← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 116

Sashe 79

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wunin ranar Yumnah bata kuma fitowa ba, abinci kuwa dama rabonta da shi tun anaa gobe auren aminiyar mijinta, idan ta ji yinwa takan samawa kanta ne bata bi ta cikinsa, dan ta kula idan ta bashi ko a'a ba zai zauna da yinwa ba tunda kakarsa na gefe

A bangaren TAUFEEK kuwa sai dare ya dawo gidan, yauma shi dai ya samu Yumnah a bangarenta, gwargwadon iyawarsa ya kwatanta bata kulawa , ko dan abinda ke cikinta, sannan har ga Allah yana so ya bata darajar ta daidai misali, dan baya so ya shiga hakinta ko kadan, Khausar kuwa dama yau bai ganta a wajen aiki ba, bai kuma je gidan ba, dan ya dan tsinci cewar tana cen tana kuka, bashi da amsar bawa kansa sai girgiza kai da ya yi ya ci gaba da lamuransa, abu daya ne ya sani rikici ne Mai kwanoni da Malan muntari sun daurawa kansu, mai kuncewa fitar ransa ne daga gangar jikinsa, gwarama Yumnah da Khausar su ba kansu lafiya ko su yi, zai kasance mai raka du wani mai doguwar tafiya ne har su kai inda yake so bi'izinilah

A gidan su KHausar Hajia Fusam ce da kanta ta yiwa gidan dira tun a lokacin da Mama ta je mata da bukatarta suka yi magana irin ta manya suka kuma shirya cikin harka ta manya, da kanta ta dauki motarta bayan Maman ta mata kwatance ta kuma sanarwa Maman su KHausar din cewa za'a zo a shiga kimtsa Khausar din

Kaya ne ta je da su na kasa da kasa, ko da ta karasa su Rukaya ne suka tayata saka kayan cikin gidan Aba dan da yawansu

Du irin yadda Khausar ta rikice da bayanin wai kwana biyu kawai zata je gidan su TAUFEEK matsayin mata a wajen TAUFEEK sai da Mama ta mata magana daya da ta sakata sakarwa ta zubawa sarautar Allah ido

Hajia Fusam ta fara ne da hada hadin da zai goge kunshin da aka yiwa Khausar ta shafa mata aka bari na dan lokaci kankani aka wanke da ruwan dumi, sai kuma ta kawo hadin da ta yi dan dora Khausar din a kujera hadi na mamaki ta saka Khausar din mikewa ta shafeta da shi ama fir ta ki yarda har wasu sassan jikinta sai ita da kanta ta shafa irin su Mamanta da cinyoyinta da mazaunanta, ita dai Fusam ta bata damarta dan ko ba komai budurwa take mai kunya abinda dai ya tabatar shine ko'ina ya samu sannan ta haudata kujerar nan ta rufeta da rigar da ake rufewa aka bar fuskarta kadai a waje

Hayaki na ratsata har cije lebe take yi dan sosai yake ratsata, gefe guda kuwa Hajia Fusam na aikin hade haden gyaran fuska da lebe da kuma na raba rabar cinyoyi da mazaunai, hadi dai na mamaki , ga kuma hadin madara mai sanyi da ta sakawa zuma ta mata da magani mai kyau da inganci namu jikake na wajen Maman khair tana yi tana kafa mata tana sha har suka gama aka sauka aka nufi bayi dan wanke kwanin
Tana fitowa Fusam ta kama dirzarta da dilka, tamkar zata kwaye mata fata dan kuwa bata yi mata da sauki ba , sosai ta darjeta har tana yan hawaye , shima aka darwaye da ruwan dumi aka kuma hauda mata kurkum hadi mai madara sannan ta dawo fuskarta ta shafa mata hadin tumatur,....a wannan rana dai Khausar ta ga ikon Allah dan hadi kan hadi ake juye mata ga na sha a gefe sai da ta ji cikinta tamkar zai fashe, ga lebenta da aka samu da nasa hadin aka darje shi da bruch har sai da ya ringa wani irin MUSMUS a ido bale a tabawa , kafin ta kare da sakata a babar robar Mama ta wanki cikin rantsatsen turaren mata masu daraja, su turarukan nan kala uku ne, dama aikinsu ratsa jikin mace ne dan ba'a shiga da pant sai da ta shiga ya zauna ta rufa jikinta da zani sai dan zabura take yi saboda zafin ruwan da aka zuba turaran ciki

Tana zaune a cikin ruwan Fusam ta ajiye kujerar tsuguno a bayanta ta shiga gyara mata gashin kanta ta hanya shafa mata hadin lallen da ta hada shi da sinadaren gyaran gashi da kuma turaren gashi mai nutsatsen kanshi bayan ta rereda shi ta ringa fesa hadin danyar cita da kananfari da ta markada ta matse ruwa ruwan ta zuba a abin fesawa ta fefesa mata shi sosai sannan ta saka mata hular kan ta daure mata shi tam

