Sashe 33
Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsintsiya da abin gugar da aka miko mata aka nuna mata wajen mai kunnar dake yashe shima ana duduba shi cewar maza ta je ta kimtsa wajen dan ya bata shi ta rike jikinta na rawa hancinta na jin karnin jinni, idannuwanta na kallon jinni da ciwo, tun tana iya jurewa wajen wanke gadon har abin ya kai wuyanta ta shiga sheka amai tamkar zata amayar da hanjin cikinta, sai dai abin mamaki masu jinyar mararsa lafiya kawai suka iya nuna mata kamar sun damu, babar likitar nan aiki take ba kama hannun yaro ana ta raraba mararsa lafiyar har sai da ya zamto ba kowa a dakin na farko ta juyo kanta ta kama kafadunta ta mikar da ita tsaye tana kallonta cikin ido ta ce" Sai fa kin kama jikinki, sai kin wanke idannuwanki, dan inda aka kawoki ana kaunarki aka kawoki, domin nan ba zaki fita ba sai kin goge iya gogewa a aiki, ama fa kin ga rama? Sai kin rame, sai hankalinki ya tashi, domin wani abin idan kika gani zaki sha kuka kamar ranki zai fita, ki jure kawai , ki jure kawai haka aikinki ya gada, ki gama wanke jinin nan tas, ki shiga dakunan cen biyu summa ki wanke sosai su fita sai ki zo cen wajen office din Samira ki tsaya ki yi pansema"
Daga haka ta wuce ta bar Khausar daga ita sai ita a dakin nan
Ido du a waje hankali a tashe
Du yadda ta hasasowa kanta tana iya haduwa da tashin hankali abin ya zarce haka, tun tana gane yannayin lokaci har ya shige mata ta daina fahimtar dare ya yi ko har yanzu a cikin wunin ranar ake
Juwa ke dibanta du idan ta motsa ama ta gaza zama bale ta kwonta
Yinwa take ji tun bayan yin amanta, ama a hankali yinwar ta disashe ta daina jinta
Idan ta ga an nufi sallah sai ta je ta yi a irgenta sun gabatar da sallar isha ama shiru ba'a salameta ba
Ido ya gama yi mata zuru zuru ya mutu murus kwalin da ta saka du ya jeme da kukan da ta yi
Tun tana tunanin ranar zata kare ta tafi ko ta daina irga gawa har ta dawo idan ta ga an rufe sai ta yiwa mamacin addu'a a zuciyarta, ama idannuwanta sun gaza daina kuka
Tana tsaye, kaffafuwanta sun sage, tana tare da wasu likitocin da take masu kallon kamar wa'inda basa jin komai a gaban jikinsu kamar ba mutane ba? Sunna kai kawonsu ba alamun gajiya a tatare da su tamkar su din basa jin gabai na jikinsu
Ita dai bata ga lokacin da suka tsaya cin abinci ba, dama dama dazun da 5a shiga sake wanke fuskarta ta ga wani namiji a tsaye yana tura wani abin a bakinsa ama bata san abinci ne ko menene ba
A yanzun da suke tsayen ta gama yankewa cewar a yau fa ta yiwu karshenta kennan kanta a kasa ta ji Hajia Rauda na magana cewar ta dauko hijabinta ta tafi gida, kar ta manta gobe karfe takwas na safe ya mata a nan idan ba haka ba zata hadu da punichment mai tsauri, sannan ta tafi da takardar rubuta dalilin yin latinta yau
Bata taba tsamanin idan akace Khausar jeki gida zata ji kamar ance Khausar shiga aljannah bane sai yau
Wani irin salama da zazabin dadi ya sauka a zuciyarta
Irin yadda take sauri ta nufi office din ta dauko baban hijabinta ta saka a saman kayan aikin ko takalminta bata tuna ba bale ta cire rigar da aka bata ta saka ta yi aikin
Salama ta masu ta fice tana tunanin ai bama zasu kuma ganninta ba bale su kasheta, Hajia Rauda kuwa ta yi murmushi a ranta ta yana' Ta yiwu da gangan chef ya turoki a lati dan ya ga yadda zamu maki, na tabata in kika fada masa zai yarda cewa muna aikinmu ba shiririta muke yi ba'
Da sauri ta fito daga Emrgncy din ita kadai sai shasheka take ta shiga tunanin abin hawa
Idonta idon mai tsaron kofar nan sai ta ga kamar wanda ya yi murmushi, tuna cewar murmushin me zai yi ya sakata dauke kanta a ranta tana tunanin yinwar da ta fara tuna mata cewar akoyta fa ce ta fara sakata gani gani a hanya
Ta fara tafiyawa kennan wata watsetsiyar mota ta parker gabanta kadan
Niyarta ta dan dakata motar ta wuce sai ta nemi abin hawa sai gannin Aisha ta yi ta fito daga motar tanna yar dariya hadi da fadin" Likita bokan turai, Aunty an fito?"
KHausar ta dan zuba mata ido, ta kifta a hankali tana kallonta , murya a raunane ta ce" Aisha kece?"
