Sashe 59
Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kashhh alkur'an sai da ta ji salama a birnin zuciyyarta, harda sau dan yin dage dan tana so ko kafadarsa ne tsayinta ya kai ko a yi magana ta sako da sako mana, ama a haka kamar abin ya fara haramta matsewar wajen, duda ba jikinsa ke gogar nata ba, ama kuma hucin junna da suke shaka ai ba halal bane!
Dan murmushi ke son kubce mata ta wani dage gira ta ce" Jan baki Kennan , haka sunnansa" gaba daya tana kokarin manta fushin ta da bacin ranta da ta kunsa a kansa, har ji take kamar zata saki murmushi dan sunna zantawa haka
Baki ya tabe ya laluba aljihunsa yana janyo dan karamin tissu fari Kal kal ya dan nufi bakin nata da shi a hankali ya ce" Khausar kwaliya bata maki kyau , ki daina, kuma kin ga shigar nan itama sam bata yi ba kin ji?"
Har zafi zafi leben nata ya fara mata ta saka hannunta tana rike nasa a hankali ta janye tana ta kokarin dan jan yaji kadan dan zafin da leben ya fara, a hankali ta ce" ka daina zafi zan tsotse abina, TAUFEEK kaine fa baka son kwaliya , Ni YANZUN ai kaunarta nake, kuma ka ga Salisma yace ashe haka nake da kyau, bai taba ganin doguwar riga ta amshi mutum ba sai a kaina........" Sai da ta karashe wai kuma kunya ta kamata, da sauri ta rufe idannuwanta ta bi ta kasan hannunsa da ya dan dafe kofar da shi ta tafi wajen kujerar nan mai tsayi lafiyayiya ta zauna tana murmushi cike da jin kunya dan wollah maganar nan ta bata kunya, batama san cewa ta yarda wani ya ji ba sai gashi tana fadawa TAUFEEK
A kala ya dauki minti daya a tsayen nan yana mamakinta, what? Har irin maganar nan take yi da wani bakon rayuwarta? Ya Salam!
Wajen ya karaso ya zauna ya bi irin zaman da ta yi da kallo ya ce" KHausar, har wannan maganar kike yi da katon banza?"
Da mamaki KHausar ta dago tana kallonsa ta ce" Taufeek salis din ne katon banza?"
A kure ya ce" To ƙatuwar banza ce?"
Khausar ta girgiza kai da sauri, sai kuma ta dan matso kusansa sosai kamar yadda takan yi idan zata masa magana mai mahimmanci ta ce" TAUFEEK, yana so na fa sosai, maganar da nake maka a yau dai Inaga zasu gana da mahaifinsa da Aba, yace aure yake so kafin ya yi tafia yake so a daura shi, kuma nima ina sonsa sosai ai"
'Dan Allah ki ringa tauna maganar bakinki haka!, Ke yanzu daga zuwan mutun rayuwarki har kike magana irin wannan da shi? Me Kennan? Au aure yake so? Yana dai son wani abin kuma bai isa ba, maganar kina sonsa kuwa wannan ai karyar banza da wofi kike yi, shirme sai an yi magana ki isheni da faman *DA CIWO A ZUCIYARKI* ke har kin san mene ciwon meye kuma zuciyar? '
"TAUFEEK?" Khausar ta katse masa masifafen fadan da ya dauka a cikin zuciyarsa har ya dawo da dubansa saman fuskarta yanai mata kallon jin haushi
Kai ya girgiza a hankali ya jinginar da bayansa jikin kujerar ba tare da yace da ita ci kanki ba
Shiru ta yi na yan dakiku, sai kuma ta tabe baki tana dauke kanta daga sajen fuskarsa sannan ta turo baki tana mai jin haushin kanta, ba dan komai ba sai dan gannin dan sirrin da ta rika itama ta ce sai dai ya ji a duniya ta zauna ta kwashe ta sanar masa rabi ba tarema da ya tambayeta ba, sam wannan hali nata baya mata dadi haushin balaki yake bata wollah
Mikewa ta yi ta saka takalmanta bakin nan a tunzure ta dauki rigarta ta yafa a kafada sannan ta juya zata wucewarta
"Ina zaki je?" Ya iya budar bakinsa da kyar ya tambayeta ama bai bude idnanuwansa ba
Lekawa take dan ta gane ta inda ya san zata tafin, sai kuma ta koma ta tsaya tana sake turo baki ta ce" Gida zan tafi ne"
Sai yanzu ya dago dubansa a nutse ya kalli agogon office din sannan ya kalleta yana ragewa idanunsa girma ya ce" kin tashi ne?"
Itama agogon ta duba, ta ga da sauran kusan awani biyar koda zata tashin
Girarakinta ta tatare tana dan son tunzuro bakinta ta wani langwabe kanta gefe tana kallonsa da alamun rarashi
A hankali ya dan girgiza kansa yana sakin dan murmushi ya ce" Me zaki yi a gidan idan kin je?"
Khausar aka wani kifta ido ta ce" Dama dan sahuna yau ya je kauye ne, sai Salis yace idan na gama da wuri zai zo ya kaini gida in ya fito daga wajen aiki"
TAUFEEK ya dan gyada kai ya sake girgiza kan nasa ya ce" To albashina za'a ringa ci ana wasa da aiki Madame?"
