← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 116

Sashe 72

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A nutse ya maida dubansa ya soketa da allurar ya kunce daurin ya zuba mata ruwan allurar sannan ya zage ya dane da audugar ya ajiye allurar a cikin dan kwanon da nurse ke rike da , shi kuwa yana rike da hannun nata a hankali yana dan murzawa yana kallon fuskarta mai zubar da hawaye har ya dauki mintinan da zasu kai sha biyar sannan ya mike yana gyarata gaba dayanta ya rufa mata abin rufa kadan sannan ya juya bayan ya daidaita mata ac ya fice a dakin yana cire safar hannunsa

Yana fitowa ya ja ya tsaya gaban ahalinsa, a yadda ya shige ya barsu yanzun basa hayaniyar, sai dai kana ganninsu ka san kowa a dane yake, sai kuma ya fuskanci abinda ya hanna su hayaniyar vigil din dake tsaye su hudu ne kowane ya hade girar sama da ta kasa sun fada masu cewar du fa wanda ya masu hayaniya fitar da shi zasu yi

Da kula ya ce"

💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

*DA CIWO A ZUCIYATA*

💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

_MALLAKIN_

*SAJIDA NIJAR*

*FREE BOOK NE* 4️⃣4️⃣

*GARABASA, GARABASA, PROMOTION, PROMOTION DIN LITATAFAN MARUBUCIYAR A KAN FARASHI MAI SAUKI 1K, YAN NIJAR KUWA 1000 FRANCS CEFA*

1: Duk karyar kada

2: Yar mahaukaciya

3: Neman na kaina

4: Bani da zabi

5: Bak'a ce

6: Kutkale

7: Makauniya ce

8: Mage

9: Duk nisan jifa

10: Idan ka raina inda kake

11: Dutse

12: Alkalamin kadarata

13: Bani da zabi

14: Dakika Biyar

15:Wata kokowar

16: Aure yakin mata

17: Ni zan ladabi

18: Daga tafia daukar soja

*Dukansu a kan farashi mai sauki, zaka saka dubu guda ne domin promotion ne nake yi, ka tuntubeni kan layina kamar haka +227 93 81 16 18, Sajida Nijar*

Now

*Da CIWO A ZUCIYATA*

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata💃💃💃💃💃

Da kula sosai ya ce" Alhamdulilah ta samu barci, ku mu je a maida kowa gida dan basa yarda da yan jinya"

Mahaifiyar Yumnah cike da gannin rainin hankalin TAUFEEK ta ce" Basa bari ko baka bari, ko kana tunanin har yanzu bamu san wanene kai da matsayinka ba? Bama wannan ba, Taufeek bani da muradin a kula da ita a wajen da ake neman ranta, ko shekara bata rufa ba an dankara mata uwar mata, wa ya san me zai sameta idan na tafi na barta, a bani y'ata kawai a tafi da ita gida mu yi jinyarta a cen!" Ta karashe tana fitar da huci, daci take ji a ranta sosai na wannan lamarin, babu irin tarewar da basu yiwa wannan abin ba ama a karshe sai da wannan anobar ta zama mata a wajensa? Lalle da take kwabar Yumnah cewar ta daina tunanin akoy wata mu'amala da ta wuce soyaya da abotakantaka tsakaninsa da wancen guzumar yanzun itama ta fara tunanin ta yiwu wata jarabar ta bulo aka yi wannan auren rufa rufar dan kar a ji!

Murmushi mahaifiyar TAUFEEK ta yi tana girgiza kanta

Shi kuwa cikin nutsuwa ya saukewa vigil din dake tsaitsaye duba, kafin kace me sun yi gaba sun bar wajen

Hajia baba ta girgiza kai cike da tarin takaici ta ce" Kai, fito mata da y'ar ta tafi da Itan mana sai me, wato ke ana baki kina roko kema nan uwar y'a kike ko? To bari ki ji da bakina ina waje a raye babu mai dagawa magidanci hankali, aikin banza wannan har matar huce haushi ce? In ba rashin daukan shawara Bama , ai macen farko rusasa ake dauka gidan hakuri gidan huce haushi idan ya so daga baya sai a bi dadi duniya yan idan Kanada shi ake iya zama da kai in baka da shi ba'a iya zama da kai!, Aikin banza ke kuwa kina tsaye ana neman zagar maki d'a sai dai ki yi murmushi , shin zafin nakuda aka fi ki sani ko amfanuwa yarta ta fi d'anki? Idanma zafin fitar kai ne ai na magidanci zai fi azaba, ke dai Allah ya shiryeki!"

