Sashe 62
Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
KHausar ta ce" A'a mama, yau din ai bani da wani aiki dama saloon zan je da wuri na koma gida na samu kiranki, gashi Maman ta fita itama da ta sama min wani abin na zo da shi sai kawai na sayo faro, bari dai in amso abincin"
Daga haka ta karasa kusa da shi sosai ta ce" Bani katin"
Tunda ya dinke bakinsa kasa kasa Hajia ce yake makawa harara tana maka masa, sai yanzu da ta wani tsaya masa a gaba
Aljihunsa ya laluba ya ciro katin ya mika mata da dan mamaki ya bi hannunta da kallo wanda ke dauke da kunshin da bai san da shi shekaran jiya ba
Kai kawai ya girgiza a ransa yana ayana' amare Kennan, dole a ringa kwaliya, dole ki tsirarwa kanki abubuwan da ba zasu fisheki ba, wai nine kike boyewa aurenki dan kawai na boye maki aikina???'
Zancen zuci yake yi, tsakaninsa da Allah sam bai san a me ya dora idannuwansa ba har wajen sai ido hudun da HAJIA ta juyo suka yi bayan ta raka bayan Khausar da ido ta wani dage gira saya sannan ta saki wani murmushi ta ci gaba da jan carbin da sam bai yarda da addu'a take yi ba wannan tsohuwar mai kwanonin
Kai ya dauke yana girgiza kai sannan ya mike ya bi umarnin Maman da tace ya tafiyarsa office dinsa hakan zai fi alkhairi dan baya so yana zaune gefen uwar mutane tana nemansa da fitina gaskiya ga ma'aikatansa ma ko sun durfafo da karfi karfi in suka ganshi sai ka ga sun shiga kame kame kamar wani dodo, KOWAMA haushi yake bashi yau din dan haka ya yi tafiyarsa
A kadan sai kusan goma matar Mai kwanoni ta sauka, ta samu baby girl dinta
Sai a lokacin Khausar ta nufi office dinsa dauke da ledar abincinsa da bata samu ta mika masa ba tunda ta zo da na su Mama
Knoking ta yi ta kama abin ta bude ta shigewarta da salama da kuma sakin fuska sosai ta karasa wajen office din ta ajiye masa abincin da katinsa tana kallonsa ta ce" Hajiar fa ta sauka kana office TAUFEEK ka sauko ka ga baby girl mai kyau da ita Masha Allah"
Yi ya yi kamar bai ji mai take fada ba yana ta rubuce rubuce a baban litafin dake gabansa
Dan dage ta yi ta ga aiki ne yake sosai, dan haka ta ajiye ta masa salama ta fice
Sai da ta fita ya dakatar da rubutun da yake yi a hankali ya jinginar da bayansa jikin kujerar nan ya lumshe idannuwansa
Tabbas ya san bashi da lafiya, zai kirayi docter ta dauki jinninsa may be rashin isashen hutu ne ke neman sakashi kwonciya
Khausar na tare da ahalin gidan mai kwanoni har aka salame su daga asibiti
Mota uku suka cika har ita suka nufi gidan domin dangin Hajiar sun fara halarta summa ta ko'ina, baby dai gata dangi na maraba da ita ama jikin uwarta du ya yi sanyi tamkar ba karuwa ta samu daga Ubangijin talikai ba wanda shi ya isa fitar da na kirki tsakanin mace da namiji, yana iya baka namijin ya zamo baban tashin hankalinka duniya ya kuma kaika wuta gobe kiyama, yana iya baka macen ta zamo itace jin dadinka mai jin kanka duniya da kiyama, har ta manta karin maganar da a haifi gwama gwara a haifi matar gwamna, ta gagije ta hade rai ko magana da kyar take yi, uwa uba abinda ta so bai samu ba cewa sai dai kishiyoyi su ga ta haihu, haihuwa mai dadi sai da ta tara mata kaf kishiyoyin ya zamo sunne suka kaita asibitin mijin yana gida yana hutawa dan ba dan fari kuma dan da bai taba samu za'a kawo masa duniya ba, ya zamana itace a ragaya itace a mumunan halin da ta saka zuciyyarta dan jin dadi, kamar zata mutu haka take ji saima idan ta bi Mama da kallo ta ga yadda take car car da ita kamar wace bata girmeta ba, dan kuwa ba zaka ce ta haifi taufeek ba, haihuwa daya haihuwar ta tsaya sai gayu da kanshi ke fita du inda ta tsaya tana walwali ita ga uwar dan masu gida ko?, Ba zaka taba cewa ta girmeta nesa ba kusa ba dan kuwa ita HAJIA yarinya ce haihuwar nan itace ta fari amarya take a gidan mai kwanoni cike da burika nata na kanta masu zaman kansu, sai fatan Allah ya bata Sa'a
Sai da suka gama ajiye mata kayayakinta sannan suka wuce bangaren Hajia, Hajiar cike da mamakin Yumnah ko a leke ko kafarta ba'a gani ba a yanzunma ? Uhum....
