← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 116

Sashe 36

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Noted: *MAI SON MAGANINMU IDAN BA A KADUNA YAKE BA, SHI ZAI YI KUDIN MOTARSA HAR ZUWA INDA YAKE, BABU INDA BAMA TURAWA IN SHA ALLAH.....SAI KUN ZO*

💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

*DA CIWO A ZUCIYATA*

💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

_MALLAKIN_

*SAJIDA NIJAR*

*FREE BOOK NE* 2️⃣1️⃣

LITATAFAN MARUBUCIYAR

Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Neman na kaina
Bani da zabi
Bak'a ce
Kutkale
Makauniya ce
Mage
Duk nisan jifa
Idan ka raina inda kake
Dutse
Alkalamin kadarata
Bani da zabi
Dakika Biyar

Now

*Da CIWO A ZUCIYATA*

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata💃💃💃💃💃

A sanyaye ya ce" Yauma kin yi aiki ne?"

Fuskarta ta dago a hankali ta zubawa tasa ido, kwanakin nan da ta yi kusam biyar bata ganshi ba saboda aiki ya yi tsanani sai ta ga ya wani cika kasumba a fuska, ko idannuwanta ne ke nuna mata haka?
A hankali ta sauke ajiyar zuciya ta dan girgiza kai tana kawar da dubanta a kansa ta kai wajen motar
Ido cikin ido suka yi da Yumnah
Da kallo wani kalla wanda idannuwanta suka gane mata daga idannuwan Yumnar, wani kallo daban kamar , kamar dai, kamar........

"Uffff, ya salam" ta fada a hankali tanaa dauke nata idannuwan, domin abu daya ranta ya bata shine yannayinta na son taba mata kwakwaluwa bayan zuciya

"Kina da wata damuwa ne?" Ya sake fada, domin gaba daya yannayinta ke neman taba nasa yannayin

A hankali ta girgiza kai tana kokarin daidaita yannayinta ta ce" Ba komai"

Zuba mata ido ya yi, yana gannin kwalar da ta maida karfi da yaji, naan fa ya ji hankalinsa na neman tashi
Ya san wacece wannan yarinya ciki da bai
Kasantuwarta mai tsananin rauni , mai mutunci mai mutunta kowa, mai farin cikin badawa, mai zama da zuciya daya ya saka ya shaku da ita shakurwa irin ta mamakin nan, domin yakan rikice lokuta da dama da damuwarta

"Yaushe kika fara boye min damuwarki?" Ya fada a hankali yana so lalle sai ta kalle shi

Dagowa ta yi lokaci daya idannuwanta suka ciko da kwallah mai zafin gaske ta saka idannuwanta cikin nasa

A hankali hawayenta ya shiga wanke fuskarta har ya zamto ta dan fara shasheka tana kallonsa cikin hijab dinta milk color wanda ke boye sirrin jikinta gaba daya

Ido cikin idon nan bataa dauke nata ba dan tana nitsewa ne a cikin idannuwansa idan har tana hali na kaka nakka yi, takan samu solution ne a nasa idannuwan dan takan ga tausayi, karfafa gwuiwa, fada, jajircewar sai ta yi hakuri a nasa idannuwan a kan dole

A hankali taa shiga fadin" shin menene nakasata? Har yau ka ki kaa fada min, ko da ake cewa nauyin jikina haka din ne? Shin na yi mugun nauyin da za'a riga raina min wayo ne ? Anya Mujaheed zai aureni kuwa? Yau da gobensa ya fara bani tsoro, bayan dukkan biyayar da ya dace ace na masa ina kamantawa hharda wace bai dace ba domin tun kafin na shigaa gidansa ya dora min dokoki irin masu tsaurin da idan ka ji kana iya yin fushi da ni,ama shiru kake ji bayan a da shine da kansa yace ana yin sallah zai turo, gashi yanzu an fara irgen kwanakin babar sallah,....."
Ta langwabe kai ta ci gaba da fadin" idan na yarda iyyayena suka ga hawayena a yau tanar farin ciki yaya zamu kwashe ne? Idan kuma suka ganni gani gododo Rukaya kanwata ta baya an saka mata rana yyaya zasu iya rintsawa ne? Gashi ranna ce baba, rana ce da gidanmu kaf ya dace ace muna cen muna shagali, shin na fara yiwa ahalina baakin cikin samun farin ciki komenene nake ji a nan ya tsaye min a daidau kahin zuciya? TAUFEEK inada ciwo mai girma a zuciyata wanda nake rainonsa tunda na kai shekaru goma sha bakwai a duniya, domin nan da ka ganni tun inada sha uku Mama ke dan tare tana fadin zata ga autanci idan na kai sha bakwai Aba ya mikani dakin miji, a yau shekarata ashirin da bakwai zuwa da takwas, tun tana jefa yan kofunna da kwanoni Aba na hannawa a taba cewar nawa ne har wasu suka lalace aka zubar wasun kuwa a dole aka fitar muka yi anfani da su a cikin gida, TAUFEEK yannayin jikina zai iya hannawa na auru ne ni na hakura gaba daya ko menene? Ko dai bani da lafiyane? Domin wasu na cewa ko ina fama da bakin aljani ne?????"