TAUFEEK ya idasa sauke dubansa a kan Hajia , ikon Allah yake kallo, Hajia da hijab kamar zai tadeta ta fadi ama banda neman rigima ba komai a cikinta,
Kai ya girgiza ya juya zai bar masu wajen mahaifiyar Yumnah da take ji inama inama idan ta bude baki ta durawa uban kowa zagi babu abinda za'a yi, ama tana tsoron wannan dakewa ta TAUFEEK da kuma sharewar da mamansa ta yi, bata san me hakan ke nufi ba, ta sake dubansa ta ce" Yaya zaka tafi bayan na fada maka ina so a fito min da ita mu tafi gida?"

TAUFEEK ya dakata da tafiyar da yake yi ya juyo, a hankali ya washe fuskarsa daga yannayin hadewa ya dan saki murmushi ya ce" Cewa na yi kowa ya koma gida, zan kawo ta idan na ga zata iya jurewa hakan"
Daga haka ya yi tafiyarsa

Mahaifiyarsa ta yi murmushi ta dauki ledar goron Hajia da ta yar tana masifa ta ce" Hajia mu je a maida mu gida"

Hajia da ta gama summa a tsaye gannin badalar da Magidanci ya aikata ta ja numfashi ta ce" Eh kaini gidan dai na ga mai Kwanoni, kin ga kuma yannayin magidanci ya bani tsoro gaba dayanmu ya hade ya kora, Ni uwar mai kwanoni harda Ni? Mu je mu je"

Da sauri Akilah ta fice itama a wajen ta bi bayan su Mama, har Mama ta shiga Mota ta dakata gannin ta karaso

Tsayinta ta rage sosai ta ce" Mama dan Allah ku yi hakuri da abinda ya faru, in sha Allah idan mun je gida komai zai daidaita"

Mama ta sakar mata murmushi cike da gannin girmanta, sosai yarinyar ta birgeta, da kula sosai ta ce" Kar ki damu auntynsu, ba wani abu kin ji? Allah ya bata lafiya, a kuma yi hakuri abin ne ya zo a haka, kin san aure da haihuwa ke da komaima na rayuwa lokaci ne, Allah ya yi haka zata kasance, kwarai ba'a kyauta mata ba, kuma Ni mace ce na san me muka dauki kishi, ama ina mai bata hakuri kuma in sha Allah Elhaji karami zai yi adalci a tsakaninsu"

Daga haka suka yi mata salama direban da TAUFEEK ya sa ya kai su gida ya ja motar

Sai da suka yi nisa Hajia ta ce" Uhum, wani lokacin sai ki yi halaya na munafukai sak , yo me kika masu da zaki basu hakuri? Aure fa an daura sai dai a ci da haka, Ni abinda nake son sani wani shege ne ya yi kiran uwar yarinyar nan ya sanar mata kai tsaye har take son zagina?"

Mama ta ce" Aa Hajia ba zata yarda ta zageki ba, kawai rai ne ya bace, ama komai zai wuce , ita Allah ya bata lafiya, wanda ya hadasa haka kuma Allah ya bashi ribar da ta dace da shi"

Sunna tattaunawar nan har suka isa gida

A asibiti kuwa hajia nawarah basu tashi bada hakuri mai kama da zigi ba sai da aka watse aka barsu da Maman Yumnah
Hajia Fatahiya ta saba yarta a kafada tana fadin" Zamu tafi Hajia, kin san mijin Yumnar bai cika lalaba abu ba, du girmanmu da matsayinmu na matan mahaifinsa in ya dawo ya same mu a nan yana iya zazaginmu , kin san abu da baban gida , Allah dai ya sanyaya ama ai abin ba tausayi sam, yarinya karama a hada da wannan ina zata saka ranta, yaya zata iya kishi da wannan mace, ai kawai in nice Elhajin zan nemi gani a duba lamarin nan , gaskiya a zaba y'ata ko wancen kaska rabi mai jinni jikar"

Hajia nawarah ta cafke da fadin" Uhum, Ni dama na san a irin kwadayin yarinyar nan da iyayenta komaima zai faru, Allah dai ya sa a barwa Yumnah cikinta kar aje a kaita wajen bokaye a rabata da cikinma dan kuwa na tabata kai sake Elhaji ba zai aurawa Magidanci wannan guzumar ba, menene abin mora a mota mai hayaki? Wahala ce kawai, Allah dai ya kyauta mun tafi kar ya dawo ya wulakantamu , kin san bashi da sauki ko kadan!"

Sosai abin ya sake rikita mata lisafi, suka fice suka barta zaune ta zubawa waje daya ido har Akilah ta dawo ta zauna gefenta kanta a kasa ta kasa cewa komai ama tana sauraron wayar mahaifiyar Tata domin ta yi kiran babansu ta sanar masa abinda yake faruwa ya kuma ce zai kirayeta yanzu yanzu su koma gida zai dawo shima yanzun ya sameta
Chapter 72 · 0% Book details