Sashe 8
Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Itafa idan har ba gani ta yi an daura aurenta da TAUFEEK ba da wahala hankalinta ya kwonta da wannan KAUSAR din
Ita ta rasa a wani bigiri zata ajiye wannan shirmen, kana zaune kalau da mutumen da ake kira miji a gareka nan da kwana kusa ama kiri kiri kana fuskantar kusanci da shi da wata macen cen da yake kira da kawarsa fiye da kai? Sau biyu sunna samun matsalar da TAUFEEK ya dauke mata kafa kwata kwata na tsayin lokaci, ta ringa bibiyarsa itace nan , itace cen ya ki sauraronta, har gidansu ta zo fir ya ki kulata, tana samun KAUSAR ta mata bayani ta mata fadan itama laifinta ne ta daina kula kowa tunda bata so ta kuma mata alkawarin ya wuce a washe gari TAUFEEK din ya amsa kiranta?, Bayanshi kayan sallah wannan idan za'a yi mata ta sha gannin an mata wani abun iri daya da KAUSAR bayan wannan kyauta ce ta mahaifiyarsa bama tasa ba, abubuwa ire iren haka idan har irgawa zata yi sunna da yawan gaske, sai gashi yauma an maimaita abinda aka saba yi mata sai ance mata za'a zo a fasa dan an je an zauna a wajen KAUSAR an cika dare ana hira, itafa zata iya rantsewa da Allah ko yan matan da suke amsa matsayin yan matansa a gari basa yi mata katutu a wuya irin na wannan baiwar Allahn, sam bata da nutsuwa da ita, bata son lamarinta, ama ba komai in sha Allah lokaci dai idan har ta amsa sunnan matarsa kuma zata maida hankali ta fara haihuwa du taurin kaan TAUFEEK ai dole zai daina mu'amalantar mace a matsayin kawa ko dan tarbiyar ya'yansa.....ita abinda ya fi bata mamaki mahaifinsa fa ya san da maganar KAUSAR ama bai hanna ba, ba'a maganar mahaifiyarsa dan ta kula sonsa take sosai , ama ba komai a juri zuwa rafi wata rana tulun zai fashe ne!
Hajia yake kallo da kaskon hannunta hakan ya sa bai gane jimawar da YUMNAH ta yi bata yi magana ba har sai da Hajiar ta saki murmushi tana sakace hakorinta da tsinke ta ce" Kun gama maganar ne?"
Idannuwansa ya lumshe a hankali ya ce" YUMNAH?"
YUMNAH ta ja hanci tana share hawayenta kasa kasa sosai ta amsa
TAUFEEK ya ce" Kuka kike yi ne?"
YUMNAH ta ta fashe da kukan da ta kasa hanna kanta tana sauraronshi, hakan ya sa ya dan sake lumshe idannuwannsa da suka dauki launin ja a hankali ya ce" Zan fa zo gobe in sha Allah, menene na kukan kuma?"
YUMNAH ta ringa jan hanci tana hanna kantaa kukan, a hankali ta ce" ka tabata gobemaa ba zaka tafiyarka wajen KAUSAR ba?"
KAUSAR........sunnan da ta ambata ya saka shi jin wani takaicin da ya dan barshi ya sake kule masa wuya
Yanzu KAUSAR ba zata taba girma ta yi hankali ba Fisabililahi? Inama abinda ya yi mata, bata tsaya ta ji aiken Aba bane, bata tsaya ta ji bama ya kasar Dubai ya tafi shigowarsa jiya , yau yana fama ya gama da wasu kayan ya je ya sameta ama shine ta watsa shi? Shi KAUSAR ke hanna Auta gaisarwa? Shi KAUSAR ke cema in ta haihu yar halak ba ita ba maganar ya gyara kayansa? Wai shi ya gama menema tace? Itace mene? Lalle KAUSAR ta kirta masa rashin hankali wanda ba zai taba mantawa ba, kuma shi da ita su zuna za'a ga maganar da ta yi wa zata komewa, ba tace in ta kuma masa maganar ya yi karatu ba meye meye? Zai ki yin karatun za'a gani waye zai cika dare yana fadim ya yi karatu, ita in bama ta raina shi ba shi sa'anta ne zata wanke shi soso da sabulu kamar wani danta?, Har ga Allah a gari kaf ya zagaya da kwakwaluwarsa bai ga dan jagaliyan da zai yi wannan gagancin ba bale mai hankali, kama daga kan mace har namiji sai KAUSAR, shi shi????
"Ana halo halo a wayar magidanci amsa mana ka gama na ji kukan uban me take yi ita kuma? Ba dai gaba take saka ka tana maka kukan rainin hankali ba salon a raba maka hankali biyu, jigilar gidan nan ka yi ko rikicin munafurci na mata? Ni fa ka ga du macen da za'a aura maka sai na kaita kotu ta yi rantsuwar ba zata cuta maka ba dan bana son rikita rikitar yan matan zamani yan iska masu taba halitar ALLAH sunna zanna gira da kwaliyar aljannu wai su masu kyau" ta karashe tana sake gyara tsayuwa ta dauke kai daga kallon da yake yi mata kamar ya ga bakuwar halita harda zarro ido yana kallonta da mamaki
Dididif din wayar ya saka shi kallon alon wayar sannan ya sake kallon Hajia dake harare harare
Kasa kasa kamar kar wani ya ji shi ya ce" Kin kuwa san wacece kika zazage tas ?"