"Ke uban wanene ya dake ki iyi?" Muryar Hajia ta katse mata hawayen da take yi da kuma maganar da take masa mai kamada rada wace take fitarwa daga zuciyarta tana sanarwa mutun daya tak da take iya sanarwa a duniya

*KAF DUNIYA BATA DA SIRRI SAMA DA TAUFEEK* , kaf duniya bata da da sirrin da take gannin bai sani ba, komai ya sani nata, kamar wani wanda sukaa girma tarr bayan ya bata tazarar shekaru , asalima bai fi shekara hudu da suka san junna ba

Da kyar ya iya sauke dubansa a kan Hajia, wace ta kamo kumatun Khausar tana gyatsine ta ce" Ke dilla kalle ni nan, nace uban wanene ya dake ki? Ke yanzu a haka zaki zauna ki yiwa wani kuka? To na cire maki mutun biyu, ita ko shi wa'inda suka kawo ki duniyar, bayansu du wanda ya san ya dake ki fada min sai inda karfina ya kare, aikin banza aikin wofi ni du sai na ga kamar kin rage kumari daga gannin karshe da na maki, kumatun nan naki kamar sun rage auki, dan mu ga dagen hijabin mu gani....."

Da sauri ya rike hannun Hajiar, har idannuwansa na yin waje, jasa kasa ya ce" Cire mata hijab zaki yi a waje ?"

"Igiyar uban wani ke kanta da zan ki gannin kumarinta a waje?" Ta bashi amsa tana maka masa harara sannan ta kama hannun KHausar ta ce" Ke maka maka share hawayen maka, wuce mu je"

Da ido ya iya binsu, jiki a sanyaye ya juya ya nufi motar ya bude ya shiga sannan ya saka hannunsa a hankali ya dafe wajen gemunsa yana hangen kofar gidan inda Hajia ke magana da Aba wanda zuwansa kennan ya dan zagaya dan amso ruwan piyawata don su yi anfani da shi a gidan

Hajia kuwa abinda ta fadawa Aba ya saka shi yin murmushi yana bada hanya ya ce" Kai Hajia ni kam ai bani da ta cewa Khausar ai taki ce"

Ta sake sakin wani murmushi ta ce" Mamuda ko, kai dai an yi dan mutunci walahi bara na karbo completinta ko ashirin ne mu je, yar nan sai na tashi tsaye a kanta inaga sam ba'a san ciwonta ba"

Shi dai hanya ya bata ta shige, kafin ya sauke ajiyar zuciya, godiyarsa ga Allah da take da wajaje na jin sanyi a zuciya, ya sani zata dan sake tare da hajia kuma har cikin ransa ya yarda da Hajiar bashi da damuwa da tafiyar Khausar din gidanta na kwana biyu

Sunna shiga Hajia ta kirayi Mama gefe ta rage murya sosai ta ce" Kayan yar nan zaki bani mu je tare, wai kin kula kamar ta rage kumari kuwa? Yadda na ci burin auren yar nan harta gado nice nan zan mata bana son na ga tana rage kumari, wai kina bata yan jiko da su yusufa dan karro farin jinni kuwa? Sai fa da yan jiko da turare turare saboda makiya, yau ko dan yannayinta sai fa ta tsole ido, dan dauko min ko kala ashirin ne mu je kin gane?"

Mama ta amsa da to,sannan ya yi dakinsu da dan sauri

Jim kadan ta fito dauke da yar akwati dauke da kayan na Khausar, dan a shigarta sai da ta tabo Aba , yaba dagawa ya sanar mata su tafi dan haka ta sauke ajiyar zuciya ita dinma ta hado mata harda yan baby hijab dinta da hijabinta baba da kalolin kaya uku

Hajia ta amsa tana washe baki ta yi gaba ta bar Khausar tsaye wace ido ya cikowa da kwallah takasa bin hajiar ta kuma kasa cewa komai

A sanyaye tana kallon mamanta ta ce" Mama"

Mama ta sakar mata murmushi a hankali ta dan shafa gefen fuskarta ta ce" Ki je Khausar din Aba kin ji? hajia ce ai , kin ga tana sonki ki yi kokari ki kiyaye abinda zaki batawa kowa rai kin ji? Idan kina so gobena sai ki dawo ko?"

Khausar ta gyada kai a hankali sannan ta juya, tana ji wani irri, dan tunda take bata taba kwana ba a gidansu ba, komai nisan waje tana dawowa ne ta kwana a gida
Chapter 36 · 0% Book details