Khausar ta Dube shi, sai kuma ta saki murmushi tana tuna abubuwa da yawa a ranta, Allah mai alheri wai ashe gagarumin likita ne, Uhum lalle
Rigar ta bude ta shiga sakawa tana dan murmushin da ya ki barin fuskarta har ta saka ta dan dube shi ta ce" Na koma Sir"
Shima murmushin ya yi yana kallonta har ta juya a hankali ya ce" Kuma Ni ne zan kai ki gidan"
Daga haka ya yi shiru ya dauke dubansa a kanta har ta gama yar tsayuwarta ta wuce
Mikewa ya yi a Nutse ya karasa dakin nan ya bude ya shiga
Tarar da ita ya yi ta yi wani irin zama kanta a saman kaffafuwanta , kuka take yi ne ko me tana dai ta girgiza jikinta yannayinta sam babu dadin gani
A Nutse ya karasa inda take ya zauna gefenta ya saka hannunsa ya janyota jikinsa a hankali ya zuba mata ido yana gannin yadda ta rukunkume shi ta saki kuka a birkice ta shiga bashi hakuri da kuma fadin" Dan Allah kar ka ce min kana son ta, Bara na fada maka maganar gaskiya ina matukar kishinta, ina kishinta, kishin Kausar nake yi fiye da kowace mace da zata iya rabarka, dan kuwa a yadda kake nunawa Khausar kula da dukkan abinda nake gani idan har maganar soyyaya ce tsakaninka da ita Ni na san ta rabani da mijina Kennan har Abada, Taufeek ka fada min soyaya kuke yi ne?"
Ita ke maganar shi ke jin hankalinsa na karra tashi a kan maganar, soyayya? Wace irin siyaya,
Gannin halin da take ciki, gashi kuma shi dama tun jiyan nan ya gama gane tana dauke da junna biyu ne ya sa a Nutse ya riketa sosai a jikinsa dan ta daina mugun motsin da take yi kar ta jima kanta rauni, du irin rukunin bacin ran da ta hadasa masa ya yi iya yinsa ya danne, dan kuwa bacin ran da yake ciki ba zai sa ya danne yannayinta ba, abu daya ya sani a furucinta baban abinda zai iya dakatar da tafiyarsa da ita take dauke da shi, watau tana zarginsu ne da Khausar, in kuwa hakane lalle Yumnah bata da wayo kuma wajen soyayar da take masa ba yau ba ya tsaya iya kunnensa, dan idan har so din kake, dole zaka jure wasu abubuwa na mutun, Bama zaka iya ganninsu a matsayin laifi ba, ba kuma zaka ringa harinsa cikin jahilci ba
Sai da ya ga ta dan nutsu ama kuma tana matukar son jin amsarsa ya mata biris ya mikar da ita tsaye a Nutse ya ce" Ki wanke fuskarki a kai ki gida" daga haka ya juya ya fice a dakin
Yumnah ta dauki lokaci mai tsayi a bayin nan cikin halin tunani kala kala
Babu abinda ke rudar mutun irin jiran fada ya ji shiru
Bata san me hakan ke nufi ba, ta kuma san ta aikata baban laifin da baya so wanda wannan banzar ta zo ta fada kai tsaye , watau zarginsu take
Da kyar ta iya fitowa ta maida hijab din ta ta fito
Nan ta samu direba da wata nurse rike da abincinta suka mata jagora suka wuce
Sai da suka tafi ya dawo office din ya nemi waje ya zauna a hankali ya dafe gaban goshinsa dake masa barazanar tarwatsewa
Tarin abinda ke cikin ransa ya masa yawa
Yana tare da gagarumin *CIWO A ZUCIYARSA* wanda ya rasa ta inda zai kamo
Ba dan komai ba sai dan zuciyarsa da ta ki bashi amanar hakan
A hankali ya mike ya koma saman kujerar nan ya kwonta yana kankame jikinsa dake masa wani iri, shi kadai ya san a irin gabar da yake kai a wannan lokacin, baya tunanin idan ya riki mace ko wace zata samu kanta cikin sauki a hannunsa, shi yasa ya nisanta kansa da wace take halalin nasa dan gudun kar ya raunatata
________________________________
Tunda Elhaji ya gama maganar nan Aba ya dafe haba cike da matsanancin mamaki ya kasa furta koda A ne yana kallon Elhaji
Yar dariya Elhajin ya yi yana jinjina kansa ɗan tabbatar masa da maganar da ya fada din, ama kuma Aba ya kasa furta koda a ne
Elhaji ya ce" Elhaji Mamuda ko dai na zo a lati ne?"
Aba ya ja numfashi yana jinjina kansa cike da mamaki ya ce"
....
Ga breakfast 😁😁😁😁😁
💔💔💔💔❤🩹❤🩹💔💔💔💔
*DA CIWO A ZUCIYATA*
💔💔💔💔❤🩹❤🩹💔💔💔💔
_MALLAKIN_
*SAJIDA NIJAR*
*FREE BOOK NE* 3️⃣6️⃣
*GARABASA, GARABASA, PROMOTION, PROMOTION DIN LITATAFAN MARUBUCIYAR A KAN FARASHI MAI SAUKI 1K, YAN NIJAR KUWA 1000 FRANCS CEFA*
1: Duk karyar kada
2: Yar mahaukaciya
3: Neman na kaina
4: Bani da zabi
5: Bak'a ce
6: Kutkale
7: Makauniya ce
8: Mage
9: Duk nisan jifa
10: Idan ka raina inda kake
11: Dutse
12: Alkalamin kadarata
13: Bani da zabi
14: Dakika Biyar
15:Wata kokowar
16: Aure yakin mata
17: Ni zan ladabi
18: Daga tafia daukar soja
19 : ZAKIN SARAKAI
*Dukansu a kan farashi mai sauki, zaka saka dubu guda ne domin promotion ne nake yi, ka tuntubeni kan layina kamar haka +227 93 81 16 18, Sajida Nijar*
Now
*Da CIWO A ZUCIYATA*
*Tallah, tallah, tallah*
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*