Hajia ta juyo tana maka masa harara ta ajiye kaskon ta watsa magungunnan da ta harhada ta yi raf da hannunsa da ya kawo zai kautar da hayakin da ya shiga binsa bududu tana gyatsine ta ce" Ko wacece uwata, nace uwata in itace mai KWANONI kuwa ni nice babarta!, Alkur'ani idan baka san ciwon kanka ba na san ciwonka babu wace zata lalata maka zaman lafiya ta maka kukan kirsa ta cuceka ina raye!"
Har ga Allah bashi da karfin rikicin yau, haka kawai yake jin karfinsa ba na rikici bane yau, ga hayakin nan juya masa kai yake kamar zai sume bayan tace na mayu ne da na aljannu, shi kuwa ba maye bane a sanninsa haka kuma shi ba aljani ba, hayakin ne kawai bai cika so ba har wani makaki yake masa a wuya, ama ta ki ganewa sai da ta gama rikita masa rayuwa ta saki tana jan tsaki ta dauka ta ringa zagaye kujerar da yake zaune tana tofe shi sannan ta yi gaba tana ta fadace fadacenta
Idannuwansa a lumshe suke ya zuba su a kan hanyar da ta bacewa ganninsa a kala ya dauki minti biyar kafin ya sauke ajiyar zuciya ya shiga bude abincin ya shiga ci dan yinwar dake cikinsa idan ya kwonta ga takaicin Kausar, ga na Yumnah, ga na Hajia ana iya tardoshi ya karkace da hawan jinni, gwara ya cencani kansa tunda rayuwar ta zama haka
Sun dan jima kafin suke shigowa kusan a tare a lokacin Aba tuni ya dawo gida ya ci abinci ya shiga karatun Alkur'ani domin shi wannan lokacin kadai yake da shi wanda yake yin ibada sosai, dan kuwa idan ya fita nema baya zama sai dare ya yi kafin yake samun zama
Bayan sun huta Aban ne ya saka aka masa kiransu su dukansu ukun,
Sun jinginu ne a jikin garu kwon fitilar da nepa sula kawo ya haske dakin, hakan ya sa yake binsu da kallo daya bayan daya harda Mamansu Auta kuwa yana cen saman katifa yana barci abinsa
Numfashi ya sake saukewa zuciyarsa a tsintsinke ya shiga bayanin abinda ya wuni da shi a saman zuciyarsa wanda bai shigo gidan nan da wuri bane saboda sai da ya je wajen manyansa ya duka ya nemi shawara kuma aka amince masa da hakan harma aka sake bashi shawarwarin da zai ji dadinsu
A tausashe sosai ya ce" KAUSAR, A'isha, RUKAYA, na tara ku a nan ne dan na ji daga bakinku dangane da maganar aure......."
A cikinsu su biyun nan wani irin salama ne ya sauka a kahon zukatansu, ita kuwa wani irin firgici da tashin hankali ne ya dirar mata bayan fushin fadanta da yaron cen da ya raina mata hankali
Kanta a kasa yake, ama mahaifinta yana iya gane halin da take ciki domin ta kama hannunta sai murzar yar yatsarta take yi haka kuma kaffafuwanta dake hade daya kan daya sai murzasu take yi tamkar tana jin fitsari ya matsotan nan
Idannuwansa ya dauke cike da rauni ya sauke kan fuskar matarsa
Irin kallon da take masa mai dauke da girmamawa da mutuntawa da nuna alamu na tana tare da shi ya saka shi jin dan kwarin gwuiwa a hankali ya ce" In sha Allah gobe da safe ina jiran amsarku, kowace ta yi kokarin gannin ta bani amsar da ta dace mai kyau wace zan yi bincike a kai dan mu samu matsaya daya mai kyau, domin bi'izinillah shekarar nan idan har ta wuce ku babu aure to zan samo maku Wa'inda suka dace na hadaku na aurar, ku tashi maza a je a kwonta a huta, du wace bata yi shafa'i da wuturi ba ta tabatar ta yi kafin ta kwonta"
Amsawa suka yi su biyun, ita kuwa kai kawai ta iya gyadawa tana jin hankalinta na karra tashi
A hankali ta mike dan bin bayan yan uwanta , mahaifinta ya yi kiran sunnanta yana dauke dubansa daga kan mamanta dake masa alamun kar fa ya nuna gazawarsa
Juyawa ya yi ya ciro yar karamar wayarta da ta bashi ajiya tunda zasu fara jarabawa ya miko mata yana dan murmushi ya ce" Dama ga wayarki nan ai na san za'a samu kira yau ko?"
Wayar ta kalla, sannan ta kalli mahaifinta.....
Za'a samu kira?, To daga wajen wa?
Sai dai bata da amsa, hakan ya sa ta yi godiya ta juya ta fice ta karasa dakin itama ta kwonta saman katifarsu ta juya tana fuskantar garu
Tun tana jin maganar yan uwanta sama sama sunna waya da albishir wa masoyansu cewa Abansu ya yi tambaya kan abinda ya shafi zumuntarsu da sake jadadawa zumuncinsu da karra yarda in har alkarsu da burinsu na nan? har shiru ya wanzu a dakin a hankali minsharin Rukaya ya fara tashi hakan ya tabatar mata cewa sun yi barci ne
Idannuwanta kekyashe suke ba alamun zasu risina ko su aro barawon da aka sheda kwarewarsa a sata dan ya saceta ko dan wuni da ta yi a kai kawo da jigila kala kala na auren da aka yi yau, ama shi sarkin baiwa bawa kunya shiru bai dauketa ba, bai yi alamun zai dauketa ba
A hankali ta dago hannunta da ya sage ta dafa ta mike zaune sannan ta jinginar da bayanta a jikin garun ta kurawa waje daya ido