kamar wace kike yade yaden magana a wajen nan , Ni wama ya sanar maki da maganar nan ne? Mu bamu isa mu kula da ita bane sai an taso ki? Aure ne fa aka daurawa magidanci Bama shi ya je ya nemi auren ba shine zaki zo kamar kubunuwa kina magangannu kamar wace ke daf da kyatsa ashariya? Allah dai ya sa ba magidanci kike son fadawa magana ba , dan da wahala na iya kawar da kaina kowani shashasha ya wulakanta min jika, da kika ganni nan babu irin fadan da ban gani ba, ke karama ce, in zaki nemi kawo min raini a duniyar magidanci in dauke fuskarki da mari ba wani abu bane a wajena! Ke yau ga salamamiya, an yiwa yar taki kishiya kuma ubanda ya kirayeki ko waye ya kuka da kansa, ai ji ji zaki yi dan ba abin a boye bane, yaro kuwa da kudinsa da lafiyarsa akoy wanda ya isa ya tsayar da shi a daya kwalin kwal ? Ai hudu cifff zai jera maki gani ya kauda idannuwansa!"

Hankali tashe Akilah ta karasa tana kokarin riko hannun Hajia ta ce" Hajia, dan Allah ki yi hakuri, duka abin nan an samu rashin fahimta ne, irin yadda aka sanar da momynmu maganar auren da rashin lafiyarta ne ya tayar mana da hankali, ama ba maganar wulakanta TAUFEEK,, itama momy ba zata yi haka ba , an riga an zama daya ai du wata fitina ana fatan Allah ya tsare ta, aure kuwa ai nufi ne na Allah dan ya yi aure ai ba shine damuwar ba in dai mutuniyar kirki ce fatanmu Allah ya hada kansu ya bada zaman lafiya............"

Magana Akilah ke yi da dukkan gaskiyarta, burinta ta katse fitinar da take gannin na kokarin Kunno masu a tsakaninsu, bayan ita fitina farkonta aka sani ba'a san karshenta ba, kuma ko ba komai a duniyar hausawa ake kuma musulmai, idan har aka yi duba da irin yannayinsa bata san lafiyarsa ba ama a tsarin dukiya da yannayin nasabarsa tara mace hudun da kakarsa ke ambata ba laifi bane, dama an umarta a yi idan za'a iya kula da su a fita hakinsu ne, a nan bata ga abin rikicin nan ba, abinda ba'a yiwa kanwarta adalci ba daya ne tak, shine aka yi ba'a sanar mata ba, dole ne a ji ba dadi, ama idan rai ya bace hankali ya tashi sai a yi shiru a yi ta ambaton sunnan Allah sai ka ga komai ya zo da sauki

Tana rike da hannun Hajiar wace ta zuba mata ido tana kallonta alamun jikin Hajiar kamar ya fara yin sanyi jin kalaman Akilar suka ji an fizgo Akilar, basu yi wata wata ba suka ji dauke fuskar Akilar da zazafan marin da ya saka MAMAN TAUFEEK dago kanta daga wajen da take kallo tana jan carbinta irin na jikin yatsar nan fari kal mai yar kyalkyali a jikinsa ta sauke dubanta a kan su gaba dayansu, daidai lokacin ne kuma TAUFEEK ya karaso, ya dan samu tsaikon isowar ne sakamakon rigar aikinsa da nurse Halima ta je cen sama office dinsa ta dauko masa da takalmin aiki da Safar hannu da abin auna awon zuciya

A nutse yake karasowa, idannuwansa a kansu baki dayansu, tun daga kan iyayensa har na matarsa

A hankali ya sauke dubansa a kan Akilah, wace ta dafe fuskarta kanta a kasa tuni hawaye ya fara wanke mata fuska, a haife ko Akilah ya girma bale Yumnah, sai dai a yadda take mutuntashi yakan ce mata auntynmu , itama sai tace da shi yayanmu dan girmama junna

Kai ya dauke ba tare da ya iya cewa kowa komai ba ya ratsa su, cike da kamala da yannayi irin na baban likita ya shige ciki, hakan ya sa gaba daya suka bi shi da kallo kowa na ayana abinda yake ayanawa a ransa dangane da dan uwansa a kan TAUFEEK din

Yana shiga dakin ya karasa wajen allurar da docter Muktar ya haɗa ya amsa a nutse ya karasa gaban gadon nata ya janyo kujerar dake gaban gadon ya zauna sannan ya zuba mata ido bayan ya dauki audugar da zai yi anfani da ita dan yi mata allurar tunda ba karin ruwa ta yarda aka jona mata ba

Numfashi ta ringa ja tana kallonsa, kallo irin kamar ta ga wani maciyin amana, dubansa take yi kamar wace ta ga bakinta, tarin hawayen da ya cika gurbin idannuwanta kuwa na masa nuni da tashin hankalin dake saman harshenta, sai dai tarin firgicin da ya sameta, da irin yadda ya kasance mai tasiri a dukkan motsinta ya hannata iya budar baki bale har ta masa rikicin da take jin tana iya yi masa a kan maganar da ta gama yankewa kanta ko ita ko wace ake nufin an aurawa mijinta!

A hankali ta budi bakinta gannin ya kama hannunta ya daura yar igiyar da zata bashi damar samun jijiyar da kyau sannan ya rike audugar a nutse ya goge bayan hannun nata, ita kuma ta budi baki ta ce" Yayanmu, dan Allah ka ce min ba zaka iya amsar auren nan ba, na san ba son ranka bane, kana da damar sakin............."

"Yumnah" ya fada a hankali, cike da fitar da amon da ya fi kasarata, ya tsare idannuwanta da manyan idannuwansa, a dole ta sauke dubanta kan sajensa domin kallon ya matukar mata girma
Chapter 71 · 0% Book details