Sashe 29
Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yauma TAUFEEK ya cika dare sosai, domin ya shantake a wajen abansa ne sun sha hira daga nan kuma ya je wajen Hajia ta gama masa turare turarenta wanda a dole sai da ya je ya yi wanka ya cenza kayansa domin a tunaninsa bangaren Yumnah da baki ba zai je haka yana kauri uwa dan bori ba
Yau dinma da hannunsa rike da tsaraba ya karasa bangaren nata
Sai dai abin mamaki tunda ya tura ya shiga da salama ya fahimci yau din kamar ita daya ce ba bakinsu
Du irin yadda ranta ke bace da gannin rabonsa da ita tunda safe da zasu wuce gaishe da iyayenta da abokansa sai yanzun, ama ganninsa ya saka ranta yin fari, harma ta mike tana murmushi ta nufo shi dan amsar ledar hannunsa
Da dan mamaki ya bi shigar jikinta da kallo, riga da wando ne a jikin nata masu tsarin santsi da dan lafewa a jiki kadan, domin idan ka saka su zasu bi tsarin jikinka ne su lafe
Dauke kansa ya yi a lokacin da ya tuna cewar ai normal ne yanzu mijinta yake dan an tarbeshi a haka daidai din kennan
Yana zama saman kujerar falon yana dan waigawa dan maganar da ya dauka yana fadin" Ina bakin ne? Ko sun kwonta da wuri haka?"
Agogo ta kalla bayan ta dauko farin tawul tana dawowa da jug din jus mai sanyi a hannunta ta karaso tana sakin murmushi a ranta ta ayana' Yar banza ce ni zan zauna 8na zubawa karti ido sunna wuni sunna cikan kunne da iya shege bayan ga dalilina a gefe kunya ta hanna shi tarewa da ni?, Bama zai yiwu ba gaskiya ' a bayane kuwa cike da fitar da harufa a tausashe ta ce" Ai dama kwana daidaya ne zasu yi , kusan magariba bayan sun gama girki suka tafi"
Murmushi ya yi yana amsar jus din da ta zuba masa ya dan kurba kadan sai kuma ya bita da mamaki gannin ta duba ta kamo kafarsa zata dora saman cinyarta
A hankali ya ajiye kofin ya mika hannayensa biyu bayan ya janye kafar tasa yana kallonta da kula sosai ya ce" Hey, yumnah me zaki yi haka ne?"
Yumnah ta zubawa fuskarsa ido, cike da tarin kaunarsa ta ce" safar zan cire maka mu je ka yi wanka sai ka ci abinci Yayanmu"
Dan murmushi ya yi, kwarai hakan ya birge shi, sai dai a tunaninsa a yanzu shine zai fara riritata, ya bata daraja irin nata, ya nuna mata ita din mace ce, koda zai iya amsar irin kula daga gare ta, dan ba zai tashi zikin kato ya sakata irin wahalar nan ba tana amarya, lada ne ai yanzu suka fara ratabarsa, in sha Allah
A hankali bayan ya yi wani yannayi da bata taba ganninsa ya yi ba, yannayi irin na tarin a ji kunyar nan, domin TAUFEEK nata wanda bai cika dogon kallonta bane a yau ya bi rigar jikinta da kallo a hankali ya ce" Na yi wanka ai, sai dai zan so na maki idan Allah ya sa baki yi ba"
Ya salam, tabas maganar ta zo mata s ba zata, shi yasa ta wani irin tsare shi da ido cike da mamaki da tunanin shine ya yi furucin nan? Sai kuma wani madaukakin dadi ya nemi rufe dukkan gaban jikinta da yannayinta
A hankali ta dan lumshe idannuwanta sakamakon jin hannunsa a saman habarta ya dan murza kadan, baban burinta ta sake ce masa eh tana so ya yi mata wankan, dan irin rayuwar nan ita take hangowa kanta da mijinta dama, su zamto tamkar abu daya komai nasu iri daya
Ashe ashe zata iya jin furucin nan daga bakinsa bayan tsoro ya gama mamaye ta cewar wata ta gama yi mata karuwar alaka da miji?