Sai kusan magariba suka gama shirin yau, tana tsaye a kanta har ta dauro alwallah bayan ta kuma yin wanka da wani hadin ta zo ta tayata shafa man da ta hada mata mai karra laushi da santsin fata ta sakata a gaba ta ci dahuwar kazar amarya mai ridi da nonon rakumi ta kuma bata tsumi matsayin ruwa sannan ta zauna har suka yi sallar isha ta masu salama bayan ta tabatar mata gobe idan Allah ya kaimu zata dawo tun da duku duku duku mai kunshi da mai kitso , sannan ta tafi

Bayan tafiyarta sosai Khausar ta so tsundumuwa a tunani, sai dai wani irin kanshi da laushin shinfidar da aka yi mata ya luliyata a barci mai nauyin gaske, ko ba komai wannan dirza da ta sha da gasuwa da ruwan dumi sun isa su sakata barci koda bata yi niya ba

Mama kam ta kwana saman salaya
Tana neman alkhairin auren nan da kuma adu'ar Allah ya kade dukkan wata fitinar dake iya kunnowa, ya kawota da sauki, fatanta yarinyarta ta amshi aurenta ta kuma je ta yi biyayya a dakin mijinta, sun yi magana sosai a kan tarewar, Aba ya nuna damuwarsa na yana so ya yi mata kayan daki ama Baba mai kwanoni ya daureshi da jijiyoyin jikinsa ya hannashi maganar kayan dakin, duda haka tanadin da ya yi dan kayan dakin da garar sai ya zuba kaf a Gara , ya yi niya zai mata Gara ta mamaki, mamama ta yarda da haka, babu abinda ya gigitasu harda makota irin akwatunan da aka kawo, ta san aure wani lamari ne na Ubangiji, lalle Khausar ta yi goshi na mamaki, maganar akwatunnan Khausar har gidan su tsohon saurayinta ya kai, wace ta kai maganar kuma ita ta kawowa mama cewar mamansa na cewa auren jari aka yi, Maman kuwa ta bata amsar ai ba laifi bane, ba haramun bane !

Babar rana

Rana bata karya sai dai uwar diya ta ji kunya in ji yan magana
A dade ana yi kuma sai gaskiya
A yau ranar asabar ta kama babar ranar da ta zamto ranar tarewar Khausar a dakin mijinta, amini a gareta, abokinta bisa hukuncin ubangiji ba tare da shirinta ko yardar ta ba sai dan hakan shine a rubuce a kundun tarihinta, tsayin shekaru tana rayuwarta tare da kalolin tsangwamar mutane da tsangwamarta ta kanta, a yanzu ta amsa kiran matar AURE, auren da take yiwa kallon wasan yara, wanda ta gama yarda har a zuciyarta cewa ta girmami wannan aure nema ake yi a hadata da shi dan ta shiga uku, sai dai ta makara, domin sauko ta yi ba tare da ta san shi a hanya ya kwana ba, a daidai wannan lokacin da magariba ta sanyo kai ya zamto a dole Mama ta cire kunyar y'ar fari ita da yar uwarta suka tsaya a dokin kofar dakin Aba suka hanna mutane shigowa

Wato wani irin taro ne na mamaki ya dauka har anguwar ba iya gidan Aban ba
Mama bata yi gaya ba, hakama Khausar, dama dama su Aisha sun gayyaci daidaikun kawayensu , sai ga abin mamaki matan anguwa tun kafin magariba ta rufa suke shigowa kowace kuma da haramar rakiyar amarya Khausar, domin da yawa daurin auren a wai suke jinsa, an daura din wasu basu san waye angon ba, irin yadda ta yi rayuwarta kuwa zasu so su ga wanene wannan ango!
[7/19, 3:17 PM] Maman Aslam: 💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

*DA CIWO A ZUCIYATA*

💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

_MALLAKIN_

*SAJIDA NIJAR*

*FREE BOOK NE* 4️⃣9️⃣

*GARABASA, GARABASA, PROMOTION, PROMOTION DIN LITATAFAN MARUBUCIYAR A KAN FARASHI MAI SAUKI 1K, YAN NIJAR KUWA 1000 FRANCS CEFA*

1: Duk karyar kada

2: Yar mahaukaciya

3: Neman na kaina

4: Bani da zabi

5: Bak'a ce

6: Kutkale

7: Makauniya ce

8: Mage

9: Duk nisan jifa

10: Idan ka raina inda kake

11: Dutse

12: Alkalamin kadarata

13: Bani da zabi

14: Dakika Biyar

15:Wata kokowar

16: Aure yakin mata

17: Ni zan ladabi

18: Daga tafia daukar soja

*Dukansu a kan farashi mai sauki, zaka saka dubu guda ne domin promotion ne nake yi, ka tuntubeni kan layina kamar haka +227 93 81 16 18, Sajida Nijar*

Now

*Da CIWO A ZUCIYATA*

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata
Chapter 79 · 0% Book details