Aisha ta yi mata wani kallo jin tana tambayarta ko itace, sai kuma ta kamo hannunta ta janyota tana fadin" Zo mu je, yaya TAUFEEK ne ya zo daukarki, tun dazun Baba ya kasa hakuri ya tabo shi, shine ya je ya kwatantawa Baba yanzun fa sai an yi hakuri dole an jure , wai harda gadi zakina yi akace ko me? Kingama sai da muka biya butique din nan baba muka siyo maki hijabai masu yawa walahi wai a saman rigar aiki ake sakawa inji shi"
Bude mata gaba ta yi tana mata alamun ta shiga mana, Khausar ta bude baki murya na rawa ta ce" Aisha yinwa nake ji" sai ga hawaye sharrrrr sun fara bin kumatunta
A hankali TAUFEEK ya labe fuskarsa yana sakin murmushi
Aisha kuwa da mamaki ta ce" Kai aunty, dari uku fa kika zo da ita ai ya ci ace ta isheki , Mama fa ta ajiye maki doyarki "
Khausar ta samu ta shiga motar da kyar tana share hawayenta ta ce" Ni nama manta da kudin nan, kin ga abin hawa ne fa nake nema idan na je Aba ya biya, ba zan iya wannan aikin ba, a yau wankin jinni na ringa yi da gadajen da aka rasu, Aisha rasuwa biyar aka yi a gabana ana rufewa ana fita da su, Aisha an yi karaya kashi a fili aka hade aka dinke ina kallo, tunda na shiga ban zauna ba a tsaye nake, ko ruwa ban sha ba babu wanda ya bani, ki duba ki ga yadda jikina ke rawa, idan na yi sati a wajen nan ni na san ramar da zan yi ko mai cutar s wanda baya daukan magani sai ya fini kyan jiki, walahi TAUFEEK ba zan iya ba, sai in mutu, kamar wanda suke jirana? Kamar wace na masu laifi, wai dan na zo a lati ka ga harda takardar na cike dalilin zuwana a lati bayan ba laifina bane, TAUFEEK ba zaka taba iya aikin Asibiti ba, na rantse maka sai ka summa kai da baka son wahala ko ta rana ce bale irin wannan, TAUFEEK gawa gawa kamar me, ashe haka ake mutuwa? Kai da baka saba ba ai na san bama zaka iya ba"
Da kyar ya iya hanna kansa dariya, bale da take hawaye ka'in da na'in
Ceinduith din da ya siyo ya juya ya dauko ya miko mata da ruwa ama ba masu sanyi ba masu dumi dumi yana gimshewa kadan ya ce" Amshi dan fara shan ruwan kadan sai ki ci"
Ruwan ta dan rike, jin bashi da sanyi ta dube shi fuska har yanzu a raunane ta ce" Besty, ruwan ba mai dan sanyi sanyi?"
Kai ya gyada mata sannan ya tayar da motar dan karma tace zata sayi mai sanyin , a irin yadda cikinta ya shaki abubuwan da bata taba shaka ba in ta fara shan ruwa mai sanyi da yawa zata sha, in kuwa ta sha da yawa cikin zai kule ne ya kama ciwo
Haka ta ringa tura abincin nan kafin su karasa gida
Sunna zuwa ya dubeta fuskarsa ba alamar dariya ya ce" Gobe, idan Allah ya kaimu ki shirya da wuri ki tafi a kafa, jikinki zai saba ne da wahalar , ba maganar wai kin daina zuwa kin fahimta"
Da mamaki take kallonsa, shi dan bai ji abinda ta ji bane, koda yake dama haka zai ce mana shi da shine ta tabbata bama zai iya tsayuwar minti ashirin ba , tsafma zai ajiye karatun asibitin tunda dama su suke so ya yi ba shi yake so ba
Motar ya kunna yana sake dan haske ta Mujahid dake parker ya mata alamun ta fita mana
Fita ta yi tana turo baki ta yi baya kadan har ya tayar ya yi gaba
Harga Allah bata gane motar waye gaba da gidan kadan ba sai da ta tsinci murya kasa kasa da tsayinta haka ana fadin" Watau Motatace ba zaki shiga ba sai ta Elhaji TAUFEEK? Khausar wannan kawance da Elhaji TAUFEEK zan iya rabashi kuwa? Ina nufin idan kika zama matata kin san ai ko magana haramta maki zan yi da shi tunda ba muharaminki bane!"
Da zafi zafi yake maganar, har kamarma yana huci gaskiya
Da farko tsoratama ta yi, sai da hasken farin wata ya dale mata sankonsa ta yarda cewa shine
Dan rage tsayinta ta yi tana gaisar da shi, da kula sosai da mutuntawa ta ce" Yah Mujaheed barka da warhaka, ban san zaka zo yau ba ai"
Baki ya dan tabe cike da kishi ya ce" Yaya zaki yi ki sani kin kashen waya ama k8n kunnawa Elhaji, Khausar gwarama ki ba maganata mahinmanci , ko dai ke din ba matar karamin mutun irina bace?"
Mamaki madaukaki ya kamata, wai me yake damun bawan Allahn nan ne yau? Ji fa wasu magangannu kuma fisabililahi, me yake faruwa da shi ne haka?, Gajiyar dake tare da ita kadai ta isheta, kanta ciwo yake yi haka gaban jikinta, dan haka a tausashe ta dan sake risinawa dan bata son tana saman nan yana kasa walahi, ta fi so ta ringa rage tsayinta sosai in dai zasu yi magana ta ce"
*ALLAH BAI SAUKAR DA CIWO BA SAI DA YA SAUKAR DA MAGANINSA*