Sashe 97
Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yumnah na jin yannayinta , ama ta kasa fitowa fili ta fada mata abinda yake damun nata dan gani take yi ba zata gane komai ba tunda har take kallon auren TAUFEEK a daidai ne
"Yumnah?, Ki fada min damuwarki kin ji kanwata? Shin kina da wanda zaki fadawa ne sama da Ni? Baki da lafiya ne? Menene um? Sanar min" Akilah ta karasa fada da kula da kuma tausasawa
Yumnah ta ja numfashi, a hankali ta saki kukanta kasa kasa sosai tana murzar hannunta ta ce" Aunty, na kasa sakawa zuciyata salama da maganar auren nan, Ni na san ba zai taba bani kulawar da yake iya bata ba, idan kuma ya zama abu daya da ita Ni na san na zama banza a gabansa dan ta ko ina ta fi Ni power a duniyarsa"
Cike da tausayawa Akilah ta ce" Ya Allah, haba Yumnah me yasa kika ce haka? "
Yumnah ta ja numfashi ta ce" Aunty Ni na san haka ne, ban taba gannin wanda zasu yi masifa da shi murya sama sama ba ya dawo yana kokarin ganin farin haƙoransa ba sai ita, domin ko a da da muke soyaya idan ya yi fushi ma gaza shawo kansa ina fada mata a waya zata ce sai ya zo inda nake ki ganshi ya zo din, a da da take nesa da shi bale yanzu?"
"Yumnah ki dan dakata da wannan dogon bayanin dan kima neman sakani a damuwa, ina son Sannin wulakantaki yake yi ne yanzun ko mene?" Akilah ta katse ta dan bata son dogon shiga details din nan, haka kawai take ji a ranta bata so
Yumnah ta ce" Aunty, Ni bai min komai ba, ama ina mai tabbatar maki zai min din ne, dakinta fa na ganshi zai shiga daure da tawul"
Akilah da mamaki ta ce" Ke bai taba shiga naki dakin ba kennan?"
Yumnah ta ce" Yana shiga, yana shigowa, a yannayin da na ganshi ne ya tsoratani kamar wanda ya yi having s ......"
"Yi shiru dan Allah" Akilah ta fada a sanyaye tana katse mata hanzarin son fayace wasu abubuwan da bai dace ta fito ta fada kai tsaye ba
A tausashe Akilah ta ce" Bayan wannan laifin wane da wane kuma ya maki yar kanwata?"
Yumnah ta sake gyara zamanta ta ce" Aunty, dazu wai ya mana rabon kwana, shi da kansa fa, yace wai bata gama satin amarci ba bayan ita da kanta ne tace ai ta cika sati da daurin aurensu yau, sai kawai cewa ya yi bata cika ba ya hade fuska ya mana banza, Aunty sonta yake yi ko? So yake ya wulakantaki ko aunty?"
A sanyaye sosai Akilah ta ce" Aa, ba maganar wulakanci a nan, Yumnah dan Allah zamu iya yin magana da ke ta fahimta? Kin min alkawarin saurarata da kuma kokarin yiwa kanki adalci ta hanyar kwatanta shawarwarina?"
Yumnah ta yi tsai tana shan jinnin jikinta, sai dai yadda auntyn nata ke yi mata magana a tausashe ta saka a ranta cewar zata iya yi mata magana mai dadi yau
A nutse sosai Akilah ta ce" Kanwata, ina so ki san cewa a duniya kowa yana rayuwa ne da son ransa, sai dai idan ka yi kokari ka yi anfani da hakan ta hanya mai kyau zaka ji dadi, Yumnah, ya dace ki kwatanta abinda kike ji a kan Khausar, itama mutun ce, mai rai da lafiya, wace ya dace a tausayawa fiye da kowa ko dan shekarun da ta dauka bata samu miji ba, ki sani itama tana da zuciya a kirjinta kuma zata so a so ta a kuma kyautata mata, Yumnah baki san irin tsakaninta da mijinku ba, ama har yanzu ban ji inda kika ce ta maki ba daidai ba, ko marin da mama ke fadawa dad cewar ta maki da aka bi sila a kanki fadan ya sauka dan kece kika yi abinda kika jama kanki haka, Yumnah ita rayuwa tun ana rakiyarka kar ka ja a dawo daga rakiyarka, ki sani mijinki mai adalci ne domin a irin yadda kike zuba masa abubuwa da wani ne da tuni an yi dayan biyu, ko karamar bazawara ko ya maisheki ba kowa ba a gabanki ya aikata abinda ya san zai iya dauke numfashinki, ki sani ba tsoronki zai sa a so ki ba, a'a sai dai biyayarki, idan takamarki kuwa kina dauke da cikinsa ki taka a sannu itama wace ya auro tana iya dauka, Haba Yumnah sai kace ba yar musulmai ba? Ina karatunki? Mama tace yace ya raba maku gida kin kiya, to me kike so ne a maki a rayuwa? Haba Yumnah kin san da ba so da ba zai daga maki kafa ba, mijinki baban mutun ne, ban kara jin ina shakarsa ba sai a asibiti, shikenan ke sai ki ringa wulakanta masa zuciya? Yaya zaki budi baki ki ce wai ya je dakin matarsa kuma ke da na tambayeki bai taba shiga naki dakin ba hankali kwonce kin shaida min yana shiga , shin ita ba mutun bace? Haba Yumnah ta yayama zaka sakawa namiji ido a kan shigarsa da fitarsa da matarsa? Idan ke aka sakawa yaya zaki ji ne?, Ya dace in kana abu ka ringa saka lisafi ka kuma ringa tuna mutuwa, dukka kaf abubuwan nan da kike yi zaki tsaya gaban Allah ne ki yi bayani Yumnah, dole zaki tsaya ki yi bayani, ki tuna fa Allah yana yafe laifin da ka yi masa ne idan ka nemi yafiya ama baya yafe laifin da ka yiwa bawansa sai idan shi bawan nasa ne ya yafe maka, Yumnah shin bakya gannin wannan laifin a baba ko? Ki sani baban laifi ne dake iya kaiki halaka, kina ji kina gannin son zuciyarki zai kaiki halaka idan baki tuba ba"
Akilah ta saurara har tana dubawa dan kar aje ita kadai ke zuba Yumnah ta kashe kiran , dan a yadda kanwar Tata ke nunawa ita abin har tsoro yake bata
A tausashe ta ce" Yumnah kina fahimtana kuwa?"