Fira suka sha , KHausar cike da jin kunya domin HAJIA gyara zama ta yi ta saka Mama a gaba wai du abinda ya dace na yi a rubuta masu su fara zuwa kasuwa, ita saima da ta sha mamakin Kennan dai maganar aurenta dai da gaske ne? Mahaifinta yace mata da izinin ubangiji ya yanke aurenta nan da kwana goma, kai sai take ji wani iri, wai ita KHausar? Ashe dama mijin nata a bayan gidansu yake bata sani ba?, Allah mai hikima bata da abin fada sai hamdallah
Bata tashi tafia gida ba sai da yama ta yi sosai domin har sai da ta haɗawa HAJIA yar tsala ta toya suka ci abinsu harda Mama sannan maman ta saka direba ya kaita har gida sai godiya take mata, HAJIA kuwa fadi take in sha Allahu gobe zasu je su ciro anko ita da TAUFEEK, ita kuwa daria kawai ta yi abinta tana tunanin HAJIA da rigima ina ita ina tisa Taufeek cirar anko? Cap itafa tunda ta san waye shi take wani kiyaye wasu abubuwan da a da kai tsaye take masa
Koda ta huta sosai wayarsa ta gwada kira dan ta sanar masa da kanta domin ta san in HAJIA ta ji yanzu zai ji, ita kuma haka kawai bata so ya ji daga bakin wani, tana so ta ji irin murnar da zai yi, tana matukar so ta ji irin farin cikin da zai nuna , hakan nema ya sa har ta kusa shiga barci tana neman layinsa , sai dai cikin ikon Allah Sweet off ake fada mata, karshe dai haka ta hakura ta nemi na Salis , sai dai shi kuma tana ta ringin har ta katse bai daga ba , a dole ta yi kwonciyarta da nufin gobe asabar in sha ALLAH tana da isashen lokacin hutu da gyaran jikinta da kuma neman wayar TAUFEEK din , Salis kuwa ta sani ne a yau din sai ya nemeta dan haka ta kashe wayar ko zata samu isasshen hutu dan ta san in dai ya ga miss call DINTA zai kirayeta ne ya tsareta da firar dare
Wasa wasa lokaci matsowa yake yi, lokaci da wuyar zuwansa saka shi ne dama, haka kuma cikin ikon Allah Mama ce da kanta mahaifiyar TAUFEEK ta yi kiran KHAUSAR cewar ta dakata da zuwa wajen aiki har a daura auren nata wanda dududu abinda ya rage kwana uku ne kawai, sai take ji kamar fa wannan din da gaske zai tabbata ne
A kulun zata tashi ne cikin tarin fargaba da tsoro da faduwar gaba, bale a yanzu wayarta da Salis ta rage sosai ya zamtoma itace zata yi kiransa kulun idan ya daga kamar wanda yake cikin ɓaci ko busy kulun yana da uzurin da zai gabatar mata da nuna mata zai tabota ya katse kiransa hakan ya sa zuciyyarta ke cikin tarin zulumi da tsoro har take tashi tsakiyar dare tana fadawa Allah take kuma daukan azumi kan koma menene ke damunsa Allah ya sa ba na daina aurenta bane tunda dai zuwansa da farko farko ba haka yake ba
Ana saura kwana biyu Hajiya ta yi wani zuwanta gidan suka dinke da Mama a daka , sai da yama sosai ta juya gida da tarin kyaututtukan da suka saka KHausar fashewa da kuka cike da gannin kokarin mutanen ta ringa yi masu Adu'a da tunanin koda bayan aurenta ne rabasu zumunci da mutanen nan da ita ba zai taba katsewa ba, abinda ya karra daga mata hankali kwana biyu saura a daura mata aure ama bata da labarin Taufeek, ta yi kiran, ta bar msg ama shiru, ko yanzu ta tambayi HAJIA sai take ce mata aiki ne ya mukemuke shi dan suma rabonsu da shi a yi fira ta gwa da gwa har sun manta, sam basa samun lokacinsa , duda haka dai ta so ta sake damun kanta da tunanin duba da bai taba share sati cirrr bai zo gidan nan ba, ama gashi har yau kwana takwas ba shi ba labarinsa? Gashi an kusa fara tafia HAJI , ta yiwuma har ya tafi bata da labari
Da dare bayan Aba ya dawo da auta an dan taba fira Aban ke sanar mata wani sabon cenji cewar ba zata dauki dogon lokaci zata tare ba wai mahaifin mijin nata ya nemi alfarmar ta tafi gidanta da wuri , wannan ya sakata shiga hali irin na kimtsatsun amare, ba irin amarenmu na zamani ba da za'a masu auren sai dai su maka kiba su yi bulbul da su, maimakun su ringa zugewa saboda zulumin rabuwa da iyaye da tunanin sabuwar rayuwar da za'a je a tarar a gidan mijin, wanda in dai yarinya budurwar take dole tana cikin zulumin abubuwa da yawa masu firgita zuciyyarta
Tarin fargaba da tsoro ya sakata da safe neman izinin zuwa gidan yan uwanta, wanda tunda aka yi auren
kannen nata bata taɓa zuwa gidajensu ba dan kuwa takan ce in dai ba halin rashin lafiya ba ita din bana ce na zata je gotai gotai yin komai gidansu ba, sai dai su su zo gida lokaci zuwa lokaci dan su dinma Aba ya Hanna zuwansu koda yaushe yace su yi zamansu a dakunnansu su yi ibada