Murmushi ya saki , duda a bayane ba zai ce asalin kunya bane ya cinye harshen Yumnah ba, ama daukewar maganarta ya saka shi daukan cewa hakan ne, dan haka ya ringa jin wani sauki sauki a zuciyarsa, domin shi dai da Allah ya halice shi mutun ne mai matukar son mace mai kunya, yana so a rana irin ta yau da wa'inda zasu biyo baya ya zamto ya yaki kunyar amaryarsa , ya koya mata irin yadda ya fi so su kasance cikin koyarwar islama, a duniya ya tsani rawar kai, da shegen banzan yayi irin na wasu matan da mazan, yakan dora laifin haka a kan Mazan ne domin da ace namijin ya nunawa macen yadda zata daidaita lamuranta to da kunya ta zamto ado a motsinta, yana matukar son koda zawara ya aura a yi yayi irin na jin kunyar junna, wasu abubuwan kuwa yau da gobe suke zamtowa dole a saje, ama wasu matan har su mutu akoy yare mai daraja mai sunna kunya a tsakaninsu da mazajensu, dan kuwa du irin sabawar nan da tarin haihuwa wace ke nunin du wani sirri mai sunna sirrinta ya gama sani ciki da bai zaka ga wasu abubuwan a bayane suke na kunya har ana iya gani, shi din da kansa hakan naniya kasancewa nishadi a gareshi, domin yana iya daukan hakan abin tsokanar iyalinsa idan ya yi ta labe fuska ko ta yi shiru ta sada kai, to fa sai ka ga yana dariya a bayane ......., Yana matukar girmama darajar iyayenmu , ba wai gyaran bane ba'a yiwa maza, ba kuma kanshi bane ba'a shaka masu, uwa uba babu wa'inda suka kaisu iya kirsa da sada kai, kai sun fi yan matan iya juya akalar namijin cikin nutsuwa domin su sunna dauke da wani sirri da suka yarda da shi cewa eh a maganar gaskiyama namiji shine shugaba, a kuma maganar hanyar da zasu iya bi su sace zuciyarsama su nuna masa cewar shi din ne dai shugaban, ko magana ta hada su ta rashin fahimta sukan shanye a lokacin su bada hakuri ba dan sun kyale ba, dan kuwa sunna da nasu hanyoyin nuna maka kaime ya dace ka bada hakurin nan fa, harma ka shiga bayarwa ba tare da ka gane hakuri kake bata ba..... Abubuwa ire iren haka dai, shi shine burinsa, shine muradinsa, muhali yake so da rayuwa cike da kula da kare hakoki irin na adininsa da kuma al'adar malan bahaushe, ba rayuwa irin ta turawa ba ............
Da wannan tunanin ya mikar da ita suka karasa wajen diner ya ja mata kujera ta zauna sannan ya ja ya zauna yana dan sakar mata murmushi a lokacin da ta mike tana kokarin zuba masa abincin
A nutse ya ce" Kadan zaki saka"
Ta kuwa zuba kadan din, sannan ta zuba natama dan kadan sosai, dan ta riga ta ci tun kafin ya shigo, an fada mata cewar kar ta ringa hadama a gabansa
Da kula a lokacin da ya fara ci ta ce" Na zata zaka shigo da wuri yau?"
Bai bata amsa ba sai da ya gama cin abincinsa a nutse domin dama ba yinwa yake ji ba, ama gudun kar ya shiga hakinta ya saka ya amshi abincin
Da kula ya dubeta ya ce" Eh na dan yi wasu uzuririka ne, ama da wuri na shigo daga gidan su KHausar"
Cokalin dake hannunta sai da ya kusan fasa plate din da take dan cacaka sanadiyar caka shi da yan yatsunta suka yi da dan karfi
Hankali a dan tashe ta ce" Khausar kuma?"
A hankali ya dan bi yannayinta da kallo
Idannuwanta ta kikifta tana fadin" Me ya jadaka da gidan su KHausar yanzun kuma?, Bayan gani? Ina tunanin a yanzu ai ba Khausar tsohuwar mace ba ko yarinya sabon jinni ce ba zaka kula ba tunda kake da amaryarka a gefe sabuwa fill ko? A tunanina zuwa yanzu ko Khausar ta yi kiranka ba zaka amsata ba tunda gani ko?"
Ba da hatsaniya ko ihu ya yi furucinta ba, dan bata taba yi masa magana da ihu haka, tunda ta taba kwatantawa ya nuna mata aa, ba zasu fara haka ba, take kiyayewa,
Sai dai ko a hakan a bayane tsagwaron tsanar sunnan wace ta yi magana a kanta ya bayana ba a rufe ba
Da mamaki yake kallon fuskarta da ta dauki ja nan da nan
A hankali ya kai duban nasa kan hannayenta da take aukin murzawa kamar zata fitar da yan yatsun daga jiki, alamu na a haka din tana dane kanta ainun daga abinda ke zuciyarta
Sosai mamaki ya cika masa zuciya
Me ya hadata da Khausar mai zafi haka?
A sanninsa sunna matukar jituwa tsakaninsu, dan sha nawa zasu samu matsala ita da shi ta samu Khausar din da maganar ita kuma ta ce sai a shirya , ya yi hakuri kuwa su shirya din?,
Khausar dai Khausar dinsa ce take nufin a yanzu dan ya aureta du wata alaka zata kunce tsakaninsa da ita?
Tana nufin ko wata aka bashi kennan ya mu'amalanta ko mene? Subahanallah shin yarinyar nan bata da wayo ne ko akoy wata a kasa tsakaninta da Khausar?
Idannuwansa ya lumshe a hankali yana mai aro nasa yannayi idan ransa ya baci gudun kar ya yi abinda zai iya zuwa ya dawo, watau yin shiru wa abinda ya bata masa ran, rashin tankawa a lokacin har sai ya ji zuciyarsa ta yi sanyi
A hankali ya mike da tissu a hannunsa ya wuce ya barta a nan zaune ba tare da ya ce uffan wa maganarta ba
A rikice ta juyo ta raka bayansa da kallo har ya bacewa ganninta, sai dai abinda ya dan sanyaya zuciyarta ba waje ya fita ba, aa, ciki ya shige ta hanyar hawa sama