Yumnah dake share hawaye a hankali ta gyada kanta tana amsawa da eh
"Mijinki yana son ki, yana son ki, kuma yannayin jikinki ba shine zai sa ya tsane ki ba dan ya auri wace ta fi ki yannayin jiki da wani abin da kike gannin zai iya zame maki cikas a zamantakewar ki da mijinki sai idan kin yarda , kema macece, komai yannayin jikinki kina da damar jan ragamarsa abinki, kin san waye mijinki, a tunanina zaki yi iya yinki ne dan gannin kin samu fuskar mijinki ta hanyar biyayya da tsaftatacen kishi ba banzan kishi ba, Haba Yumnah sai kace ba mace ba?" Akilah ta kuma fada a sanyaye sannan ta dora da fadin" Yumnah Mama bata da lafiya, bata da lafiya Yumnah, abinda ya hanna Ni juyawa kennan, ta saka damuwarki a ranta fiye da ke din, kima kwaso abu kina fada mata tana nisawa dan bata da yadda zata yi domin dad ya sharanda mata manyan sharudan da ba zata iya takawa ba, dan kuwa komai dadin gidansu ina mai tabbatar maki nan gidan mijinta nan ne kwonciyar hankalinta, kuma du irin abin nan dake faruwa Yumnah Mama zata fi kowa farin cikin ace kina dakinki a tsugunne irin kowace mace, kawai dai ita bata iya tankwasa zuciyarta a kanki ne, tana maki kallon yar jaririyarta ne, Yumnah a duk lokacin da kika yi kiranta kika fashe da kuka zata dafe kirji ne, tun tana boyewa har ya zamana bata iya yakin hakan dan kuwa jinninta hawa yake yi, kuma a abinda bata da maganinsa, Yumnah shin zaki so ace kece sanadiyar kamuwar mahaifiyarmu da mugun cuta a kan abinda fadan son kai ne kike yi ba na gaskiya ba?, Yau da ace mijinki na anfani da damarsa wajen wulakantaki ne , da ki sani Ni din nan sai na kwatar maki yancin ki, Yumnah da gatanki gaba da baya sai dai ki sani daga Abanmu har Ni yayarku ba zamu hau kan turbar karya ba dan jin dadinki, domin a duniya ake iya neman yafiya , a lahira sai dai a amshi sakamako gashi babu wanda ya san ranar mutuwarsa, kana biki budiri sai dai a wayi gari ka ji kanka a cikin kasa ba gaba ba baya!" Akilah ta karashe a tausashe tana share nata hawayen, dan bata san yaya zata yi da kanwar nata ba, bata son halin nan, tana yi mata uzuri ne dan har yanzu da yarinta a tare da Yumnah, sai dai zata so ta gane shi fa namiji zaka ji dadinsa ne idan kana kyautata masa, in kana wulakantashi komai son da yake maka komai kyanka komai takamarka tsaf zai watsar da kai kuma babu wanda ya isa ya dawo maka da shi sai Allah sai dai a ci da hakuri ko a rabu idan ba za'a iya ba, ita kuma bata yiwa kanwar Tata fatan zawarci , ta fita daga hannun TAUFEEK ta fada wani hannu? Da wahala ta auri saurayi mai mace daya, a halayanta ko mai mace dayan ta aura da wahala su jitu dan kuwa bata iya bambance duniyar mutane da ta ALJANU ba!
Yumnah, gaba daya jikinta ya yi wani irin sanyi, a jikin kofar da take zaune na dakinta a hankali ta jinginar da kanta a jikin kofar
Sosai maganar da suke tataunawa da yayarta yau ke neman yin mugun tasiri a zuciyarta
Bambancin yayarta da mahaifiyarta shine, ita Mamanta ko me ta nuna tana so zata dafa mata baya ne, har kwanan gobe, yayarta kuwa idan ta kawo rigimarta sai ta duba in abin yi ne a yi in ba na yi bane fakat take nuna kin amincewar ta, shi yasa suke da dan rashin jituwa a tsakaninsu, dan ita gani take yi bata sonta ne,
Ama a yau sai take ji kamar idan ta bi shawarar yayar Tata zata samu mafitar abinda yake damunta